AKIDAR AHLUL BAIT
Wanda Ya Wallafa:
SHEIKH MOHAMMAD RIDA MUZAFFAR
Wanda Ya Yi Nazari:
SHEIKH MOHAMMAD JAWAD ATTURAIHI
Wanda Ya Fassara:
YAKUBU ABDU NINGI
( 4 )
Sunan Littafi: AKIDAR AHLUL BAIT.
Wanda Ya Wallafa: Sheikh Mohammad Rida Muzaffar.
Wanda Ya yi Nazari: Moh'd Jawad At-Turaihi.
Wanda Ya Fassara: Yakubu Abdu Ningi
Shekarar Da Aka Buga: 1419, 1998
Madaba'ar Da Ta Buga: Mihir.
Adadi: 3000.
Hakkin Mallaka: Muassasar Imam Ali (a.s.).
( 5 )
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI.
( 6 )
IMAM ALI (A.S) FOUNDATION
P.O. Box 37185/737
Qum - IRAN
LAMBAR TARHO DA FAX: 730006
( 7 )
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.
Shekaru goma ke nan suka gushe da buga wannan littafi, a duk cikin wadannan shekaru ban sami wani abu da ke iza ni in canja ra'ayina a kansa ba game da cewa ya dace da bukatun musulmi baki daya game bayyanar da akidojin Shi'a Imamiya ( masu bin Imamai sha biyu daga Zuriyar Manzo (S.A.W.A.) ).
Sai dai ma na sake samun karfin gwuiwa a kan sake jaddada yada shi, tare da fatan ya zamanto ya cimma manufa kuma ya biya bukatar kokarin gusar da lullubin giragizan da suka shamakance tsakanin manyan bangarorin musulmi guda biyu masu girma na tsawon lokaci; wato Ahlus Sunna da Shi'a, da kuma kokarin karkade kurar da tsohon tarihi dadadde ya bari a kan akidojin musulunci ingantattu.
Ni ina da tabbacin cewa ra'ayin "kusato da mazhabobi" a yau Ya zama wata bukata matsananciya, kuma manufa mai daukaka ga dukan wani musulmi mai kishin musulunci, koda mene ne kuwa sabanin mazhabarsa da ra'ayinsa a bambance-bambancen akida kuma babu abinda ya fi a wannan ra'ayin kusatowar fiye da cewa kowane mai akida ya dauki nauyin tono bisonta da hakikaninta.
Wannan hanya - a ganina - ita ce mafi aminci wajen ba da ingantaccen tunani game da mazhabar, kuma har wa yau ita ce hanya
( 8 )
mafi kusaci ga fahintar daidai daga ra'ayin da jama'arta suke rike da shi.
Saboda in amsa bukatar "Sanyin idona" mai aiki a tafarkin Allah mai daraja Sidi Murtadha Kashmir, na sake duba wannan littafi, na kuma kara shigar da wasu gyare-gyare da kare-karen da kurarren lokaci ya ba da damar yi, tare kuma da gyara kurakuren da suka auku wajen bugawa da ma wadanda ba na bugawa ba, domin in sake gabatar da shi ga Madaba'a, ina mai fatan Allah Ya tabbatar da cimma manufar da ake so, sa'an nan kuma Ya ba mu dacewar rungumar tafarki madaidaici da bin gaskiya, lalle Shi Shi ne mafi alherin wadanda ake roko.
Mawallafi
21 Shawwal 1380 Hijiriyya
1960 Miladiyya
( 9 )
GABATARWA
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Yabo da godiya su tabbata ga Allah,
Tsira da aminci su tabbata ga Muhammadu Mafificin `yan Adam da zuriyarsa shiryayyu.
Na yi shiftar wannan littafi ne kuma babu wata manufa tare da shi illa rubuce takaitaccen abinda na kai gare shi na fahintar akidojin musulunci a bisa tafarkin Ahlul Baiti (Zuriyar Gidan Manzo (S.A.W.A.) aminci Ya tabbata gare su.
An dai rubuce wannan takaitaccen littafin ne ba tare da kawo nassosin da yawanci suka iso daga Ahlul-Baiti game da su ba, domin sabon kamu da kuma mai koyo da kuma malami su amfana da shi, na sanya masa suna "Akidojin Shi'a"
1 abinda nake nufi kuwa shi ne "Shi'a Imamiya Ithna Ashariya" a kebe.
Shiftar wannan littafi an yi ta ne a shekarar 1363 Hijiriya, kuma an yi ta ne da nufin ba da ita a matsayin laccar da ake yi a ayyanannen lokacin
____________
1- Wannan shi ne sunan da marabucin Littafin ya sanya wa Littafin a bugu na farko.
( 10 )
koyarwa da kwalejin "Muntadan Nashrid Diniya"
2 don amfani da ita wajen share fagen dogon bincike game da akida daga bisani.
A wancan lokacin na ci nasarar gabatar da dama daga cikinta a laccoci kuma sam ban kasance na shirya su domin a wallafa a yada a kuma karanta ba, don haka na zamanto na jinkirtar da dama daga cikin takardun laccoci masu muhimmanci da kuma darrusan da na ba da shiftarsu a cikin wancan halin, musamman ma dangane da abinda Ya shafi Akida da ilimin tabbatar da samuwar Allah.
Sai dai kuma a wannan shekarar - bayan wucewar shekaru takwas- babban malami mai alfarma Malam Muhammadu Kazim Al-Kutbi
3 Allah Ya kiyaye shi, ya kwadaitar da ni wajen sake tunani a kansu, da kuma taro su a maida su rubutaccen littafi takaitacce mai isar da dukan bangarori da nufin yada su domin amfana baki daya, domin kuma a kore da dama daga cikin soke - soke da aka lika wa Shi'a Imamiyya, musamman ma da yake wasu marubutan wannan zamani a kasar Masar da sauransu ba su gushe ba suna ta dira a kan Shi'a da alkalumansu suna soke - soken rashin adalci a kan mazhabar Shi'a da akidojinta domin jahilci ko kuma kin sani da gangan game da tafarkin Zuriyar Gidan Manzon Allah (S.AW.A.) a tafarkunansu na addini kuma da haka ne duk suka hadu a kan zaluntar gaskiya da yada jahilci a tsakanin masu karanta littafansu suna masu kira zuwa rarraba kalmar musulmi, da haifar da husuma da kufe a zukatanru, kai har ma da cuna wasunsu a kan wasunsu... Kuma babu masani da a yau zai jahilci gwargwadon bukatar kusato da jama'ar musulmi ga junansu da binne kullace - kullacensu idan har ba mu iya mun zamar da su sahu daya baki daya a karkashin tuta guda ba.
Ina fadan haka alhali kuma ina mai jin cewa - abin ban takaici - ba za mu iya yin kome game da irin wadannan miyagun soke-soken tare da wadanda muka jarraba daga cikin irin wadannan marubutan ba
____________
2- Wannan kwalejin makarantar marubucin ce shi kansa kuma daga bisani an canja mata suna zuwa "Kwalejin Fikihu".
3- Shi ne mai Dakin karatu da ake kira Haidariyya - Najaf shi ne farkon wanda ya biya kudinsa aka fara yada wannan littafin.
( 11 )
kamarsu Dokta Ahmad Amin marubucin littafin Fajrul Islam da makamancinsa masu kira zuwa ga rarraba, su bayanin akidojin Shi'a Imamiya bai kara musu kome ba illa tsaurin kai, kuma fadakar da su kura-kurensu bai kare da kome ba sai jayayya.
Kuma bai dame su ba kan cewa su wadannan da ma wadanda ba su ba don sun ci gaba da tsaurin kan su sun dage a kai ba don gudun kada wadanda ba su sani ba su yarda da su wannan dibilbilewar ta baibaye su kuma soke-soke su kwashe su su tsiro musu da kufe da kunci.
Kuma koda ma mene ne wannan al'amarin , ni dai ina mai kaddamar da wannan littafin ne da fatan cewa a cikinsa za a sami abinda zai amfani mai neman gaskiya, don in zamanto ni ma na ba da gudummawa mai amfani ga musulunci, kai hidima ma ga `yan Adamtaka baki daya, na tsara shi a kan gabatarwa da kuma Fasali-Fasali; kuma daga Madaukaki Shi Kadai nake neman gamon katar.
Muhammad Ridha Al Muzaffar
Najaf - Iraki
27 watan Jumada Akhir 1370
Miladiyya 1950
( 12 )
1- Imaninmu Game Da Sani Da Kuma Neman Ilimi
Mun yi imanin cewa da yake Allah Ya Yi mana baiwar karfin tunani kuma Ya ba mu hankali to Ya umarce mu ne da mu yi nazari da tuntuntuni a kan alamun ayyukanSa mu yi tunani a kan hikimarSa da kuma kyautata lura a ayoyinSa a kan duniya baki daya da kuma a kan kanmu, Allah Ta'ala Yana cewa:
"Za mu nuna musu ayoyin Mu cikin sama da kuma a kawukansu, har Ya bayyana gare su cewa Shi lalle gaskiya ne..." (Surar Fussilat: 53)
Kuma Ya zargi masu bin iyaye ba tambaya da cewa:
"Suka ce mu dai kawai za mu bi abinda muka samu iyayenmu a kai ne, ashe koda ma iyayen nasu sun kasance ba sa hankalta ne kuma ba sa shiryuwa." (Surar Bakara: 170)
Kamar kuma yadda Ya aibata masu bin zato kawai da dikake a cikin duhu da cewa:
"Babu abinda suke bi sai zato kawai." (Surar An'am: 116)
Alal hakika mu abinda muka yi imani da shi shi ne cewa: Lalle hankulanmu su ne suka wajabta mana yin tuntuni kan halittu kamar yadda suka wajabta mana yin tunani a kan kiran wanda ya yi da'awar cewa shi Annabi ne da mu'ujizarsa. Kuma a gurin hankali bai dace ba a yi koyi da wani ba a cikin wadannan al'amuran kome matsayinsa da darajarsa kuwa.
( 13 )
Abinda Ya zo a cikin Alkur'ani na kwadaitarwa a kan tuntuni da bin ilimi da sani ya zo ne kawai don kara tabbatar da wannan `yancin na dabi'ar halitta a hankali da suka dace da ra'ayoyin ma'abuta hankali, Ya kuma zo ne don fuskantarwa zuwa ga abinda dabi'ar hankula ta hakunta.
4
Bai dace ba a cikin irin wannan hali mutum ya yi wa kansa saki na dafe a kan al'amarin akida, ko kuma ya kare da dogaro a kan wadanda suka masa tarbiyya, ko kuma wasu mutane daban, lalle ma ya wajaba ne a kansa daidai yadda yake a dabi'a karfafa kan ya yi bincike ya yi tunani ya yi nazari ya yi kididdiga a kan jiga-jigan akidarsa
5 wadanda ake kira jiga jigan addini wadanda mafi muhimmancinsu su ne: Tauhidi, wato kadaita Allah, da Annabci da Imamanci da kuma Tashin Kiyama.
Duk wanda Ya yi koyi da iyaye haka siddan ko kuma makamantansu a imani da wadannan jiga-jigan, to lalle ya ketare iyaka ya fandare daga hanya madaidaiciya kuma ba zai taba zama an yafe masa ba har abada. A takaice dai mu muna da'awar abubuwa biyu ne:
____________
4- Wanan kuwa shi ne daga fadar Allah Ta'ala cewa: "Ka ce ku yi dubi zuwa ga sammai da kasa." Surar Yunus:l01 da Kuma Fadar Allah Ta'ala: "Shin ba sa duba rakumi yadda aka halitta shi, da kuma sammai yadda aka kakkafa su. Da kuma kasa yadda aka shimfida ta. To ka yi fadakarwa kai dai mai fadakarwa ne kawai." Surar Gashiya: 17-21.
Da kuma fadar Allah Ta'ala: "Shin su ba sa yin tuntuni ne .:an kawu'kansu" Surar Rum: 8.
Da kuwa fadar Allah Ta'ala: "Ka sani cewa babu wani abin bautawa sai Allah". Surar Muhammad: 19.
5- Ba wai dukan abinda aka ambata wannan littafi ba ne yake daga cikin jiga-jigan akida, da yawa daga cikin akidojin da aka ambata kamarsu Hukuncin Allah da kaddara, da Raja'a da sauransu ba wajibi ba ne a kudurce da su ko kuma a yi bincike a kansu, ya halatta a dogara ga wani da aka san ingancin maganarsa game da su kamar Annabawa da Imamai. Da yawa daga cikin al'amura irin wadannan da muka yi Imani da su dogaro ne kawai da abinda aka samo daga Imamanmu na daga ingantattun hadisai tabbatattu. (Marubuci R.A.)
( 14 )
Na Farko: Wajabcin bincike da kuma nema sani a kanjiga jigan akida bai halatta a koyi da wani ba a kansu.
Na Biyu: Wannan wajabcin wajabci ne na hankali kafin ya zamanto na shari'a wato saninsa ba wai ya samo asali daga nassosin addini ba ne koda yake ya inganta su karfafa shi bayan hankali ya tabbatar da shi.
Kuma Ma'anar wajabcin hankali babu abinda take nufi illa fahintar neman sani da hankali ya yi da kuma lizimtar yin tuntuni da kokari a jiga-jigan akida.
( 15 )
2- Imaninmu Game da Koyi da Wani a Rassan
Al'amuran Addini.
Rassan al'amuran addini su ne hukunce hukuncen shari'a wadanda suka shaif ayyuka, su ba wajibi hukunce-hukuncen ba ne a yi bincike da ijtihadi a kansu sai dai ma idan ba su kasance daga cikin muhimman al'amura wadanda suka tabbata da ingantattun hujjoji kamarsu wajabcin salla da zakka da azumi ba to dayan uku ne ya wajaba:
Ko Ya yi ijtihadi Ya yi bincike a kan hukumce-hukumce idan yana daga cikin masu iya yin hakan.
6
Ko kuma ya zama mai ihtiyadi, idan yin ihtiyadi zai wadatar da shi.
7
Ko kuma ya yi koyi da Mujtahidi wanda ya cika saharruda.
8 Wato ya zamanto cewa wanda zai yi koyin da shi, mai hankali ne, Adali
____________
6- Ijtihadi kalma ce ta larabci da aka samo ta daga Juhud a lugga wato yin kokari don yin wani aiki amma a Ka'idar malaman mu na fikihu tana nufin tsamo hukunce-hukuncen shari'a daga nassosinsu tsararru. Akwai Mujtahidi Mudlak, wato cikakken mujtahidi, akwai kuma Mujtaliid Mutajazzi wato Mujtahiddi a wasu sassa, shi ne Mujtahidin da zai iya tsamo hukunce- hukunce a kan wasu al'amura banda wasu. Don karin bayani ana iya duba Littafin Al- Usul Amma lilfikihil Mukarin na Hujjat Muhammad Taki Al- Hakim Shafi na 561 zuwa 565. Da kuma Al- Masa'il Al-Muntakaba na fatawoyin Ayatullahil Uzma Sayyid Sistani shafi na 9 zuwa 10.
7- Ihtiyadi shi ne aikin da mutum zai sami yakinin cewa ya sauke wajibin da ke kansa idan ya aikata shi wannan shi ne ihtiyadi a dunkule, akwai kuma ihtiyadi a kebe da ke nufin bin fatawoyin mujtahidai don tabbatar da cewa an yi aiki da fatawar daya daga cikinsu. Littafin da ya gabata shafi na 10 zuwa 14.
8- Taklidi, koyi, shi ne yin aiki daidai da fatawar Mujtahidi wanda maganarsa hujja ce a aikace a halin yanzu tare da kiyaye cewa a bi ta daidai. Masu koyi sun kasu kashi biyu: (1) Wanda bai san kome ba a hukunce-hukuncen sahri'a. (2) Da kuma wanda ya san wani abu amma ba zai iya tsamo hukunce-hukuncen da kansa ba.
( 16 )
"mai kiyaye kansa, mai kare addininsa, mai saba wa so ransa, mai bin umarnin Ubangijinsa",
9 ·
Duk wanda ba Mujtahidi ba ne kuma ba mai yin ihtiyadi ba ne kuma bai yi koyi da mujtahidi wanda ya cika sharuda ba to dukkan ayyukan ibadarsa batattu ne ba za a karba daga gare shi ba, ko da kuwa ya yi salla ya yi azumi ya y ta ibada duk tsawon rayuwarwa, sai dai idan aikin sa Ya dace da ra'ayin wanda zai yi koyi da shi daga baya, ya kuma yi gamon katar cewa ya yi aikin nasa ne da nufin bauta ga Allah Ta'ala.
10
____________
9- Tafsirul Askari shafi na 300 da Littafin Al- Ihtijaj, 511, H. 337, abinda ya wadatar da karin bayani.
10- Manyan Malamai sun kawo abinda ya wadatar da karin bayani a cikin mukaddamomin Risalolinsu na hukunci da ke kunshe da fatawoyinsu a Babin Takalidi (yadda ya wajaba a kan dukan baligi wanda bai kai ga darajar ijtihadi ba kan cewa ya zamanto a cikin dukkan ayyukan ibadarsa da mu'amalarsa da sauran ayyukansa, ya zamanto mai yin koyi ko mai yin ihtiyadi, sai dai kawai idan yana da tabbacin cewa ba ya bukatarsa a aikinsa ko kuma barinsa ba zai zama saba wa hukunci ba koda da gwargwadon haramcin shari'a, ko kuma hukuncin ya kasance daga larurar addini da mazhaba kamar yadda yake a wasu wajibai da haramtattu da kuma da dama daga mustahabbai da halalai, ko ya kuma zamanto ya sami sani a zuci da kuma natsuwa a zuciya daga madogarai na hankali, kamar yaduwar labari, da fadar kwararren da ya tabbatar da cewa suna daga ciki.) A duba: Minhajis Salihin Juzu'i na daya daga fatawoyin Ayatullahil Uzma Sayyid Ali Husain Sistani shafi na 9.
( 17 )
3- Imaninmu Game da Ijtihadi
Mun yi Imanin cewa: Ijtihadi (matsayin tsamo hukunce-hukunce) a rassan hukunce-hukuncen shari'a wajibi ne da wajabcin kifa'iyya da ya doru a kan dukkan musulmi a zamanin boyuwar Imam
11, wato.
____________
11- Imam Muhammad Mahadi dan Imam Hasan Askari (a.s) wanda shi ne cikamakin Imamai goma sha biyu - Boyuwarsa ta kasance sau biyu ne:
Ta farko: Ana ce da ita karamar boyuwa: Ta fara ne a daga shekarar da mahaifinsa Imam Hasan Askari (a.s) ya rasu shekara ta 260 Hijiriyya kuma ta kare a shekara ta 329 Hijiriyya kuma ya kasance yana da jakadu hudu su ne:
Na farko Usman bin Sa'id Al -Umari Al- Asadi, shi ya kasance wakilin Imam Hadi sa'an nan kuma wakili ga Imam Askari sai kuma ga Imam Muhammad Mahadi. Aminci ya tabbata gare su.
Na Biyu: Muhammad bin Usman bin Sa'idul Umari al- Asadi wanda ya dauki nauyin wakilci bayan rasuwar mahaifinsa na tsawo kimanin shekaru arba'in har zuwa mutuwarsa; a shekarar 329 Hijiriyya.
Na uku: Husain bin Ruh wanda ya dauki nauyin al'amarin wakilcin tun daga rasuwar Muhammad bin Usman al- Umarin har zuwa wafatinsa a shekarar 326. Hijiriyya.
Na Hudu: Aliyu bin Muhammad As- Samarri, shi ne na karshe daga cikin wakilai hudu, ya yi wakilcinsa ne na tsawo shekara uku yayin da ya kawo karshe da wafatinsa ranar 15 ga watan Sha'aban shekarar 329. Hijiriyya.
Sananne ne cewa dukkan wadannan wakilai an yi musu kabari ne a birnin Bagadaza bayan rasuwarsu, ya zuwa yanzu kuma Makabartunsu sanannu ne mashahurai.
Ta Biyu: Babbar Boyuwa: Ta fara ne daga ranar 15 ga watan Sha'aban shekarar 329, Hijiriyya daga rasuwar wakili na hudu wanda yayin da aka tambaye shi cewa wa zai gadarwa wannan al'amarin kuma sai ya ce Allah na da wani al'amari kuma shi ne mai isar da shi: A cikin wannan akwai bayani game da abinda Imam al- Muntazar
( 18 )
ma'ana cewa ya wajaba a kan musulmi a kowane zamani. Amma kuma idan har wani da zai iya kuma zai wadatar ya dauki nauyin yi to ya fadi daga kan sauran musulman, sai su wadatu da wanda ya dauki nauyin yin hakan kuma ya kai ga matsayin ijtihadi kuma ya zamanto ya cika sharudan, sai, su yi masa takalidi, su yi koyi da shi, su koma gare shi a kan rassan hukunce-hukuncen addininsu.
Don haka a kowane zamani wajibi ne musulmi su duba kansu su gani, idan sun sami Mujtahidi a tsakaninsu wanda ya sadaukar da kansa ya kai ga matsayin Ijtihadi- wanda babu mai samunsa sai mai babban rabo- kuma ya kasance ya cika sharudan da suka sa ya cancanci a yi masa takalidi, a yi koyi da shi, sai su wadatu da shi su yi masa takalidi, su koma gare shi domin sanin hukunce-hukuncen addininsu.
____________
Allah Ya gaggauta bayyanarsa ya sanar da shi game da fara babbar boyuwa wadda take ci gaba har zuwa yau, yayin wakilcin Imam a zamanin boyuwar babba ya zama an sallama shi ga Mujtahidi wanda ya cika sharudan da aka bayyana a littafan fikihu.
Kamar yadda ya gabata a bayanin ma'anar ijtihadi za mu ga cewa tsamo hukunce-hukunce wanda ke nufin "ayyana matsayin aiki game da shari'a tare da dalilai kuma Muhimmancin ijtihadi yana zuwa ne saboda bayyana cewa mutum a bisa biyayyarsa ga shari'a mai tsarki da kuma wajibcin gudanar da hukunce-hukuncenta -lalle ne gare shi ya ayyana abin da zai aikata game da ita. Tunda yake yawancin hukunce-hukuncen shari'a ba su bayyana karara yadda za ta wadatar daga neman dalilai ba, bai dace da hankali ba a ce za a haramta wa mutane baki daya ayyana matsayin aiki a bisa dalilai, a hana su duba dalilan da suka ayyana matsayinsu game da shari'a. Don haka aikin tsamo hukunce-hukunce ba ma kawai ya halatta ba ne, larura ne ma a yi shi, wannan larura kuma asalinta daga biyayyar mutum ne ga shari'a, musu a kan haka tamkar musu ne a kan abinda yake bayyananne kuma kalmar ijtihadi a tarihi ta sami fassarori dabam-daban yadda har fassarorin suka sanya ma'anoninsa a cikin duhu har ya kai ga sabani saboda damarwa da rikitarwa ba a samu tabbacin ma'anarta ba a yau har sai da ya ketare matakai daban-daban na fassarar ma'anoninsa.
A duba Littafin "Ma'alimuj Jadid Lil Usul: Sayyid Shahid Sadr (r.a) shafi na 23 zuwa sama. Don karin bayani kuma game da Boyawar Imam a duba Littafin Tarikhul Gaibatus Sugra na Sayyid' Muhammad Sadr: 395 fasali na uku (Assufara'ul Arba'ati Hayatuhum wa Nashadatuhum).
( 19 )
Idan kuwa ba su sami wanda yake da wannan matsayin ba to Ya wajaba a kansu kowane daya daga cikinsu Ya kai ga matsayin Ijtihadi, ko kuma su shirya a tsakaninsu wanda zai dukufa domin kaiwa ga wannan mukami domin ba zai yiwu ba dukansu su dukufa domin neman wannan al'amari ko kuma zai yi wahala.
Kuma bai halatta gare su ba su yi koyi da wanda ya rigaya ya mutu daga cikin Mujtahidai.
l2 Ijtihadi shi ne nazarin dalilan shari'a domin samun masaniya game da rassan hukunce-hukuncen shari'ar da shugaban Manzanni (S.A.W.A.) Ya zo da ita, kuma ba ta canzawa ba ta sakewa da sakewar zamani da kuma halaye "Halalin Muhammadu halal ne har zuwa ranar Kiyama, haramun dinsa kuma haramun ne har zuwa ranar tashin Kiyama."
13
Dalilan shari'a su ne: Alkur'ani mai girma, da sunna, da Ijma'i, da Hankali kamar yadda yake a filla filla a littafin Usulil Fikhi.
Samun matsayin Ijtihadi kuwa yana bukatar tarin ilimi da sani wandanda ba sa samuwa sai ga wanda ya dage ya wahalay ya sallama kansa ya ba da kokarinsa wajen samun sa.
14
____________
12- Takalidi, koyi da Mujtahidi kashi biyu ne: (1) Farawa (2) da Dorewa
Farawa: Shi ne baligi ya yi wa mujtahidi matacce taklidi ba tare da ya riga fara yi masa taklidi tun yana raye ba. Wannan bai halatta ba koda kuwa mujtahidi matacce ya fi wadanda ke raye ilimi.
Dorewa: Wannan kuma shi ne mukallafi ya fara ya yi wa wani mujtahidi ayyananne taklidi tun yana raye sa'an nan ya ci gaba da binsa bayan rasuwarsa. Wannan ya halatta idan har Mujtahidin da ya rasun ya fi wadanda suke raye ilimi ko kuma idan ba a sani ba ko da a dunkule cewa fatawar wanda ya rasun ta saba wa ta wanda yake raye a al'amuran da ya zama yana fuskantar mushkila game da su. Domin karin bayani a duba littafin Urwatul Wuska Juzu'i na 1 shafi na 17-18, da kuma Masa'ilul Muntakhaba na Sayyid Sistani Matsala ta 13 (12, 13, 14).
13- Al- Kafi Juzu'i na 58/1 H. 19, Al- Mahasin 1/420 H. 963.
14- Abubuwan da Mujtahidi ke bukata na ilimi kashi tara ne, uku daga-cikinsu daga ilimin adabi su ne ilimi,lugga, da ilimin Sarfu, da ilimin nahwu, akwai kuma ilimin aiki da hankali da suka hada da ilimin Usuli, da Ilmul Kalam, da kuma ilimin Mandiki, sai kuma ilimin tafsirin ayoyin hukunce-hukuncen Kur'ani, da ilimin hadisan hukunce-hukunce sai kuma ilimin sanin rauni da kuma inganci da kuma
( 20 )
4- Imaninmu Game da Mujtahidi
Abinda muka yi imani da shi game da Mujtahidi wanda ya cika sharuda: cewa shi Na'ibin Imam (A.S.) na halin boyuwar shi Imam din.
15 Kuma shi mai hukunci ne, shugaba cikakke, abinda yake ga Imam (A.S.) yana gare shi a fannin al'amura da shugabanci a tsakanin mutane kuma duk wanda ya ki hukuncinsa tamkar ya ki hukuncin Imam (A.S.) wanda ya ki hukuncin Imam (A.S.) kuwa Ya ki hukuncin Allah ne wannan kuwa a matsayin shirka da Allah yake, kamar yadda Ya zo a hadisi daga Sadikun Ahlul Baiti (A.S.).
16
Shi Mujtahidin da ya cika sharruda ba wai madogara ne kawai a wajen ba da fatawa ba, a'a har ma yana da jagoranci na gaba daya,
17
____________
inganci masu ruwaya. Don Karin bayani a duba Al-Wafi fi Usul'ul Fikhi na Fadhilul Tuni 25-29 da kuma AlKur'an wal Akida na Sayyid Muslim Hamudil Hilli: 248-252.
15- A duba karin bayanin da ya gabata a kan Abinda muka yi Imami da shi game Ijtihadi.
16- Ihtijaj 2/260 H. 232 Al-Kafi 1/54 H. 10.
17- Willayatul Fakihi, shugabancin Malami, ma'ana ce da ke nufin shugabanci na shari'a da jagorancin dokoki ga Mujtahidi wanda ya cika sharruda wanda shi wannan matsayi yana mazaunin ci gaban sakon Imama ne kuma ba ya da cikin fararrun al'amuran addinin a wannan zamanin sai dai ma asalin wannan batu yana da tushe ne tun daga farkon sako da kuma zamanin Imamai Ma'asumai (A.S.) a halin wannan matsayi yana misalta ci gaban Imamanci ta bangaren ayyuka baki daya ya bambanta da Imamanci ta nassosi na musamman ga kowane fakihi, da kuma ismar da ta kebantu ga Mamzon Allah (S.A.W.A.) da kuma Imami goma sha biyu bayansa tunda yake nassi da isma sun kebantu ne da Ma'asumai (A.S.).
Babu makawa a san hikimar wannan shugabanci na gaba daya a zamanin Boyuwar Imam, wannan matsayi yana nufin kafa hujja ne ga mutane, da kuma ja-
( 21 )
don haka ana komawa gare shi a hukunci da raba gardama da shari'a, wannan duk na daga cikin abubuwan da suka kebantu da shi kuma bai halatta ga wani ba ya dauki nauyinsu sai shi, sai dai da izininsa, kamar kuma yadda bai halatta ba a yi haddi ko labadtarwa sai da umarninsa da hukuncinsa.
18
____________
gorancin wannan zamanin domin kare amfanin bayin Allah da kuma tafi da al'amuransu a kan yadda shari'ar musulunci ta tsara. Daga cikin manyan manufofinta kuwa akwai kare hukunce-hukuncen shari'a domin al'amarin tsara shari'a da sanya dokoki na Allah Ta'ala ne mahalicci mai kudura ,amma dangane da hukunce-hukunce al'amuran rayuwa kuwa musamman sababbi da ke aukuwa yanzu, ba za su gaza kasan cewa tabbacin hukunce-hukunce ne da aka gama gabatar da su daga bangaren Manzo (S.A.W.A.) ba yayin rayuwarsa...
An ruwaito daga Imam Mahadi, (Allah ya gaggauta bayyanar sa) cewa "Amma hakikanin al'amura masu faruwa to dangane da su ku koma ga masu ruwaita hadisanmu, domin su hujjatu ne a kanku ni kumar hujjar Allah ne a kansu." A duba Littafin Al- Imama Hatta Wilayatul Fakih shafi na 51."
18- Ruwayar Umar Bin Hanzala na ishara da haka yayin da ya ce: 'Na tambayi Aba Abdillah, Alaihis Salam dangane da mutane biyu daga cikin ma'abutanmu (shi'a) wadanda ke da rikici a tsakaninsu a kan bashi ko kuma gado suka kai kara zuwa gurin shugaba ko Alkalai shin haka ya halatta? Ya ce: Wanda ya kai kara gare su a kan gaskiya ko karya to ya kai kara gurin Dagutu da kuma abinda Allah Ya yi umarni a kafirce masa, Allah Ta'ala Ya ce: "Suna so ne su kai kara zuwa ga Dagutu alhali kuwa an umarce su da su kafurce masa" Na ce: To yaya za su yi? Ya ce: Su duba wanda ya ruwaito hadisanmu, ya kuma duba halal dinmu da kuma haram dinmu, kuma ya san hukunce-hukuncenmu su amince da shi a matsayin mai hukunci, domin ni na sanya shi mai hukunci a kanku, idan ya yi hukunci da hukuncinmu bai amince ba to ya wawaitar da hukuncin Allah kuma ya dawo mana da hukuncin ne, wanda ya mayar mana kuwa ya mayar wa Allah, kuma daidai yake da shirka da Allah".
Al-Wasa'il Juzu'i na 27 shafi na 136 Hadisi na 33416, Al Kafi Juzu'i na 1 shafi na 54 Hadisi na 10, Al- Ihtijaj Juzu'i na 2 shafi na 260 Hadisi na 232, Tahzibil Ahkam Juzu'i na 6 shafi na 218 hadisi na 514 da shafi na 301 hadisi na 845 da kuma surar Nisa'i aya ta 60.
( 22 )
Kuma ana komawa gare shi a kan dukiyoyin da suke hakkokin Imam ne da suka kebantu da shi.
19
____________
19- Abin nufi da dukiya: Zakka da khumusi. Zakka tana daga wajiban addini. Hadisai da dama suna nuna cewa mai hana Zakka kafiri ne, da kuma cewa wanda baya ba da zakka ba shi da salla. Zakka tana wajaba ne a kan abubuwa tara:
1- Dabbobin Ni'ima guda uku wadanda su ne: Rakumi da shanu da kuma tumaki da Awaki.
2- Zinare da Azurfa.
3- Kayan Abinci hudu:Alkama, Sha'ir, Dabino da kuma zabibi.
A kowace shekara ake karbar zakka a wadannan abubuwan tara a bisa kimanin da aka sani, da sharrudan da aka ambata a gurarensu, zakka ba ta wajaba ba a kan abubuwan da ba wadannan taran ba sai dai kuma mustahabbi ne a fidda zakka a dukiyar kasuwanci da dawaki da kuma abubuwan da kasa ke tsirarwa na daga `ya'yan itaciya da wasunsu. Wadannan dukiyoyin kuma ana kashe su ne a kan kasafi takwas wadanda su ne: 1- Fakiri 2- Miskini 3- Masu Aikinta 4- Wadande aka son jawo hankalinsu ga musulunci 5- Bayi 6- Wadanda ake bi bashi 7- A tafarkin Allah -wawo dukkan wata hanya ta alheri, an kuma ce ya kebanta ne ga abinda ya shafi fa'idar kowa da kowa. 8- Wanda ke kan Tafarki, shi ne matafiyi wanda guzuri ya yanke masa ko kuma kayansa ya bace yadda ba zai iya komawa muhallinsa ba koda kuwa mawadaci ne, babu wani al'amari na zakka a mazhabar Shi'a Imamiyya face ya yi daidai da sauran mazhabobi hudun nan sanannu.
A duba littafin Urwatul Wuska Juzu'i na 2 shafi na 87-134, da masa'ilul Muntakhaba na Sayyid Sistani, da Aslus Shi'a wa Usuliha da rubuto hujjojinsa na Mu'assasar Imam Ali (A.S.) shafi na 243.
Khumusi: A gurin Shi'a Imamiyya hakki ne da Allah Ya wajabta saboda zuriyar gidan Manzon Allah Muhammadu (S.A.W.A.) a madadin sadakar zakka wadda take haramun ce gare su. Asalinsa kuma shi ne fadar Allah Ta'ala: "Ku sani cewa lalle abinda kuka samu ganimarsa da wani abu to lalle khumusinsa na Allah ne da Manzonsa da kuma dangi makusata." Surar Anfal ayata 41.
Khumusi ya wajaba ne a kan abubuwa bakwai:
1- Ganimar da aka kwata daga kafiran yaki yayin yakayya da su tare da izinin Imam.
2- Ma'adanai kamar su zinare da azurfa da.....
3- Taskar tsintuwa a karkashin kasa
4- Jawharai da aka tsamo a teku.
5- Dukiyar Halal da ta gauraya da ta Haram kuma ba'a san mamallakinta ba.
( 23 )
Wannan matsayin ko kuma shugabanci na gaba daya Imam (A.S.) Ya ba da shi ga Mujtahidi wanda ya cika sharruda domin ya kasance na'ibinsa wato wakili ko magajinsa a yayin boyuwarsa, wannan shi ne abinda ya sa ake ce masa "Na'ibin Imam".
____________
6- Fegin da kafirin amana ya saya a gurin musulmi.
7- Abinda ya saura daga kasafin shekara da kasafin iyali na ribar kasuwanci da aiki.
Ana raba khumusi kashi shida:
l- Na Allah
2- Na Annabi.
3- Na Imam. Wanan kasafin gida uku ya kebanta ne ga Imam Mahadi da ake
jira. Allah ya gaggauto da bayyanarsa, Amin.
4- Marayu
5- Miskinai da kuma
6- Wadanda ke kan tafarki guzuri ya yanke musu.
Domin karin bayani a duba Urwatul Wuska Juzu'i na 2 shafi na 170-199, da kuma masa'ilul Muntakhaba na Sayyid Sistani matsala ta 251-239, da Aslushi'a wa Usuliha shafi na 245 da ma dukkan Risalolin hukunce-hukunce.
( 24 )
( 25 )
FASALI NA FARKO
Sanin Ubangiji Imaninmu Game da:
Allah Ta'ala
Tauhidi
Siffofinsa Ta'ala
Adalci
Wajabta Aiki
Hukuncin Allah da Kaddara
Al-Bada'
Hukunce - Hukuncen Addini
( 26 )
( 27 )
5- Imaninmu Game da Allah Ta'ala.
Mun yi imani cewa Allah Madaukaki daya ne Makadaici babu wani abu kamar Shi, Wanzazze bai gushe ba kuma ba Ya gushewa, Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai Hikima, Adali, Rayayye, Mai iko, Mawadaci, Mai Ji, Mai gani, ba a siffanta Shi da abinda ake siffanta halittu, Shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba jiki ba ne kuma ba rabi ba ne, ba Shi da nauyi ko sakwaikwaya, ba Shi da motsi ko lambo, ba Shi da guri ba Shi da zamani kuma ba a nuni zuwa gare Shi.
20 Kamar kuma yadda babu kini gare Shi, babu kama, babu kishiya, babu mata gare Shi, babu da, babu abokin tarayya, kuma babu wani tamka gare Shi, maganai ba sa riskar Sa Shi kuwa yana riskar maganai.
____________
20- An ruwaito daga Amirul Muminin Imam (A.S.) a amsar da ya ba wa Za'alab cewa: "Ni ba bawan Ubangijin da bana gani ba ne" sai kuma ya kara bayani game da siffofin Allah yana cewa: "Kaiton ka ai idanduna ba sa ganin Sa da hallarar maganai sai dai zukata ne ke ganin Sa da hakikanin imani, Kaitonka ya Za'alab, lalle Ubangijina ba a siffanta Shi da nisa, ba a siffanta Shi da motsi ko lambo, ko tsayuwa, tsayuwa ta mikewa kyam, ba kuma a siffanta Shi da zuwa ko kuma tafiya, mai Taushin Tausasawa ba a siffanta Shi da babba ,mafi girman masu girma wanda ba a siffanta Shi da girma mafi daukakar masu daukaka wanda ba a siffanta shi da gallazawa, Mai jin kai da rahama ba a siffantashi da rauni mumini ba wai da ibada ba, mai riska amma ba da jiki ba, mai magana amma ba da lafazi ba, Ya na tare da abubuwa amma bada gauraita ba, Yana kuma rabe da su amma ba wai da sabani ba, Ya na sama da kome ba a ce wani abu na sama da shi, Yana gaban kome ba a ce yana da gaba, Yana cikin kome ba wai kamar yadda wani abu ke wajen wani abu ba."
Littafin At-Tauhid na Saduk Shafi na 304 Babin Hadisin Za'alab da kuma Amali Saduk Shafi na 280 Al-Majlisul Khamis Wal Khamsun, da Biharul Anwar juzu'i na 4. Shafi na 27.
( 28 )
Duk wanda Ya ce ana kamanta Shi to Ya zamar da Shi halitta ke nan, wato Ya suranta fuska gare Shi da hannu da kuma idaniya, ko kuma cewa Shi yana saukowa zuwa saman duniya, ko kuma cewa zai bayyana ga 'yan aljanna kamar wata, ko kuma makamantan wannan,
21 to lalle yana matsayin wanda ya kafirce da Shi ne, wanda ya jahilci hakikanin mahaliccin da Ya tsarkaka daga nakasa, kai duk ma abinda muka bambance Shi da sake-saken zukatanmu a mafi daldalewar ma'anarsa to Shi abin halitta na kamar mu wanda kuma mai komawa ne gare mu, kamar yadda Imam Bakir (A.S.) fassara Shi gare mu da bayyani mai hikima da kuma zurfin ma'ana ta ilimi mai zurfi.
Har ila yau ana hade duk wanda ya ce yana nuna kanSa ga halittunSa ranar kiyama,ana hade shi a cikin kafirai
22, koda kuwa ya
____________
21- Kamar Yadda Karamiyawa ke fada cewa yana sama.
22- Asha'irawa sun hukunta cewa Allah Zai nuna Kansa ga bayinSa. A duba littafin Al-Ibana fi Usulid Din na Al- Hasanul Ash'ari Juzu'i na 5 da na 6 da Almilal wan Nihal Juzu'i na 1 shafi na 85-94, da kuma Hashiyyar kastali da aka buga a Hamish sharhin Al-Aka'id na Taftazani shafi na 70 da kuma Allawani'u Ilahiya Shafi na 82-981
Al-Bagadadi ya kara da cewa: "Ahlussunna sun hadu a kan cewa ranar Alkiyama Muminai za su ga Allah kuma suka ce ya halatta a gan Shi ko ta halin kaka ta hanyar hankali, amma wajabcin ganin Sa ga muminai ranar Alkiyama ya zo ne a hadisasi Littafin Al fark bainal Firak shafi na 335-336.
In banda Jama'ar da ake kira Mujassama daga cikin Ahlussunna, wadanda suka yi imanin cewa dukkan wadanda za su tashi ranar Kiyama za su gan Shi tamkar yadda ake ganin rana da wata ba tare da giragizai a tsakaninsu. Abinda ake da sabani a kai baki daya shi ne ganin Allah Ta'ala, shi zai yiwu ne tare da tsarkake Shi? Ko kuwa sam ba zai yiwu ba ne sam, tare kuma da tsarkake Shi? Su Asha'irawa sunyi imani da na farko (yiwuwar ganinsa) mu kuma Shi'a mun yi imani da na biyu (rashin yiwuwar ganin sa) muna masu bin maganar Imamanmu (A.S.) na Ahlul Bait.
A duba Littafin: Kitab Haular Ru'uya na Imam Sharafuddin ya warware wannan al'amari yadda ya kamata ta hanya mai karfi.
Wannan kuma duk kari ne a kan abinda ya zo na cewa Allah Ya halitta Annabi Adam (A.S.) a kan kama irin tasa, kuma cewa yana da gabobi bayyanannu kamar su yatsu da makyangyama, da kasfa da kuma cewa akwai wata alama a makyangyamarSa da za a gane shi da ita, da kuma cewa zai sanya kafarSa a cikin
( 29 )
kore masa kamantawa da jiki, batun baka ne kawai kuma irin wadannan masu da'awa sun sandare ne kawai a kan wasu laffuza na zahiri na Alkur'ani ne ko kuma wasu hadisai kuma suka karyata hankulansu suka yi watsi da su a bayansu. Don haka suka gaza yin aiki da zahiri gwargwadon yadda nazari da dalilai suka hukunta da kuma ka'idojin lakabi da kuma aron ma'anar kalma ba.
____________
wutar Jahannama ranar Alkiyama har sai ta ce kad-kad,. Da kuma Manzon (S.A.W.A) zai ga Allah sai ya fadi ya yi sujada. Da kuma cewa Allah zai sauko ranar Kiyama zuwa gurin bayinSa domin Ya yi hukunci a tsakaninsu. Da kuma cewa muminai za su ga Ubangijinsu ranar Alkiyama kuma ba za su matsatsu ba wajen ganinsa. Da dai irinsu irinsu da yawa. A duba Sahih Bukhari Juzu'i na 8 shafi na 62 da Juzu'i na 9 shafi na 156. Da kuma Sahih Muslim Juzu'i na 4 shafi na 2, 83. Da ibn Majah Juzu'i na 1 shafi na 64, da Musnad Ahmad Juzu'i na 2 shafi na 264 da Muwadda Juzu'i na 1 shafi na 214 Hadisi na 30.
( 30 )
6- Imaninmu Game da Tauhidi.
Mun yi imani ya wajaba a kadaita Allah ta kowace nahiya, kamar yadda ya wajaba a kadaita Shi a zatinSa haka nan kuma muka yi imani da cewa Shi kadai ne a zatinSa da wajabcin samuwarSa, kazalika Ya wajaba kadaita Shi a siffofi. Wannan kuwa saboda imani ne da cewa siffofinSa ainihin zatinSa ne kuma Shi a ilimi da kudura ba Shi da na biyu a halitta da arzutawa kuma ba Shi da abokin tarayya, a cikin dukkan kamala kuma ba Shi da kwatankwaci.
Kazalika mun yi imani da kadaita Shi a bauta. Bai halatta a bauta wa waninSa ba ko ta wace fuska, kamar kuma yadda bai halatta ba a hada Shi da wani nau'i na nau'o'in ibada, wajiba ce ko kuma wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma a wasu da ba ita ba na daga ibadoji.
Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to shi Mushiriki ne kamar kuma wanda yake riya a ibadarsa yana neman kusancin wanin Allah Ta'ala, hukuncinsa shi wanda ya yi haka hukuncin wanda ya bauta wa gumaka ne babu bambanci a tsakaninsu.
23
____________
23- Shaikh Muzaffar (R.A.) ya ambata ta a laccarsa ta Falsafar Musulunci cewa: "A bayananmu game da Ubangiji muna bin mataki-mataki ne, muna ketare marhaloli:
1- Marhala ta farko: a tabbatar da asalin wanda samuwarsa wajibi ne.
2- Marhala ta Biyu: Bayan tabbatar da asalin wanda samuwarsa wajibi ne ya zamonta abin siffantawa da ainihin samuwa.
3- Marhala ta uku: bayan mun tabbatar da marhalolin biyu sai mu zarce zuwa kadaitakarSa, domin idan har ya tabbata cewa ainihin samuwa ne to lalle ne
( 31 )
Amma abinda ya shafi ziyatar kaburbura da kuma gudanar da bukukuwa ba sa daga cikin nau'in neman kusaci ga wanin Allah (ibada) kamar yadda wasu daga masu son suka ga tafarkin Shi'a Imamiyya suke rayawa suna masu jahiltar hakikanin al'amarin su.
24 Sai
____________
ya zamanto shi makadaici ne domin ainihin samuwa makadaici ne idan kuwa ba haka ba zai zama ainihin samuwa ba.
Sa'annan kuma sai ya ambato dalilin malamai magabata wajen tabbatar da samuwar Allah a takaice kamar haka: "Duniya daya ce don haka mahaliccinta ma lalle ne ya zamanto daya. Akwai dangantaka tsakanin kasancewar mahalicci daya abin halittar ma daya wato duniya ta yadda idan da an kaddara cewa an samu duniyoyi biyu ko da iyayen gijinsu ma sun kasance biyu shi ne fadinsa cewa: Makadaici ba ya samarwa illa makadaici.
Sa'an nan sai ya yi ishara ga hudubar Imam Ali (A.S.) game da tauhidi da ke cewa "cikar tauhidi shi ne tsarkake aiki gare Shi." Gajeruwar fahinta game da tsarkakewa shi ne tsarkakewa gare Shi a ayyukan ibada, sai dai kuma wannan ba zai dace da abin da ya gabace shi da kuma wanda ya biyo baya ba a maganar.
Tsarkakewa gare Shi na nufin tsarkake Shi daga dukkan nakasa, da kuma dukan abinda zai soke cewa Shi Wajibin samamme ne, wato tsarkakewa ta fi da'irar tsarkake aikin ibada girma. Don haka tawhidi ko kuma kadaita Allah ba ya zamantowa na hakika har sai ya zamanto ka kadaita Shi ta kowace jiha, a zatinSa, da siffofinSa, da ayyukanSa, da kuma bautarsa, tsarkakewa gare Shi na nufin kadaita Shi ta kowace fuska, da kuma tsarkake Shi daga abokin tarayya ta kowane bangare..."
A duba littafin Falsafatul Islamiyya; laccocin Shaikh Muzaffar (R.A.) da ya yiwa daliban kwalejin Fikihu a garin Najaf mai Alfarma, darasi na goma shafi 91, da kuma darasi na goma sha daya shafi na 93, da darasi na goma sha hudu shafi na 103.
24- A nan marubucin yana ishara ne ga irin batutuwan rikitarwar da wasu masu husuma da Shi'a suka tayar kan cewa ziyartar kaburbura haramun ne kuma suka yi ta yayatawa. Suka dogara da wani hadisi da Nisa'i ya ruwaito a cikin littafinsa sunan Nisa'i wanda lafazinsa ya zo kamar haka:
"Allah Ya la'anci masu ziyartar kaburbura da kuma wadanda suka rike masallatai da kuma gurin kunna fitila." Juzu'i na 4 shafi na 95. Littafin Kanzul Ummal ma ya kawo shi da lafazi iri daya, Juzu'i na 16 shafi na 388 hadisi na 45039, Ibn Majah shi ma ya kawo shi da lafazi sabanin wannan da ke cewa: "Manzon Allah (S.A.W.A.) ya la'ani masu ziyartar kaburbura" Juzu'i na 1 shafi na 502 Babu Ma Ja'a fin Nahyi an Ziyaratun Nisa'il Kubura hadisi na 1574 da 1576. A sarari yake cewa a hadisan biyu akwai sabanin lafazi da kuma rikitarwa lafazin masu ziyarta mata ya bambanta daga lafazin masu yawan ziyarta da ke nufin matukar ziyarta ta
( 32 )
kali. Kamar kuma yadda akwai rashin karin da yake Nisa'i ya ambata, bugu da kuma Muhammad Nasiruddin Albani ya ambata wannan hadisin a ciki raunanan hadisai "Silsilatul Ahadisid Dha'ifa Juzu'i na 1 shafi na 258 hadisi na 225 da kuma Ibn Uday a littafi Al- Kamil Fid Dhu'afa Juzu'i na 5 shafi na 1698 ba tare da ya ambata karin da ke akwai a cikin sunani Nisa' i ba.
Wannan dangane da matanin hadisin ke nan, amma abinda ya shafi Isnad wato hanyar ruwaito hadisin. A cikin Isnadin wannan hadisin akwai Abdul Waris bin Abu Salih a ruwayar Nisa'i da kuma ruwayar Ibin Majah na farko da kuma Abdullah bin Usman da kuma Abdurrahman bin Bahman a ruwayar Ibin Majah ta biyu wadanan maruwaita kuwa za a iya fahintar al'amarinsu kamar haka:
Abdulwaris bin Sa'id Ibin Haban ya ce shi dan Kadariyya ne. Assaji ya ce dan Kadariyya ne da ake zargi saboda bidi'arsa. Ibin Mu'in ma ya ce: Ya yi imani da kadariyya kuma yana bayyana haka. An ambata wannan ne a cikin littafin Tahzibut Tahzib Juzu'i na 6 shafi na 391-392.
1 - Abu Salih: Shi ana taraddudi a kansa tsakanin kasancewarsa shi ne Mizanin al-Basari ko kuwa shi Bazam Mawla Ummi Hani. Wanda mafi yawancin malaman sanin maruwaita suka fi ba da karfi a kan shi ne cewa shi Baz Bazam kuwa Ibin Hijir ya fada a cikin Tahzibit Tahzib a Juzuz'i na 1 shafi 364 da 365 cewa game da shi Ahmad ya ce: Ibin Mahdi ya bar hadisin Abu Hatim kuma ya ce: Ana rubuta hadisinsa amma ba a kafa hujja da shi. Nisa'i kuma ya ce: Shi ba amintacce ba ne. Ibin Udayyi ya ce: Ban san wani daya daga cikin magabata da ya yarda da shi ba. Zakariyya bin Abi Za'ida kuma ya ce: Sha'abi ya kasance yana wucewa ta gurin Abi Salih ya kama kunnensa ya ja kana ya ce: kaitonka kana fassara Alkur'ani alhali kai ba ka kiyaye Alkur'ani ba,Ibin Madini kuma daga Kaddani daga Sauri ya ce: Kalbi yace Abu Salih ya ce mini duk hadisin da na fada karya ne. An kuma kawo daga Jawzi daga Azdi cewa ya ce: Makaryaci ne. Wannan abinda Tahzibut'Tahzib ya ambata ke nan kawai. Amma a littafin Silsilatul Ahadisud Dha'ifa " Silsilar Raunanan Hadisai" bayan an ambato hadisin an kuma ba da karfin cewa AbuSalih din shi ne Bazam sai ya ce: "Abu Salih din nan shi ne Mawla Ummi Hani Bint Abi Dalib Kuma sunansa Bazan ne ana kuma ce masa Bazam shi rarrauna ne a gurin kowa da kowa, kuma mai yawan suka ne babu wani da ya amince shi sai dai Ajali shi kadai. Hatta Isma'il Bin Abi Khalid Azdi ma cewa ya yi makaryaci ne wasunsu kuma sun siffata shi da gurbatarwa. Hafiz yace a cikin At-Takrib mai rauni ne mai cudanya hadisi. Shi rarrauna ne a gurin Ibin Mulakkan da kuma Abdul Hak Asbili. Silsilatul Ahadisud Dha'ifa juzu'ina 5 shafi na 275-276.
( 33 )
2- Abdullahi Bin Usman: Nisa'i ya ce: Amintacce ne: Wani lokaci kuma ya ce: ba kakkarfa ba ne. Ibin Haban kuma ya ce: ya kasance yana yin kuskure. Abdullah bin Dauraki kuma daga Ibin Mu'in ya ce: Hadisansa ba su da karfi. Ibin Khasim kuma ya ce: Ba mai karfi ba ne. Aliya Binul Madini kuma ya ce: Ibin Khasim ya ce: Ana kiya masa hadisi. Ya ambata haka ne a cikin littafin Tahzibit Tahzib, Juzu'i na 5 shafi na 275-276.
4- Abdurrahman Bin Bahman: Wannan kuwa game da shi ibin Madini cewa ya yi: Ba mu san shi ba, kamar yadda ya zo a Tahzibit Tahzib, Juzu'i na 6 shafi na 135.
Wannan shi ne al'amarin sanadin, ko tafarkin wannan hadisi da kuma nassinsa,
karin kuma a kan wannan shi ne cewa yana da sabani da hadisai da dama da suka fi shi kyawun matani da karfin isnadi. Ya zo a cikin hadisan da ake kwadaitar da ziyartar kabarin Annabi (S.A.W.A.) wadanda da yawa daga cikinsu a Kanzul Ummal suke: Juzu'i na 15 shafi na 651 Hadisi na 42582 da 42584. Kazalika ya zo a Juzu'i na 5 shafi na 135 hadisi na 12368 da 12373 kamar kuma yadda ya zo a Sunanul Kubra na Baihaki Juzu'i na 5 shafi na 249 Babin ziyaratul Kuburil Lati fi Baki'i Farkad, da kuma Babu Ziyaratil Kuburus Shuhada. Kamar kuma yadda ya zo a Sunani ibin Majah Juzu'i na 1 shafi na 500 Babu Ma Ja'a fi Ziyaratil Kubur da dai sauran littafa da dama wadanda wannan gurin ya yi kadan ya kidaye su.
Idan ma da a ce mun sallama mun yarda da ingancin wancan hadisin da ya gabata, duk da karonsa da kuma sabawarsa da ya yi da dukkan wadannan hadisan ingantattu, ai wadannan hadisan ana iya daukansu a matsayin shafaffu idan muka lura da maganar Manzon Allah (S.A.W.A.) cewa: "Na kasance na hana ku ziyartar kaburbura, to ku ziyarce su, domin suna tunatar da ku game da lahira" Kanzul Ummal Juzu'i na 15 shafi na 646 Hadisi na 42555...
Wannan kuma duk da cewa musulmi baki daya sun yi ittifakin cewa ziyartar kabari abu ne da yake halattacce. Mun ma karfafa cewa mustahabi ne tare kuma da kasancewar al'ada a kan haka tun zamanin Annabi (S.A.W.A.).
Baihaki ya kawo a cikin littafinsa Sunanul Kubra da waninsa cewa duk wani daren da Manzon Allah (S.A.W.A.) ya kasance a Dakin A'isha yakan fita a karshen dare zuwa makabartar Baki'a yana cewa: "Aminci ya tabbata gare ku gidajen mutane muminai, kuma abinda aka muku alkawari ya zo gare ku." Ya ambata wannan a Juzu'i na 5 shafi na 249. Nisa'i ma ya ambata a littafinsa Sunan a kitabul Jana'iz Babu Ziyaratu Kuburil Mushrikin, da kuma Abu Dawud a littafinsa Sunan a sashen Ziyaratul Kubur Hadisi na 3234 da kuma Ibin Majah a littafinsa sunan a Babin Ziyartar kaburburan Mushirikai cewa Annabi (S.A.W.A.) ya ziyarci kabarin Mahaifiyarsa har ya yi kuka sa'an nan wadanda ke kewaye da shi ma suka yi kuka. Tare kuma da kari a kan cewa akwai hadisai da dama da aka ambata wadanda ke nuna
( 34 )
dai ma wani nau'i ne na kusaci ga Allah Ta'ala ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusaci gare Shi ta hanyar gaishe da marar lafiya, da raka gawa zuwa kabari, da ziyartar 'yan'uwa a addini, da kuma taimakon fakiri.
Don zuwa gaishe da marar lafiya shi a kan kansa, alal misali, kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusaci ga Allah ta hanyarsa, ba neman kusaci ga marar lafiyar ba ne da zai zamar da aikata shi ya zama bauta ga wanin Allah Ta'ala ko kuma shirka a bautarSa. Kazalika sauran misalan kyawawan ayyuka irin wadannan wadanda a cikinsu har da ziyartar kaburbura, da gudanar da bukukuwa, da rakiyar gawa zuwa kabari da kuma ziyartar 'yan'uwa.
____________
cewa Annabi (S.A.W.A.) ya kasance yana koya wa A'isha yadda ake addu'a idan an ziyarci kabari.
Idan ma har muka kyale duk wadannan muka koma ga hadisin da suka dogara da shi muka yi nazarin sa tare da kawar da kai daga dukkan abubuwan da muka ambata to sam ba za mu sami wata ishara a cikinsa manyan malaman hadisi da malaman fikihu sun hukunta makaruhancin ziyartar kaburbura ne ga mata kawai.Ga nassin abinda Baihaki ya kawo a littafinsa Sunanul Kubra Juzu'i na 4 shafi na 78. Ya ce: "Lalle Fatima 'Yar Annabi (S.A.W.A.) ta kasance tana ziyartar kabarin kawunta Hamza kowace Juma'a tana yin salla tana kuma kuka a gurin... Sa'an nan kuma sai ya ce; kuma mun riga mun ruwaito a hadisi tabbatacce daga Anas bin Malik cewa Manzon Allah (S.A.W.A.) ya wuce wata mata tana kuka a gurin wani kabari tana kuka sai ya ce; " Ki ji tsoron Allah ki yi hakuri" kuma a wannan hadisin babu cewa ya hana ta zuwa Makabarta, sai dai kuma a cikin wannan akwai karfi a kan abinda muka ruwaito daga A'isha sai dai kuma mafi ingancin abinda aka ruwaito a kan hakan hadisa bayyanan, shi ne hadisin Ummu Atiyya da kuma hadisan da suka yi daidai da shi, cewa; idan da su tsarkaka daga rakiyar gawawwaki zuwa makabarta da kuma fita zuwa makabarta da ziyartar kaburbura to da haka ya fi musu dacewa". A nan maganarsa ta kare.
Hadisin Ummu Atiyya kuwa shi ne " Ta ce an hane mu rakiyar gawawwaki zuwa makabarta, Kuma bai wani nauyaya a kanmu ba." Sunanul Kubra Juzu'i na 4 shafi na 77 kuma ya ce Muslim ma ya ruwaito shi a cikin Sahihi Muslim ta fuskoki biyu daga Hisham. Da kuma Sunanu Ibin Majah Juzu'i na 1 shafi na 502 hadisi na 1577.
Idan ana bukatar Karin bayani sai a duba littafin `Kashful Irtiyab fi Atba'i Muhammad bin Abdulwahab wanda Sayyid Muhsin Al- Amin Al- Amuli ya rubuta.
( 35 )
Amma kasancewar ziyartar kaburbura da bukukuwan addini a matsayin kyawawan ayyuka a shari'a al'amari ne da fannin fikihu ke tabbatar da Shi ba nan ne gurin tabbatar da Shi ba.
25
Manufa ita ce cewa aikata irin wadannan ayyukan ba sa daga cikin shirka a ibada kamar yadda wasu suke rayawa kuma ba ma ana nufin bauta wa Imamai da su ba ne, abin nufin da su kawai shi raya al'amarinsu, da kuma sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin addinin Allah da tare da su
"wancan duk wanda ya girmama alamomin addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyakun ibadar zukata." Surar Hajj: 32.
____________
25- Alal misali za mu ambata misali daga sunna da kuma tarihin rayuwar Annabi (S.A.W.A.) da kuma na Zuriyarsa dangane da fifita wadannan irin kyawawan ayyuka. Akwai misalin abinda Bukhari ya ruwaito a Sahihul Bukhari a Babin Fadha'ilil Sahaban Nabi juzu'i na 4 shafi na 204 daga Annabi (S.A.W.A.) "Masu kuka su yi kuka ga Mutum kamar Ja'afar." Kazalika Annabi (S.A.W.A.) ya sunnata kuka ga Hamza ya ce: "Masu kuka su yi kuka ga mutum kamar Hamza". A duba littafin Tabakat na Ibin Sa'ad Juzu'i na 2 shafi na 44 da kuma littafin Magazi na Wakidi Juzu'i na 1 shafi na 317, da Musnad Ahmad Juzu'i na 2 shafi na 40. Nisa'i ma ya ambata shi a cikin littafinsa Sunan a kitabul Jana'iz Babu Ziyarati Kuburil Mushrikin, da kuma Abu Dawud a littafinsa sunan a Ziyaratul Kubur hadisi na 3234 da kuma Ibin Majah a littafin Sunan a Babu Maja'a fi Ziyarati Kuburil mushrikin: Cewa Annabi (S.A.W.A.) ya ziyarci kabarin mahaifiyarsa ya yi kuka ya sa wadanda ke tare da shi suka yi kuka.
Kazalika kukan Fatimatuz-Zahra (a.s.)ga mahaifinta, kukan Zainab 'yar Amirul Muminin Aliyu bin Abi Talib (a.s.) ga yayunta Hasan da Husaini (a.s.), Imam Sadik (a.s.) ya ce: Imam Husain (a.s.) ya ce: Ni wanda aka kashe ne don in zama darasi, babu muminin da zai tuna ni face ya yi kuka." [ Littafin Kamiluz Ziyarat shafi na 108] har ila yau kuma ya kara da cewa: Nisawar bakin ciki saboda mu tasbihi ne, himmar yinsa saboda mu kuma ibada ne, boye asirinmu kuma jihadi ne a tafarkin Allah" Biharul Anwar juzu'i na 44 shafi na 278 hadisi na 4.
Imam Ridha (A.S.) kuma ya ce: "Duk wanda ya tuna masifar da ta same mu ya yi kuka kuma ya sa aka yi kuka idonsa ba zai yi kuka ba ranar da idanduna suke kuka, wanda kuma ya zauna a gurin zaman da ake raya al'amarinmu zuciyarsa ba za ta mutu ba ranar da zukata ke mutuwa". Littafin Amali Saduk Majilisi na 17.
( 36 )
7- Imaninmu Game da SiffofinSa Ta'ala
Mun yi imani cewa daga cikin siffofinsa Ta'ala akwai wajiban siffofi tabbatattu na Hakikanin kamala da ake kira siffofin jamal da kamal, wato kyawu da kamala, kamar ilimi da kudura, da wadata, da irada, nufi, da rayuwa wadanda su kansu su ne ainihin zatinSa, su ba siffofi ba ne kari ne dabam a kan zatinSa. Ainihin samuwarSa ba wani abu ba ne a kan zatinSa, kudurarSa kuma dangane da rayuwarSa, rayuwarSa ita ce kudurarSa, Shi mai kudura ne ta yadda Ya ke rayayye, kuma rayayye ta yadda Yake mai kudura, babu tagwaye tsakanin siffofinSa da samuwarSa, haka nan kuma a sauran siffofinSa na kamala.
Na'am siffofinSa sun sha bamban a ma'anoninsu da manufofinsu amma ba wai a hakikaninsu da samuwarSa ba saboda idan da sun kasance haka to da lalle Ya kasance an sami wajibabbun samammu da dama kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ba wannan kuwa ya saba wa Akidar Tauhidi.
26
____________
26- Shaikh Muzaffar na ishara da wannan da fadinsa cewa: "Amma fadin cewa daukar abu a kaddare wanda ke nufin cewa siffofi ba su da ayyananniyar ma'ana ta zahiri a sarari, mu mun dauki wannan batun da cewa ba sahihi ba ne, domin Allah Ta'ala Ya siffanta kanSa da cewa Shi masani ne, Mai Hikima, Mai kudura. Shi ne tsantsan kudura, da ilimi da rayuwa, domin Shi zati ne wanda ke da kudura da ilimi da rayuwa, sai dai wadannan siffofin sun sha bamban da ma'anar da ake fahinta ga hankali, domin laffuza ba ma'ana guda suke da ita ba, sassabawarsu a ba da surar ma'ana ne kawai, ba sa sassabawa a siffofi a samuwa, da kuma kasancewa a samuwa, kuma babu adadi a daukar ma'ana kamar yadda suka ambata sai dai akwai adadin maanoni da ke hakaito wannan hakika, wannan kuwa ita ce hakika baki dayanta: Amirul Muminin Aliyu bin
( 37 )
Tabbatattun siffofi kamarsu halitta da arzurtawa kuwa, da gabatarwa, da kuma musabbabi duk alal hakika suna komawa ne ga siffa guda ta Hakika, ita ce kasancewarSa mai tafiyar da al'amuran bayinSa. Wannan ita ce siffa guda wadda siffofi da dama ke samuwa daga gare ta gwargwadon tasirori dabam-daban da kuma la'akari iri dabam-daban.
Amma siffofn da ake kira salbiyya wato korarru wadanda har wa yau ake kiran su siffofn Jalala, siffofi girma, su dukansu suna komawa ne ga siffa korarriya guda, wanda ita ce siffar kore kasancewarSa mai yiwuwar samamme ba wajibin samamme ba, ma'anarsa kore jiki gare Shi, da kore sura, da kore motsi, da kore rashin harka, da kore nauyi, da kore rashin nauyi, da dai sauran makamantansu, wato dai kore dukkan nakasa.
Sa'an nan kuma tushen kore kasancewarSa ba wajibin samamme ba-Shi ne kasancewarSa wajibin samamme, wajabcin samuwa kuwa na daga cikin siffofi tabbatattu na kamala, don haka siffofin Jalala korarru dai a karshe suna komawa ne ga siffofin kamala tabbatattu, Allah Ta'ala kuwa Shi kadai ne Makadaici ta kowace fuska, babu adadin yawantaka a zatinSa, babu kuma hauhawarwa a hakikaninSa makadaici abin nufi da bukata.
Abin mamaki ba zai kare ba ga maganar wanda yake da ra'ayin cewa siffofin tabbatarwa wadanda suke wajibai ga Allah duk suna komawa ne ga siffofin da suke korarru. Saboda haka ne Siffofin da suke korarru. Saboda Ya yi masa wahala ya fahinci cewa siffofinSa su ne ainihin zatinSa, don haka Ya kintata cewa siffofin subutiyya, tabbatattu wajibai ba sa koruwa ga Allah, duk suna komawa ga korarrun siffofi ne domin kawai Ya natsu da fadin kadaitaikar zati da
____________
Abi Talib (A.S.) ya ce: "Duk wanda ya siffanta Shi to ya sanya Shi, adadi..." Ashe ba ya siffanta shi da siffofi da dama ba ne? Abinda yake nufi Shi ne wanda ya siffanta Shi da siffofi kari a kan zatin ta yadda zai zamanto zati adadi-adadi da kuma adadin masu wanzuwa da dama har ya zamanto ya fita daga kasance wajibin samamme." Laccocin marubacin Al- Falsafatul lslamiyya. Shafi na 102.
( 38 )
rashin yawaitarsa sai kawai ya auka a cikin abinda ya fi shi muni, domin zamar da ainihin zati wanda shi ne samuwa, tsantsan samuwa, wanda ba shi da duk wata nakasa, da kore duk wata mafuskanta da ba ta dace da samamme wajibin samuwa ba, Ya sanya shi Ya aininin ma shi ne rashi kuma ainihin korarre,
27 Allah Ya kiyayye mu daga tabewar wahamce-wahamce da kuma tuntubewar duga-dugai.
____________
27- A maganar marubucin akwai ishara ga ra'ayin da Shaikh Saduk ya tafi a kai na cewa: "Duk yayin da muka siffanta Allah Ta'ala daga siffofin zatinSa to muna nufin kore kishiyoyinsu ne kawai daga gare Shi Ta'ala. Muna cewa: Allah Ta'ala bai gushe ba Ya na Mai ji, Mai gani, Masani, Mai Hikima, Mai kudura, Madaukaki, Rayayye, Tabbatacce, Makadaici, Wanzazze, wadannan kuma siffofin zatinSa ne.
Mu ba ma cewa: Shi Azza Wa Jalla bai gushe ba yana mai yawan halitta, mai Aikatawa, Mai so, Mai Nufi, Mai Yarda, Mai ki, Mai Arzurtawa, Mai yawan kyauta, Mai magana, domin wadannan siffofin ayyukanSa ne, su kuma fararru ne bai halatta ba a ce: Allah Ta'ala bai gushe ba ana siffanta shi da su". Littafin Al- I'itikadat shafi na 8.
Ba boyayye ba ne cewa za a iya danganta koruwa da dama ga al'amari guda, domin ma'anar rayuwa ita ce rashin mutuwa, ma'anar ilimi kuwa shi ne rashin jahilci, ma'anar kudura kuwa koruwar gazawa.... haka nan, wadannan korewar dabam-dabam zai yiwu a danganta su ga Zati Makadaici wato ma'ana dai, Allah Ta'ala wanda ya daukaka ga haka, shi tarin korarru dabam-dabam ne, sa'an nan sai kuma Shaikh Muzaffar ya biyar da batun cewa: "Mu muna girmama Shaikh Saduk, a matsayin mai hadisi, mai ruwaitowa, amma idan ya fadi irin wadannan maganganu to ba za mu karbi ra'ayoyinsa ba. Mu muna nufin mu ce ne hakika ba ta yawaita, ta fuskar kasancewa ne ko kuma ta adadi kawai a manufa domin yawa ko adadi ta fuskar kasantuwa ko kuma manufa ba shi da wata ma'ana. Ra'ayin da muka yi imani da shi shi ne abinda Farabi ya ke fadi da cewa:
"Shi Masani ne ta inda Yake Mai kudura ta yadda yake rayayye, rayayye kuma ta yadda yake masani... Wadannan siffofin babu yawan adadi tare da su a hakika ne ko kuma ta fuskar manufa.
Domin fuskar sani ba daban take da fuskar rayuwa ba. Don haka kasancewarsu adadi a fahinta ne kawai abin nufi ne kawai. Kuma ba ma nufin cewa fahintar abin nufi tana nufin ma'ana wanda take fassara hakika, wadda yawanta shi ne kadaitakarta. Mu abinda muke fada shi ne cewa: "Shi masani ne ta yadda yake mai kudura, wadannan kuwa manufofi ne na hakika amma ba wai don cewa suna da samuwarsu ta kai tsaye su ya su ba. Sai dai ma'anar cewa samuwa kanta ita ce ilimin, ita ce kudurar ba wai kudurar kanta samammiya ba ce wadda da wannan samuwar
( 39 )
Kamar kuma yadda mamaki ba zai kare ba ga wanda ke da ra'ayin cewa siffofinSa na subutiyya, tabbatattu, kari ne a kan zatinSa, saboda haka wanzazzu suna da dama kenan, ya kuma wajabta abokan tarayya ke nan ga wajibin samamme, ko kuma kenan ya ce Shi mai hauhawa ne sashe bisa sashe.
28
Sayyyidina Ali Amirul Muminin (A.S.) kuwa Ya ce:
Cikar Ikhlasi gare Shi kuwa shi ne kore siffofi gare Shi saboda shaidar cewa dukkan abin siffantawa to ba shi ne siffar ba, da kuma shaidar cewa dukkan abin siffantawa ba shi ne siffar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi wanda ya tagwaita Shi kuwa ya zamar da Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi."
29
____________
ne, wadda manufarta za ta zama daura da waccan manufar. Saboda haka wadannan siffofin koda yake dai tabbatattu ne da gaske amma a halin kasancewarsu masu yawa ne har ila yau kuma su kadaitaka ne kuma adadin manufofinsu yana bayyana ma'ana ta hakika ne amma dai babu yawaitaka ta fuskar ma'ana. Wannan shi ne kolin al'amari a wannan batu kuma shi ne abinda ya shiga duhu ga tunanin masu maganganun da suka gabata. A duba littafin Falsafatul Islamiyya na Shaikh Muzaffar shafi na 101 zuwa shafi na 102. A kuma duba littafin Tashihul I'itikad na Shaikhul Mufid shafi na 41 da kuma littafin Matarihun Nazar fi sharhil Babil Hadi Ashar na Shaikh Safiyuddin Turaihi fasali na 3 Shafi na 131-162.
28- Marubucin ya yi karin bayani a kan wannan al'amari kamar haka:-
a- Cewa siffofi kari ne a kan zati, kuma su ma wajiban samammu ne to wannan maganar Ash'ari yawa ce.
b- Maganar Karramiyawa kuwa ita ce cewa siffofi kari ne a kan zati sai dai kuma ba lazimai ba ne ga zatin saboda kasancewarsu lazimai zai wajabta kasancewarsu wajiban samammu ya zamanto an samu wajibai da dama.
29- Nahjul Balagha: Huduba ta 1, maganar Amirul Muminin game da fara halittan sama da kasa da kuma Al- Ihtijaj juzu' i na 2 sha i na 473 hadisi na 113.
( 40 )
8- Imaninmu Game da Adalci.
Mun yi imani da cewa: Lalle daga cikin siffofin, Allah Ta'ala, As-Subutiyya Kamaliyya wato tabbatattun siffofin kamala akwai cewa Shi, Adali ne ba azzalumi ba, ba Ya karkacewa a hukuncinSa ba Ya tabewa a hukuncinSa, Zai yi sakayya ga masu biyayya, kuma yana gare Shi Ya hukunta masu sabo, ba Ya kallafa wa bayinsa abinda ba za su iya ba, ba zai musu ukuba fiye da abinda suka cancanta ba.
30
____________
30- Adalci shi ne sakamako a kan aiki gwargwadon abinda aka cancanta a kansa, zalunci kuwa shi ne hana hakkokin Allah Ta'ala kuwa Adali, Karimi, Mai yawan alheri, Mai bayar da alheri don zabinsa, Mai Jin kai, Ya riga Ya ba da tabbacin yin sakamako a kan ayyuka da kuma musanya al'amari ga wanda ya fara alheri ya wahala Ya kuma yi alkawarin ba da kari daga gare shi. Allah Ta'ala Ya ce: "Wadanda suka kyautata suna da kyakkyawa da kuma kari." Surar Yunus aya ta 26. Wato Ya ba da labarin cewa masu kyautata aiki to yana da kwatankwacinsa goma" wato yana da kwatankwacin abinda ya cancanta a kan haka har rubi goma. "Kuma wanda ya zo da mummuna ba za a sakamta masa ba sai dai gwargwadonsa kuma su ba za a zalunce su ba." Surar An'ami aya ta 160. Wato ma'ana ba za a yi masa sakayya sama da abinda ya cancata ba. Sa'an nan kuma Ya ba da tabbacin yafewa kuma Ya yi alkcawarin gafartawa. Allah Ta'ala ya ce: "Kuma lalle Ubangijinka tabbas ma'abucin ga mutane a kan zaluncinsu ne." Surar Ra'ad aya ta 6. gafatawa Kuma yana cewa: "Allah ba ya gafarta cewa a yi shirka da shi amma Yana gafarta abinda ba wannan ba ga wanda Ya so" Surar Nisa'i aya ta 48.
Kuma Allah Ta'ala Ya yi umarni da a yi adalci kuma Ya hana yin zalunci. Allah Ta'ala Yana cewa: "Lalle Allah Yana umarni da adalci da kuma kyautatawa." Surar Nahl aya ta 90.
Da kuma Tashihul I'itikad na Shaikh Mufid shafi na 103.