Logo

AYATULLAHIL UZMA
SIDI ALI HUSAINI SISTANI


(ALLAH YA TSAWAITA RANSA)





Wanda Ya Fassara: Y.A. Ningi
Wanda Ya Buga: Mu’assasar Imam Ali (A.S.)



Sunan Littafi: Tarihin Rayuwar
Ayatullahil Uzma Ali Sistani
Wanda ya fassara: Yakubu Abdu Ningi
Adadi: 3000
Shekarar da aka Buga: 1418, 1997
madaba’ar da ta Buga: Mihir
Hakkin Mallaka: Mu’assar Imam Ali (A.S.)






Babu shakka Mumbarin Marigayi Imam Khu’i a cikin sama da rabin Karni ya horar da gwarzaye fitattu gogaggu wadanda suka zamanto su ne mafiya hazaka da daukakar baiwa a fagen musulunci da fannonin ilimi da al’amura babam-daban da Kuma matakan Musulunci masu muhimmanci, yayin da ya tarbiyyantar da daruruwan mamsanan fikihu da mujtahidai da ma’abuta daraja da daukaka wadanda suka dauki nauyin ci gabar da tafarkin musulunci da hidima da ilmantarwa, da Kuma al’amuran zamantakewa wadanda yawancinsu a yau su ne mafi yawan malaman makarantu da cibiyoyin ilimin addinin musulunci musamman ma a garin Najaf da Birnin Kum Mai tsarki wadanda suka kai matsayin wadatarwa da shahara a ilimi da halin zaman jama’a, hakan kuma ya ba su damar cancantar daukar nauyin tarbiyyantarwa da koyarwa da matsayin Marja’i da al’umma ke komawa gare su don sanin hukunce-hukunen shari’a, da matsayin Jagoranci da tafi da al’umma a wannan zamanin.
Daga cikin wadannan fıtattun gawarzayen akwai Ayatullahil Uzma Aliyu Sistani, Wanda shi yana daya daga manyan daliban Imam Khu’i (R.A.),a kamala da ilimi da falala da dacewa. Abinda ke biye takaitaccen tarihin rayuwarsa ne:-

1. Haihuwarsa da Tasowarsa


An haifi mai martaba Ayatullahil Uzma Aliyu
Sistani ne a garin Mashhad birnin da Makwancin Imam Ridha (A.S.) Imami na takwas daga zuriyar gidan Manzo (SAWA) yake a shekarar 1349 Hijriyya, a watan Rabi’ul Awwal, wato shekarar 1931 Miladiyya.
Bayan ya kammala karatunsa na elemantare da mukaddima da na marhalar tsakatsaki nan da nan sai ya ci gaba da bibiyar darrusan aiki da hankali da kuma fannin sanin Ubangiji a gurin manyan malamai masanan wadannan fannoni kuma masu koyar da su; har ya samu ya dandake su da kyau. Daga bisani sai ya shiga marhalar karatun share fagen ijtihadi a nan garin Mashhad inda ya amfana daga irin ra’ayin Malami mai yawan sani kuma ma’abucin binciken nan Allama Mirza Mahadi Isfahani (R.A.). Daga nan kuma sai ya tashi takanas zuwa makarantar ilimin addini da ke garin ilimi na birnin Kum a zamanin babban malami kuma Marja’i Sidi Husaini Burujurdi (R.A.) a shekakar 1368 Hijiriyya wato shekarar 1948 Nasariyya inda ya halarci darusan manyan malamai ma’abuta daraja ciki har Ayatullah Burjurdi a fannonin fikihu da Usuli kuma ya amfana sosai daga kwarewarsa a fannin fikihu da kuma irin ra’ayinsa a ilimin sanin maruwaitan hadisi, da fannin hadisin kansa kamar kuma yadda ya halarci darusan fikihu a gurin babban malamin nan ma’abucin daraja Sidi Hujjat Kauhakmari (R.A.) da kuma Sauran Malamai ma’abuta falala a zamanin.
Bayan ya yi shekaru uku cif-cif ne kuma sai ya sake daura damara ya tafi garin Najaf cibiyar ilimin addini inda ya duka karatu a gaban taskokin ilimi da tunanin wancan zamanin kamarsu Imam Hakim da shaikh Husain Hilli da Imam Khu’i Allah Ya kara musu rahama. Ya lizimci darussan Sidi Imam Khu’i a fikihu da kuma Usulul fikihi sama da shekaru goma kamar kuma yadda ya karanci usulul Fikihi daga farko har karshensa a gaban Shaikh Hilli.
Tun daga shekarar 1381 Hijiriyya wato 1961 Miladiyya ya dukufa wajen ba da Laccoci ga darussan share fagen matakin farko na ijtihadi a bisa asasin littafin Makasib na shaikhul A’azam Al- Ansari (R.A.) Kana ya biyar da sharhin littafin Urwatul Wuthka na Sidi Fakihi Tabataba’i (R.A.) inda tun a wancan lokacin ya kammala sharhin kitabut Tahara da kuma yawancin furu’in kitabus Salat da wani sashe na Kitabul Khums. Kamar kuma yadda ya fara bayar da darasin Usuli a shekarar 1384, 1964 inda ya kammala a bisa salon ba da laccoci ga masu shirin zama Mujtahidai, a watan sha’aban shekarar 1411, dalibansa sun rubuce darrusansa na Usuli da Kuma Fikihi.

2.iliminsa

Shi dai Sidi Sistani ya fito sarari ne a darrusan malamansa inda ya kasance yana yi wa abokan karatunsa fintinkau ta hanya taso da wasu matsaloli na ilimi da kuma gaggawar ba da ra’ayinsa da yawan bincike da bin diddigin al’amuran fikihu da ilimin masu ruwaito hadisai da dawwama a kan harkar ilimi da kuma sanin da dama daga cikin fannoni dabam-daban a ilimin makarantun addini. Ya kasance tsakaninsa da shahid Bakir Sadr akwai tserarreniya ta fuskar daukaka da cigaba a ilimi, wannan kuwa abu ne da shaidar Imam Khu’i a rubuce da kuma wadda Allama shaikh Husain Hilli (R.A.) suka tabbatar da isar sa ga matsayin Ijtihadi a shekarar 1380 Hijiriyya suna masu yabo gare shi da kuma girmama falalarsa da iliminsa. Abu guda da aka sani game da Imam Khu’i shi ne cewa bai taba ba da shaidar Ijtihadi rubutacciya ga kowa ba sai ga shi Sidi Aliyu Sistani da Kuma Ayatullahi Shaikh Ali Falsafi daga cikin manyan malaman Mashhad. Shaikh Allama Agha Buzurg Tehrani wanda shi ne babban malamin hadisin zamaninsa shi ma ya ba wa Ayatullahi Sidi Aliyu Sistani rubutacciyar Shaida yana yaba gogewarsa a kan ilimin sanin maruwaita. Wato ma’ana Shi ya riga ya sami wannan shaida ne daga manyan malamai game da wannan matsayi tun yana da shekara talatin da daya.

3. Rubuce - Rubucensa
Tun daga shekaru 34 da suka wuce ya fara koyar da Fikihu da Usul da Ilimin sanin masu ruwaito hadisai a marhalar tarbiyyantar da Mujtihidai yana ba da gudummawa mai amfani game da littafin Al-Makasib, da Tahara, As Salat da Alkhadha’u da Al-Khums kamar kuma yadda ya yi a kan Kawa’idul Fikhiyya banganren da ya shafi Riba, da Ka’idatut Takiyya, da Ka’idatul Ilzam. Kazalika ya koyar da Usulul Fikihi daga farko zuwa karshensa har sau uku kuma wasu bayanansa suna nan an tsara su daidai yadda za a iya buga su a matsayin Littafi kuma bayanansa a “Usulul Amaliyya” da “Ta’adul” da “Tarajihu” da kuma wasu bayanai na fikihu a babin Salla da kuma “Ka’idatul Takiyya” da “Ilzam”. Koyarwarsa ta tarbiyyantar da manyan dalibai wadanda hatta wasunsu sun kai ga koyar da darasin share fagen Ijtihadi; kamarsu Allama Shaikh Mahdi Marwarid da Allama Sidi Habib Husainani, da Allama Sidi Murtadha Isfahani, da Allama Shaikh Bakir Irawani da sauransu da dama da ke daga cikin manyan makarantun addini. A halin yana koyarwa da tarbiyyantar da dalibai har ila yau yana ta rubuce-rubuce domin wadata makarantun addini da littafan da ake bukata baicin kuma rubuce koyarwar malamansa da ya kasance yana karatu a gurinsu.
Ga Sunayen wasu daga cikin rubuce-rubucensa kamar haka:-
1- Sharhul Urwatul Wuthka - Littafin fikihu mafi girman matsayi da ake karantawa.
2- Kitabul kadha
3- Al- Buhuthul Usuliyya
4- Kitabul Bai’i wal Khiyarat
5- Risalatun Fil Libasul Mashkukun Fihi
6- Risalatun Fil Ka’idatul Yadi.
7- Risalatun Fi Salatul Musafir
8- Risalatun Fi Ka’idati Tajawuz Wal Farag.
9- Risalatun Fil Kibla
10- Risalatun Fil Takiyya
11- Risalatun Fi Ka’idatul Ilzam
12- Risalatun Fil Ijtihadi Wat Taklid
13- Risalatun Fi Ka’idati La- Dharara
14- Risalatun Fir Riba
15- Risalatun Fi Hujjiyyati Marasilu bin Abi Umair.
16- Nakdi Risalata Tashihil Asanid Lil Ardabil
17- Sharhu Mashikhatut Tahzib
18- Risalatun Fi Masalikil Kudama Fi hujjiyyatul Akhbar.
Wadannan duk kari ne a kan rubuce rubucensa a wasu fannonin da kuma Risala babbab a kan hukunce-hukuncen ayyukan ibada don masu yi masa takalidi suna bin hukunce-hukunce da fatawarsa.

4. Salon Koyarwarsa

Tafarkin koyarwarsa ya bambanta sosai da tafarkin da aka sani a makarantun addini. A fannin koyar da Usul ya kebantu da mafi muhimmancin kebabbun hanyoyi kamar haka:-
A) Bayanin tarihin fanni da asasinsa:
Mai yiwuwa yana iya zama na falsafa ne kamar matsalar “Basatatul Mushtak Wat Tarkibihi” ko kuma na akida ko na siyasa kamar misalin “Ta’adul Wat Tarâjih” wanda a ciki ya bayyana al’amarin sabanin hadisai wadanda arangamar ra’ayoyi da akidu ta jawo tare kuma da yanayin halin siyasa da ke kewaye da Imamai (A.S.) a wancan zamanin Wanda Kuwa abu ne a sarari cewa sanin tarihin irin wannan binciken zai fito mana da bangarorin al’amarin sarari ya kai mu ga hakikanin al’amarin ra’ayoyin da aka bayyana.
B) Kulla tsakanin tunanin makarantun addini da kuma
Zamani, a bayani game da “Ma’anil harfi” da “Ma’anil Ismi” kan cewa shin bambancinsu “Zati” ne ko Kuma “Lihazi” ne sai ya gina shi a kan fahimta irin ta falsafa ta zamani wadda ita ce fahimtar “Takathirul Idrâki” fi fa’aliyyatiz Zihni Bashari wa Khallakiyyatihi” Kuma abu ne mai yiwuwa ga hankalin dan Adam ya suranta abu guda ta fuska biyu. Wani lokaci kai tsaye kuma a bayyane wannan shi ake kira suna, wani lokaci da wasila da tsani a dunkule wannan shi ake kira harafi. Yayin kuwa da ya shiga bayani game da “Mushtak” a kan sabanin da ke tsakanin malamai game da sunan da ya kebantu da zamani “Ismuz Zaman” Sai ya bayyana “Zaman” din da fahinta irin ta falsafar yammaci wato ciro ma’anar “Zaman daga “Makan” abinda ake kira “Zamkan” saboda la’akari da bibiyar da ke tsakanin haske da duhu. Bayaninsa game da abinda sigar umarni ke nufi da kuma gundarinsa, da kuma bayani game da “tajarri” sai ya kawo ra’ayin malaman ilimin halin zaman jama’a dangane de kasafin bukatar abu ta hanyar bukata irin ta umarni da kuma ta roko da kuma ta tambaya saboda shisshigar juna da bangarorin bukata da roko da tambaya saboda kasancewar wanda ya bukatar na sama ne ko tsara madaidaici ko kuma na kasa da wanda aka bukatar daga gare shi.
Hakanan ya sanya Ka’idar sanya Ukuba a kan tsaurin kan bawa ga Ubangidansa wannan shi ma an assasa shi ne a bisa asasin halin zamantakewar dan Adam irin ta da can, wato kasancewa akwai Ubangida da kuma bawa, Madaukaka da kuma Makaskanci da makamancin wannan. Wannan ra’ayi ne da aka gina shi a bisa tunani irin na kasa al’umma dabaka - dabaka ba a bisa dokokin maslaha da amfani ‘yan Adamtaka ba.
C) Himmatuwa da Usulin da ke hade da fikihu
Sau da yawa dalibi zai ga cewa zurfafawa a karatun usuli ko koyarwarsa daga bangaren malamai da dama ba ya haifar da wani sakamako na aikace sai dai kawai a tunani da ra’ayi wato kamarsu bincike game da sanya sunaye da kasancewarsa al’amarin surantawa kawai ko kuma a halitta, ko kuma kasancewar kebewa ko kudara aniya, da kuma bayanansu game da abin binciken ilimi da dai makamantansu. Amma abin lura da darasin Sidi Aliyu Sistani shi ne zurfafawa da kokartawa wajen fitowa da ra’ayin bincike kakkarfa da ke hade da aikin tsamo hukumce-hukunce, kamar bayani game da Usulu Amaliyya da At- Ta’adul da At- Taraji da “Amun” da “Khassun”. Sauran al’amuran koyarwarsa ma daidai fada daidai aiki yake yin su.
D) Sabuntawa da Tajdidi
Daga cikin malaman makarantun addini akwai kwararru da dama wadanda ba su da kudurar sabuntawa da kawo canji sai dai kawai su mai da hankalinsu su dukufa a sharhi da karin bayani da takaituwa a kan kyawun wani bincike ko bayaninsa ba wai su kawo sabon ra’ayi a kan asasin ra’ayoyin da ke akwai ba ballantana ya yawata a cikin ra’ayoyi ya zabe na zabewa ba, sai dai kawai kara bayani a kan maganganu irinsu; “Ta’ammal” ka kuma “Fatham” wato yi tunani, ko kuma ka fahimta idan kuma ya taso da matsala sai ya tsaya a kan kawo mushkila daya ko biyu kana ya tsaya.
Shi Sidi Aliyu Sistani da Shahidi Sadir sun sha bamban da kowa a kan wannan tafarkin, kowa daga cikinsu yana kokari ne ya ba da sabuwar siga da ta dace da bukatar da ake da ita a kan binciken. Wato kamar yadda shi Sidi Sistani ya yi yayin da ya fara bayanin aiki da lafazi da ma’anoni dabam - daban. Domin su Malaman Usuli sun yi bayanansu ne ta bangaren, yiwuwa da kuma korewa, ta Imkan Wal Istihalah, a matsayin bincike na aikin hankali da kuma Falsafa Wanda ba shi da wata fa’ida ta aiki, shi kuwa sai ya bayyana shi ta fuskar aukuwa da kuma rashin aukuwa, Al-Wuku’u Wal adam domin ya fi “imkan” karfi kamar kuma yadda ya yi bayaninsa ta fuskar neman bayyanan -al- Istizhar.
A fannin “At- Ta’adul Wat Tarajih” kuwa gani ya yi cewa sirrin wannan “bahasin” La’alla yana komawa ne ga sabanin hadisai, saboda idan har muka bincika su muka kayyade dalilan sabanin nassosin shari’a to mushkilar mai tsanani ta warware ke nan wadda da’iman take ci wa mai bincike da mai amfana daga hadisan Ahlul Baiti (A.S.) tuwo a kwarya, wannan kuwa zai wadatar da mu ga barin ruwayoyin “tarjih wat tagyir” kamar yadda mai kifayah ya yi game da “Istishab” wato sashen tabbata a kan abinda ya kasance kana da tabbaci game da shi. Wannan irin bincike ma Shahid Sadir ya tabo shi, sai dai shi ya gina nasa ne a bisa asasin hankali zalla, shi kuwa Sidi Sistani ya taro hujjoji ne na tarihi da na zamani sai ya fito da muhimman ka’idojin warware sabanin sa’an nan kuma ya shiga koyar da su a darasin fikihu.
H) Gwama Tsakanin Ra’ayoyi Mabambanta
Abinda aka fi sani a gurin da dama daga cikin Malamai shi ne takaituwa da koyar da wani tafarki ayyananne ko kuma wata manufa ta musamman amma abinda aka sani daga Sidi Sistani shi ne hadowa da kuma gwama tsakanin ra’ayin karantarwar Mashhad da ra’ayin Makarantun Kum da Tafarkin Malaman Najaf. Yakan kawo ra’ayoyin Mirza Mahdi Isfahani (R.A.) da na Sidi Burujurdi daga Makarantun Mashhad, da ra’ayoyın manyan malaman uku da kuma na Sidi Khu’i (R.A.) da Shaikh Husain Hilli (R.A.) a matsayin makarantar Najaf, wadannan ra’ayoyin da tafarkunan kuwa taro su guri guda yana ba da wadatacciyar hanya gare mu da kuma mayalwaciyar manufar ilimi gare mu.
A fannin fikihu ma yana da tafarkin koyarwa na musamman da ya bambanta da da sauran hanyoyin, salon koyarwar tasa ya kebantu da abubuwa kamar haka:-
A) Auna tsakanin Mazhabar Shia da Sauran Mazhabobi da ba na Shi’a ba
Domin fahintar fikihun Mazhabar Ahlussunna da ya yi zamani da lokacin nassi kamar su Muwatta Malik da Kharraj Abi Yusuf da makamamtansu yana nuna mana munafar Imamai (A.S.) yayin kawo nassi.
B) Sabunta Abubuwan Kaddamarwa
Abu sananne a gurin mafi yawan manyan Malamanmu shi ne cewa suna karbar ka’idojin Fikihu ne kawai kamar yadda magabata suka kawo ba sa kara kome sai dai game da ingancin abinda aka dogara da shi ko kuma cewa babu wata madogarar ta dabam. Amma shi kuwa Sidi Sistani yakan yi karin sigar ka’idojin a wasu sassa. Alal misali dangane da Ka’idar “Ilzam” wadda wasun malamai suke ganin ta bangaren cewa Musulmi Mumini zai iya amfani da ita wajen cim ma manufarsa ko biyan bukatarsa ta kansa daga Ka’idojin wasu Mazhabobi na dabam koda kuwa shi ba ya bin wadannan mazhabobin. Shi kuwa Sidi Sistani yakan bullo ne ta fuskar girmama ra’ayi wato girmama ra’ayin wasu da dokokinsu, inda yakan zo da sigar cewa kowace al’umma akwai irin aurenta.
C) Amfani da dokokin zamani a wasu Bangarori na Fikihu
Kamar inda ya waiwaici dokokin Iraki, da Masar da na Faransa yayin da yake bincike game da cinikayya, da kuma kewayewa da dokokin zamani wajen fayyace ka’idojin fikihu da yalwata madogararsu da guraren aiki da su.

5. Mutumtakarsa

Duk wanda ya zauna tare da Sidi Sistani ko kuma yana da wata sadarwa da shi zai ga irin mutumtaka da daukakar ruhin da yake da ita irin wadda zuriyar gidan Manzon Allah (SAWA) suka kwadaitar a kanta da ke sanya shi shi da makamantansa su zama malaman da ake cewa “Malaman Allah” da kuma fadin Imam (A.S.) cewa: “Magudanar al’amura na hannun Malamai aminan Allah a bayan kasa a kan halalinSa da haram dinSa.” Ga misalan wasu daga cikin abubuwan da na lura da su daga gare shi yayin da nake halartar karatu a gurinsa:-
A) Insanfi da mutunta ra’ayi
Sidi Sistani, saboda shauki da yake da shi game da ilimi da neman sani da kwadayin isa ga hakika da kuma girmama’yancin ra’ayi sau da yawa zaka iske shi yana karanta littafan Malamai da marubuta dabam-daban hatta na abokan karatunsa kuma za ka iske shi yana ambato hatta ra’ayayin wadanda matsayinsu na ilimi bai kai nasa ba ko kuma ya kawo ra’ayinsu a yi muhawara a kai, wannan abu ne da ba a san malamanmu da irinsa ba.
B) Ladubban Muhawara
Makarantun addinin Musulunci a garin Najaf sun shahahara da muhawara ta ilimi tsakanin malamai da dalibai wanda hakan kan sanya dalibi ya goge wajen al’amuran ilimi. Wasu lokutan ma har muhawar takan wuce iyaka ta zama jayayyar da ba ta da wata riba ta ilimi. Shi kuwa Sidi Sistani muhawararsa da Malamai ko da dalibansa yakan yi ta ne da wani hali da ladubba na musamman wajen kaiwa ga manufa ta amfanar ilimi koda kuma wani daga cikin dalibansa ya yi zarbabiyar zartar da muhawararar zuwa da’ira jayayya yakan yi kokarin maimaita amsarsa cikin natsuwa da ladubban magana idan kuwa dalibi ya cije a kara’ayinsa to shi ya fi zabin ya yi shiru maimakon ci gaba da muhawarar da ba ta da ribar ilimi.
C) Halayyar Tarbiyya
Koyarwa ba wani aiki ne da Sidi Sistani ke yi don a ba shi albashi. Don wannan kan nesanta malami daga daidaita dalibinsa da kulawa da shi da isar da shi ga matsayin ilimi da daukaka da fita sarari; kamar yadda koyarwar ba wai kawai don tarbiyyar dalibi da kuma kai shi ga matsayin ilimi ba kawai sai dai kawai don sauke muhimmin nauyin da yake bukatar ruhin soyayya da tausasawa ga dalibai kamar yadda Sidi Imam Khu’i ya kasance yana yi da dalibansa. Dimin da’iman bayan darasi yakan kwadaitar da dalibai su yi tambaya yana cewa ku yi tambaya mana koda game da lambar shafi; ko kuma wani darasi ayyananne ko kuma littafi ayyananne ko kwa saba da muhawara da malami, kamar kuma yadda ya kasance yana sa dalibansa kintata tsakanin abinda ke rubuce da kuma wanda ake ji a gurin darasi, yana kuma yin ta’akidi koyaushe a kan girmama malamai da kuma kiyaye ladubban magana da muhawara da tattaunawa yayin magana da malamai, akwai misalan wannan da dama da dabi’arsa.
D) Wara’u, kankan da kai
Bincike da bayanai a garin Najaf wata dama ce ta fitowa sarari a tsakamin Malamai kuma ta yi nesa da taso da fitina, koda yake wasu suna ganinsa a matsayin abu da bai dace ba amma kuma akwai Maslaharsa da fa’idarsa wani lokaci domin idan har aka samu wata karkata to lalle ne malamai su fito fili, idan bidi’a ta bayyana wajibi ne ga malamai su bayyana iliminsu idan kuwa ba su yi ba to an zare musu hasken imani, kamar yadda ya zo a hadisi. Sai dai kuma idan haka zai zama fitina da ka iya cutar wa ga mutuncin wani mai matsayin addini ayyananne ko kuma tafarki ayyananne ko kuma akwai yanayin yakayyar ra’ayi da maganganu kamar yadda yake aukuwa sau da yawa yadda har takan kai ga hassada da kullace juna, Malamai da dama cikinsu har da su Sidi Sistani kan lizimci natsuwa da wara’u, wato kau da kai kamar yadda ya auku zamanin rasuwar Sidi Burujurdi da Sidi Hakim (R.A.) kamar kuma yadda yake a wannan zamanin Sidi Sistani ya yi riko da tufafinsa na zuhudu da zamansa a karamin gidansa da babu wasu kayan alfahari a ciki.
E) Auren Mushirikai
Ka’idar “Lizimtarwa” wadda yawancin malaman fikihu da na usul ke kawowa, wato kamar ka’idar hankali ko ta ma’abuta hankali tsantsa. Sidi Aliyu Sistani a karkashin ka’idar “Idhdirar” matsuwa wadda ke kaiwa ga ka’idar “tazahum” mai matsuwa da juna da kaiwa ga kunsa fahintar sanya ma’ana ta aiki. Wani lokaci kuma yakan kara fadada ka’idar kamar yadda yake a ka’idar “La tu’adu” wadda yawancin malamai sukan kebance ta ga salla kawai saboda nassi a kan haka amma shi kuwa Sidi Sistani sai ya kama ma’anar cewa “La tu’adu Salati illa min khamsatin”a farkon ruwayar don nuna cewa ta hada da salla ne da kuma abinda ba salla ba na daga wajibai da kuma cewa karshen hadisin na bayyana cewa “Sunna ba ta warware farilla” wato ma’ana ka’ida ita ce gabatar da farilla a kan sunna a salla da kuma watanta na daga ayyukan da ke tabbatar da gaskiyar wannan gabatarwar lokaci da kuma Alkibla da dai sauransu daga bangarorin salla da sharudanta domin lokaci da Alkibla suna daga farillan salla ne ba sunnoni ba.
F) Nassi game da Halin Zaman Jama’a
Daga cikin malaman fikihu akwai malaman harafi wanda kawai yana kankame ne a kan fahintar nassi kawai ba tare da kokarin fadada fahimta da yalwata ma’ana daga nassin ba, kazalika akwai daga cikin masanan fikihu wanda ke karanta yanayin nassi da sharudan da ke gewaye da shi domin ya kara gane al’amuran da ke da tasiri wajen kaiwa ga manufarsa. Alal misali ya zo daga Manzon Allah (SAWA) cewa yana haramta cin naman jakunan gida ranar Yakin Khaibar, don haka idan muka dauki ma’ana ta harafi to da mun ce ya haramta ko ya zama makaruhi game cin naman jakin gida. Idan kuwa muka duba bangaren halin zaman jama’a game da nassin za mu ga cewa yana duba tsanani da halin wahalar yaki ne da Yahudawa a Khaibara, yaki kuwa yana bukatar daukar makamai daga wani guri zuwa wani guri da kuma daukar kayan taimako kuma babu abin daukan kaya a lokacin sai dabbobi kuma jakin gida na daga cikinsu. Saboda haka alal hakika hanin na iya tafi da shugabanci saboda wata maslaha ko Ka’ida ayyananniya da yanayin da ake ciki ya haifar a wancan lokacin don haka ba za a dauke shi a matsayin haramcin Shari’a ko karhanci ba. Sidi Sistani na daga cikin masu ra’ayi na biyun da muka bayyana.
G) Cikakkiyar kwarewa game da guraren tsamo hukunce-hukunce
Sidi Sistani a kodayaushe yana ta’akidi cewa lalle Masanin fikihu ba zai zamanto masanin fikihu na sosai ba har sai ya samu cikakkiyar kwarewa game da maganganun Larabawa da wake-wakensu da adabinsu kafin ya zamanto yana da karfin ayyana abinda nassi ke nufi filla-filla ba a dunkule ba, kazalika babu makawa ya zamanto ya lakanci lugga da kyau tare da sanin halayen marubutanta domin yin haka yana daga cikin abubuwan da ake dogaro da su a lugga ko kuma ke hana dogaro da su. Kazalika Lalle ne fakihi ya san hadisan Ahlul Bait (A.S.) da masu ruwaito su, dalla dalla domin ilimin sanin maruwaita yana daga abubuwan da babu Makawa Mujthidi ya zamanto yana da su domin ya zamato yana da tabbaci game da ingancin abinda ya dogara da shi. Shi Sidi Aliyu Sistani yana da ra’ayoyi da ya kebantu da su wadanda suka saba wa Jamhurin Malamai. Alal misali suka da rashin dogaro da Ibin Fadha’iri al’amari ne da yake mashahuri ko domin saboda yawan suka gare shi ko kuma saboda rashin dogara da shi wajen raunanawa da kuma tantance adalcin maruwaita, amma shi Sidi Sistani bai yarda da wannan Mashahurin ra’ayin ba yana ganin cewa littafin tabbatacce ne kuma shi Ibinul Fadha’iri ya fi Najjashi da Shaikh zama abin dogara a fannin suka da kuma tantance adalcin Maruwaita kazalika yana da ra’ayin dogaro da tafarkin at-Tabakat wajen ayyana mai ruwaya da tabbatar da gaskiyarsa, kuma wajen tabbatar da cewa hadisi mai cikakken Isnadi ne ko mai yankakken Isnadi yana bin tafarkin Sidi Burujurdi (R.A.) ne. Kazalikia Sidi Aliyu Sistani yana da ra’ayin lalle ne a san littafan hadisai da sababaninsu da kuma sanin halin marubucin hadisan ta bangaren tsari da ka’ida da tabbataccen tafarkin talifi, da kuma abinda yake ya yadu game da wannan kan cewa Shaikh Saduk ya fi Shaikh Tusi Ka’ida bai amince da shi, shi dai kawai yana ganin Shaikh Tusi a matsayin Mai daukar hadisi ne kawai Mai gaskiya saboda abinda ya gani a littafa da kuma alamomin da ya dogara da su.
Wannan bangare game da hadisai ba kowa ba ne daga cikin malamai yake dogaro a kansa a wajen tsamo hukunci sai dai kawai su dogara da ayyanannen abinda ya bayyana ba tare da tattaro alamomi dabam daban da za su dogara a kai ba sai dai kawai su dogara a kan maganganun wasu daga cikin masana lugga ba tare da bincike game da marubucin da kuma tafarkinsa ba, wasu ma sam ba sa kasancewa suna da wata madogara game da ilimin sanin maruwaita ko kuma kwarewa game da littafan hadisai.
H) Fa’idantarwa ta fuskar Tunani
Sidi Sistani ba wai kawai Malamin fikihu ba ne a’a yana sane ma da ilimi na zamani kuma yana da masaniya game da ra’ayoyi masana fannoni dabam-daban yana kuma da matsayinsa na ilimi game da tattalin arziki da siyasa da fahimtar sha’anin tafi da shugabanci da halin zamantakewa da fahintar halin da zamani ke ciki yadda fatawarsa za ta zama alheri ga al’ummar Musulmi.

6. Matsayİnsa Na Marja’İ
Wasu Malaman garin Najaf sun bayyana cewa bayan rasuwar Ayatullahi Sidi Nasrullahi Al- Mustambat, wasu daga cikin manyan malamai sun shawarci Imam Khu’i da cewa ya ayyana wani da za a iya dogaro da shi wajen karewa da kiyaye makarantun addinin garin Najaf, zabin wannan zamanin shi ne Sidi Sistani saboda falalar iliminsa da kyawun halinsa da tafarkinsa da kuma tsayuwarsa yana ba da salla a mumbarin Sidi Khu’i (R.A.) da yin bayanai a makarantarsa da kuma rubuta karin bayani a kan Risalar shi Sidi Khu’i din (R.A.). Bayan rasuwar Imam Sidi Khu’i yana daga cikin mutane shidan da suka raka gawarsa kamar kuma yadda ya kasance shi ne ya sallace shi. Daga bisani ne kuma ya dauki matsayin shugabancin makarantun addini na garin Najaf yana aikewa da izinin tara Khumusi da rarraba hakkoki, yi masa takalidi kuma ya fara yaduwa musamman ma a Iraki, da kasashen Yankin Tekun Parisa da sauran gurare kamarsu Indiya da da sauransu musamman ma a tsakanin Malaman Makarantun addini da kuma masana ilimin Zamani da matasa saboda saninsa da suka yi da ci gaban tunani da ra’ayi. Shi yana daga cikin ’yan kalilan din da ke daga cikin manyan malaman fikihu da ake ambatawa daga cikin mafifita a ilimi tare da shaidar da dama daga malamai masana ta kan ilimi da kuma masu koyarwa a makarantun addini a garin Najaf mai alfarma da birnin Kum mai tsarki.

Saboda Muhimmancin littafan addinin musulunci ne Ma’assasar Imam Ali (a.s) da ke nan birnin Kum-Iran ta dauki nauyi fassara littafan zuwa harsuna dabam-daban da kuma bugawa da yadawa domin wadanda ba sa jin harshen larabci su fahinci abinda suka kunsa kana su ji irin dadin da ke cikin fahintar ma’anarsu; daga bisani kuma su amfane su wajen kyautata dabi’arsu da fatan za su zama hanyar fa’idantuwa da su a duniya da kuma lahira.

 

Mu’assasar Imam Ali

 

Comments

Loading...
no comments!

Related Posts