Logo

Kuma mun yi imani cewa Allah Ta'ala ba Ya barin abu mai kyau matukar ba gwamuwa ya yi da abu wanda shi ne mafi kyau ba kuma ba Ya aikata mummuna saboda Shi Allah Ta'ala Mai kudura ne a kan Ya aikata kyakkyawa Ya bar mummuna tare da kaddara saninSa game da kyawun kyakkyawa da kuma munin mummuna da wadatuwarSa ga barin kyakkyawan da kuma aikata mummunan. Babu wani kyakkyawan (aiki) da aikata shi zai cutar da Shi balantana Ya bukaci barin sa, babu kuma wani mugun aiki da yake bukatarSa ballantana Ya aikata shi kuma duk da haka Mai hikima ne babu makawa aikinSa Ya kasance ya dace da hikima kuma daidai gwargwadon tsari mafi kamala.31
____________
31- Mazhabar Ja'afariyya wato Shi'a Isna Ashariyya ta dauki adalci a matsayin jigo daga cikin ginshikan addini sai dai kuma alal hakika shi ba ginshiki ne guda shi kadai mai zaman kansa ba sai dai shi yana kunshe ne a cikin siffofin Allah Ta'ala kuma wajabcin samunsa ya lizimta tattara siffofin kyawu da kamala saboda haka shi dai adalci yana daga cikin al'amuran tauhidi ne. Sai dai kuma su Asha'irawa da suka saba wa Adaliyyawa, wato Mu'utazilawa da kuma `yan Ja'afariyya, Shi'a Isna Ashariyya sai suka musa abu mai kyau da kuma mummuna wadanda hankali ya tabbatar da su. Suka ce babu wani abu mai kyau sai wanda shari'a ta ce mai kyau ne, babu mummuna kuma a sai wanda shari'a ta ce mummuna ne kuma cewa idan da Allah zai dawwamar da mai biyayya a gidan wuta mai sabo kuma a gidan aljanna to wannan ba mummuna ba ne saboda yana jujjuya al'amura ne da ke karkashin mulkinSa kuma kamar yadda Alkur'ani ya ce: "Ba a tambayarSa a kan abinda ya aikata su kuwa ana tambayar su" Surar Anbiya'i aya ta 23. Su kuwa Adaliyyawa kuwa cewa suka yi: Mai yanke hukunci a wannan al'amari shi ne hankali shi kadai dinsa, babu abinda zai shigar da shari'a a cikinsa sai dai karin ta'akidi da kuma shiryarwa. Shi kuma hankali ya kebantu da hukunta kyawun wasu ayyuka da hukumta munin wasu kuma yana hukumta cewa danganta mummunan abu ga Allah abu ne da ba shi da kyau kuma ba zai yiwu ba Allah Ya aikata shi domin Shi Mai hikima ne azabtar da mai biyayya kuwa zalunci ne; zalunci kuwa mummunan abu ne kuma ba zai taba faruwa daga Allah Ta'ala ba.
Da haka ne suka tabbatar da siffar Adalci ga Allah suka kebance ta da ambato banda sauran siffofn don ishara ga sabani da Asha'ira. Su kuwa Adaliyawa ta hanyar ka'idar kyakkyawa da mummuna kamar yadda suke a hankali sun tabbatar da wasu ka'idoji daga ka'idojin ilimin sanin Allah: Kamar su Ka'idar Tausasawa, da kuma Wajabcin godiva ga wanda ya yi alheri da wata ni'ima, da kuma wajabcin bincike da

( 42 )

Idan har da zai aikata zalunci da kuma mummunan aiki -Shi Ya daukaka ga aikatawa- to da al'amarin hakan ba zai zamanto ya rabu da daya daga cikin surorin nan hudu:
1- Ya kasance Ya jahilci al'amarin bai san cewa mummuna ba ne.
2- Ko kuma Ya kasance Yana sane da shi amma kuma Ya zamanto Ya aikata shi ala tilas Ya gaza barin aikata shi.
3- Ko kuma Ya kasance Ya na sane da shi ba a kuma tilasta Shi Ya aikata ba bai kuma gaza kin bari ba amma Ya zamanto Yana bukatar aikatawa.
4- Ko kuma Ya kasance Yana sane da shi, ba mai aikata shi ala tilas ba, ba kuma mai bukata Ya zama Ya takaita ke nan da aikata shi a bisa sha'awa da wasa da bata lokaci.
Dukan wadannan surori kuwa sun koru ga Allah Ta'ala, Kuma tabbatar da nakasa gare Shi alhali Shi kuwa zallan kamala ne saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa Shi tsarkakakke ne daga zalunci da kuma aikata abinda yake mummuna.
Sai dai kuma wani bangare daga cikin musulmi sun halatta wa Allah Ta'ala aikata mummuna,32 sunayenSa sun Tsarkaka, suka halatta cewa zai iya hukunta musu biyayya, Ya kuma shigar da masu
____________
nazari a mu'ujiza, kuma a kan wadannan ka'idojin suka gina al'amari tilasta wa da kuma `yancin zabi da ke daga cikin mafi wahalar matsaloli.
Domin karin bayani a duba: Aslus Shi'a da kuma Matarihun Nazar na Shaikh Turaihi, Fasali na 4 shafi na 164.
32- Da dai sauran wadannan da Asha'irawa suka tafi a kai na daga maganganunsu na cewa Allah Ta'ala Ya aikata mummuna da maimaitawarSa na nau'o'in zalunci da shirka da dagawa da ketare haddi da kiyayya da yarda da su ya kuma so su -Allah Ta'ala Ya daukako ga haka, Tsarki ya tabbata gare Shi-, domin kara samun filla-fillan wadannan munanan ra'ayoyi'a duba littafi Nahjul Hak na Allama Hilli shafi na 85, da kuma sharhin Aka'ida da kuma Hashiyar na kistal, shafi na 109-113, da Milal wan Nahal Juzu'i 1 shafi na 85, 91 da kuma Al- Faslu na Ibin Hazm Juzu'i na 3 shafi na 66 da 69 da kuma Sharhit Tajrid na Kurshaji shafi na 373.

( 43 )

sabo aljanna kai hatta katirai ma, kuma suka halatta cewa Yana iya kallafa wa bayinSa abinda Ya fi karfinsu da abinda ba za su iya aikatawa ba amma kuma duk da haka Ya azabtar da su idan har suka bari ba su aikata shi ba. Har ila yau kuma sun halatta zalunci na iya faruwa daga gare Shi da tabewa, da karya da yaudara, kuma Ya aikata aiki ba tare da wata hikimaba, ba da manufa ba, ba da amfani ba, ba da fa'ida ba da hujjar cewa "Ba a tambayar sa a kan abinda yake aikatawa su kuwa ana tambayar su." Surar Anbiya: 23.
Da yawa daga cikin irin wadannan da suka suranta Shi a kan wannan akida tasu batacciya da cewa Shi, Azzalumi ne, mai Ja'irci, mai wauta ne, mai wasa ne, mai karya ne, mai yaudara ne, Yana aikata mummuna, Yana kuma barin kyakkyawa, Allah Ya daukaka ga aikata wadannan abubuwa, daukaka mai girma, wannan shi ne kafirci tsantsansa. Kuma Allah Ta'ala Ya ce: "Kuma Allah ba Ya nufin Zalunci ga bayi." Surar Mumin aya ta 23. "Kuma Allah ba Ya son barna." Surar Bakara: 31 "Kuma ba mu halitta sammai da kasa da abinda ke tsakaninsu muna Masu wasa ba." Surar Dukhan: 205. "Kuma ban halitta Aljannu da Mutane ba face don su bauta Mini." Surar Zariyat: 56.
( 44 )

9- Imaninmu Game da Wajabta Aiki.

Mun yi imani cewa Allah Ta'ala ba Ya kallafa wa bayinSa aiki sai bayan Ya tabbatar musu hujja a kansu33 kuma ba Ya kallafa musu sai
____________
33- Lalle ne a san cewa abinda ake nufi da kallafa aiki shine cewa va kallafa aiki ya bukaci wanda ya kallafawa din da ya aikata wani abu mai wahala mai tsanani. Wato ke nan abin dubawa da komawa gare shi a nan shi ne bukata saboda yadda ya zo a cikin fassara ko bayyana ma'ana da kuma fassarar kallafa aiki da cewa shi ne bukatar aiki mai tsanani da wahala daga wanda aka kallafawa. Kazalika Sayyid Sharif Murtadha Alamul Huda ya biyar da magana yana mai gyara batun da cewa: Kallafa aiki ba ya inganta sai bayan kamalar hankali da tabbatar da dalilai:
"Kuma Shi Allah Ta'ala mafi kammala hankula kuma ya kuma cika sauran sharuda don babu makawa Ya ba da taklifi wannan yana ishara da cewa takalifi ba shi ne sanarwa ba." Malamanmu sun yi bayanai masu yawa game da kallafa aiki tare da ambata fuskoki dabam-daban na abinda ake nufi da takalifi da kuma alakarsa da shi mukallafi wanda aka kallafawa aikin da kuma aikin da aka kallafa masa da siffofi shi wanda aka kallafa wa aikin da kuma manufar shi kansa aikin da kuma yadda za a yi a aiwatar da shi da kuma irin ayyukan da za a yi ya zama an aiwatar da wannan takalifin, da wanda ya kallafa masa wannan aikin, da kuma abubuwan da ya kebanta da su domin ya zamanto ya kyautata aiki ko kuma wadanne abubuwa ne wajiban wannan aikin. Sananne ne cewa wannan bangare yana daga cikin bayanan Irada wadanda suka cancanci himmatuwa ta musamman daga bangaren malaman Akida tare kuma da kebe masa sashe na musamman a sakamakon babban sabanin da ke akwai a kansa a tsakanin malamai da shugabannin mazhaba game da nufin Allah da aka ambata a ayoyin Alkur'ani da kuma alakarsa da al'amuran da Allah bai yarda da su ba da kuma tawilinsu da fuskokin da ba za su rasa matsa wa kai ba ,mafi muhimmanci daga cikinsu kamar aya ta 148 daga surar An'am da ke cewa: "Wadanda suka yi shirka za su ce idan da Allah Ya so da ba mu yi shirka ba, kuma da iyayenmu (ma ba su yi ba) kuma da ba muharamta daga wani abu ba, haka nan wadanda suka kasance kafin su suka yi karya har suka dandani azabarmu, ka ce shin kuna da wani abu na daga ilimi da za ku fito mana da shi? Babu abinda kuke bi face

( 45 )

abinda za su iya aikata shi kuma suke da ikon aikata shi kuma suka san shi domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, wanda ba zai iya
____________
zato ku ba kome ba ne illa kuna dirkaniya kawai." Da kuma aya ta 20 daga surar Zukhruf: "Kuma suka ce idan da mai Rahama Ya so da ba mu bauta musu ba, ba su da wanidalili game da wannan ba sa kome sai dai dirkaniya."
Da dai ayoyi da dama da ake wahimtar cewa su shafi Iradar mahalicci ne game da abinda halittu ke aikatawa mummuna. Allah Ta'ala Ya daukaka ga yin haka, daukaka mai girma. Daga nan na Shaikh Muzaffar (R.A.) ya ware sashe guda shi kadai domin ya rubuta abinda ya dace a cikinsa game da abinda ya kebantu da matsayin Shi'a Imamiya. Domin Mazhabar Ahlul Bait (A.S.) tana da matsayinta bayyananne wanda ke yin ta'akidi a kan tsarkake Ubangiji da kuma raba Shi da duk wani mummunan abu ko kuma mai kama da mummuna tare da matukar kore cewa Allah Ta'ala ne Ya nufi a yi shirka ko zalunci ko alfasha, ballantana ma aikata shi, ko kuma halatta aikata shi ko umarni da shi domin dukkan wannan zai kai ga saba wa hikimarSa da adalcinSa da falalarSa.
Abinda Shaikh Mufid (R.A.) ya ambata shi ne sakamako ko kuma amfanin wannan magana inda yake cewa: Allah Ta'ala ba Ya nufin a aikata sai kyakkyawa daga ayyuka, kuma ba Ya so sai kyakkyawa daga ayyuka kuma ba Ya son munanan ayyuka, ba Ya nufa a aikata alfasha, Allah Ya daukaka daukaka mai girma daga abinda mabarnata suke fada Allah yana cewa: "Kuma Allah ba Ya nufin Zalunci ga bayi." Surar Mumin: 31
"Allah Ya na nufin sauki gare ku ba Ya nufin tsanani gare ku." Surar Bakara: 185
"Allah Yana nufin Ya yi muku bayani kuma Ya shiryar da ku tafarkin wadanda suka gabace ku." Surar Nisa'i: 26.
"Allah Yana nufin Ya yafe ku wadanda suke bin sha'auce-sha'auce kuwa suna nufin ku fandare fandarewa mai girma." Surar Nisa'i: 27.
Allah Ta'ala Ya ce: "Allah Yana nufin Ya saukaka muku kuma shi mutum an halitta shi rarrauna ne." Surar Nisa'i 28.
Allah Ta'ala Ya bayyana cewa ba Ya nufin tsanani ga bayinSa Yana nufin sauki ne gare su, kuma cewa Yana nufin bayani gare su, ba Ya nufin bata gare su, kuma Yana nufin saukakawa gare su ba ya nufin nauyayawa. Kuma idan har da Allah Ya kasance Shi ne mai nufar su da sabo to ai da wannan ya sabawa nufinSa na yin bayani gare su da saukakewa gare su. Littafin Allah shaida ne a kan sabanin abinda batattu masu kaga karya ga Allah suka tafi a kai. Allah Ya daukaka daga abinda azzalumai, suke fada daukaka mai girma.
A duba littafin Azzakhira na Sayyid Murtadha Mufid Juzu'i na 5 shafi na 48-51.

( 46 )

ba, da kuma jahilin wanda ilimi bai isa zuwa gare shi ba, ba wai ya ki neman ilimin da ganganci ba.
Amma shi kuwa Jahili wanda ya ki neman sani da gangan alhali yana da damar samun ilimin hukunce-hukunce da ayyukan ibada to shi ne mai amsa tambaya a gurin Allah Ta'ala, kuma shi za a yiwa ukuba a kan sakacinsa domin wajibi ne a kan kowane mutum ya koyi abinda yake bukata na daga hukunce-hukuncen shari'a.34
Kuma mun yi imani cewa: Shi Allah Ta'ala babu makawa Ya kallafa wa bayinsa ayyuka Ya kuma sanya musu shari'o'i abinda na amfani da kuma alheri gare su a cikinta domin Ya sanya su a kan hanyoyin alheri da rabo ta dindindin, sa'an nan kuma Ya shirye su zuwa ga abinda Yake shi ne maslaha kuma Ya gargade su game da abinda yake akwai fasadi da barna a cikinsa da kuma cutarwa gare su
____________
34- Abinda ke nuna haka shi ne fadin Allah Ta'ala cewa: "To ku tambayi ma'abuta sani idan har kun kasance ba ku sani ba." Surar Nahli: 31.
Da kuma fadin Allah Ta'ala da ke cewa: "Don me wata jama'a daga cikinku ba za ta fita domin su nemi ilimi don su fahinci addini kuma su yi gargadi ga mutanensu idan sun koma zuwa gare su ko sa yi taka tsatsan ba." Surar Tauba aya ta 122.
Kazalika maganar Imam Sadik (A.S.) na yin ishara da haka yayin da aka tambaye shi dangane da maganar Allah Ta'ala da cewa "ka ce: To Allah na da cikakkiyar hujja a kanku" Sai Imam (A.S.) ya ce: "Ranar Alkiyama Allah zai ce wa bawa, bawaNa shin ka kasance masani? Idan ya ce "E" sai Ya ce masa: Shin ka yi aiki da abinda ka sani. Idan kuwa ya ce: Nina kasance Jahili sai ya ce masa: Ashe ba ka koya ba har ka yi aiki: Sai yaja da shi: To wannan ita ce cikakkiyar hujja." Haka ya zo a littafi Amali Shaikh Tusi shafi na 9 Juzu'i na 10/10. Kuma mai Biharul Anwar ya kawo daga gare shi Juzu'i na 2 shafi na 29 hadisi na 10. Da kuma hadisin da aka kawo daga Imam Sadik (A.S.) cewa: "Ku lizimci neman ilimi addinin Allah kada ku zamanto jahilan kauye, domin wanda bai nemi ilimi addinin Allah ba, Allah ba zai dube shi ba ranar Alkiyama kuma ba zai tsarkake masa aiki ba." Alkafi Juzu'i na 1 shafi 24 hadisi na 7.
Kamar kuma yadda ya zo a "Risalolin" hukunce-hukuncen ibada da ake aiki da su cewa: Wajibi ne akan mukallafi wato balagi ya nemi ilimin al'amuran shakku da na mantuwa wadanda zai yiwa su taso masa, domin kada ya auka cikin saba wa abinda aka kallafa masa idan har bai koya ba. A duba Risalar Sayyid Sistani mai suna Minhajis Salihin Babin Ibada shafi na 13 matsala ta 19.

( 47 )

da kuma mummunan karshe gare su. Koda kuwa Ya san cewa su ba za su bi Shi ba, domin wannan tausasawa ne da kuma rahama ga bayinSa don kasancewarsu sun jahilci mafi yawancin amfanin kansu da hanyoyinsu a nan duniya da kuma lahira. Sun jahilci da yawan abubuwan da za su jawo musu cuta da hasara, Shi kuwa Allah Ta'ala Shi ne Mai Rahama mai Jin kai a ainihin zatinSa, Shi kamala ne tsantsa wanda kuma shi ne ainihin zatinSa kuma har abada bai rabu daga gare shi.
Wannan tausasawa kuwa ba za ta gushe ba, don bayinsa sun kasance sun bijire sun ki bin sa, sun ki kayyaduwa da umarce-umarcensa kuma sun ki hanuwa da hane-hanenSa.


( 48 )

10- Imaninmu Game da Hukuncin Allah da
Kuma Kaddara

Jama'ar Al- Mujabbira35 sun tafi a kan cewa Allah' Ta'ala shi ne mai aikata ayyukan halittu don haka sai Ya zamanto ke nan Ya tilasta mutane a kan aikata sabo duk da haka kuma Ya yi musu azaba.
Sa'an nan kuma Ya tilasta su a kan yin da'a duk da haka kuma Ya ba su lada a kai. Domin su suna cewa: Lalle ayyukansu alal hakika ayyukanSa ne ana dai dangata ayyukan gare su ne kawai don sassautawa domin su ne muhallin ayyukan, asalin wannan kuwa shi ne
____________
35- Daga cikinsu akwai Al- Asha'ira wadanda suke inkarin musabbabi inda suka kayyade musabbabin da cewa Allah Ta'ala ne kawai, suka ce, alal misali wuta ba za ta kona kome ba sai dai kawai al'adar Allah Ta'ala ce ta gudana a kan cewa duk yayin da tutafi suka shafe ta za su kone ba wai don wuta ita ce mai wani shiga cikin al'amarin konawar ba. Don hakan ne suka tafi a kan cewa ayyukan mutane Allah ne Ya halitta su ba tare da wani hannun su bayin a kai ba, wato shi bawa bashi da wani tasiri a kan aikata aiki. A duba littafin Bidayatut Ma'ariful Ilahiyya Juzu'i na 1 shafi na 159 da shafukan da ke biye
Ba boyayye ba ne ga duk wanda ya bibiyi littafan Mazhabar Ja'fariyya, Shia Imamiya, cewa suna soke akidar Jabru da ke cewa duk abinda mutun ya yi Ubangiji ne Ya sa shi sun yi sabani da Asha'ira da suka yarda da hakan kamar kuma yadda har ila yau su 'yan Mazhabar Ja'fariyya ba su yarda da sallama kome gar bawa ba shi ne mai iko a kan kome da kome sabanin Mu'tazilawa. An ruwaito daga Imam Abi Hasan Aliyu Bin Muhammad Al-Hadi (A.S.) cewa an tambaye shi game da ayyukan mutane inda aka ce masa: Shin Allah ne Ya halitta su? Sai Ya ce: "Ai idan da Shi ne ya halitta su to da bai kore su daga gare Shi ba ai Allah Ta'ala Ya ce lalle Allah ba Shi ba mushirikai haka nan ma ManzonSa." Surar Tauba aya ta 3. Babu abinda yake nufi da rabuwar ba wai daga ainihin halittarsu ba na abin nufi shi ne shirkarsu da munanansu."

( 49 )

kasancewarsu sun yi inkarin musabbabai na dabi'a a tsakanin abubuwa domin sun yi tsammani cewa hakan shi ne ma'anar kasancewar Allah Ta'ala mahalicci da ba Shi da abokin tarayya kuma Shi ne mai sabbabawa na ainihi ba waninSa ba.
Duk wanda yake fadin irin wannan ra'ayi kuwa to lalle ya danganta zalunci ga Allah, Shi kuwa Ya daukaka ga haka.
Wasu jama'a kuma wato- Mufawwidha36 sun yi imanin cewa Allah Ya sallama ayyuka ne ga halittu, Yajanye kudurarSa da hukuncinSa da kuma kaddarawarSa daga gare su, wato ma'ana danganta ayyuka gare shi Ta'ala yana nufin dangata nakasa gare shi, kuma samammun halittu suna da nasu musabbaban na musamman koda yake dai dukansu suna komawa ne ga musabbabi guda daya na farko wanda shi ne Allah Ta'ala.
Duk wanda yake fadin wadannan irin maganganu to lalle Ya fitar da Allah daga mulkinSa Ya kuma hadar da Shi a shirka da halittunSa.
Kuma mun yi Imani muna masu biyayya ga abinda Ya zo daga Imamanmu tsarkakakku da ke cewa al'amari ne tsakanin al'amura biyu kuma tafarki matsakaici a tsakanin maganganun biyu, wanda irin wadancan ma'abuta tsaurin kan suka gaza fahimtarsa wasu suka zurfafa wasu kuma suka yi kwauro, babu wani daga cikin masana ilimi da ma'abuta falsafa da ya fahince shi sai bayan karnoni.37
____________
36- Mufawwadha su ne wadanda suka kare tilasta mutum a kan ayyuka, yawancinsu Mu'utazilawa ne, suka ce ayyuka dai an sallama su gare mu ne babu abinda ke sanya Irada da Izinin Allah Ta'ala a cikin ayyuka. Abinda ya jawo wannan mummunan ra'ayi shi ne gudun danganta sabo da kafirci ga Allah Ta'ala. Al-Tafwidh shi ne kore taka tsantsan a ayyuka ga bayin Allah da kuma halitta musu aikata abinda suka so na daga ayyukan. Wannan magana ce irinta Zindikai da ma'abuta halastarwa.
37- Shaikh Mufid ya fadi a cikin littafin Tashihul I'itikad cewa: "Hanya matsakaiciya a tsakanin wadannan maganganun biyu wato Aljabru - tilasta aiki- da kuma Tafwidh - sallama ayyuka-. Ma'ana cewa Allah Ta'ala Ya kaddara wa bayinSa ayyuka da Ya sa su aikata su Ya kuma sanya musu iyakoki a kan haka, Ya kuma shata musu zane-zanen, kuma Ya hane su aikata munanan ta hanyar gargadi da tsoratarwa da narko da azabtarwa. Kuma bai kasance Yana ma tilasta su ba ta hanyar barinsu da

( 50 )

Ba abin mamaki ba ne ga wanda ba shi da masaniya game da hikimar Imamai (A.S.) dangane da al'amari tsakanin al'amura biyu ba, da kuma hanya matsakaici ba a maganganun biyu Ya ce wannan batu ne daga cikin al'amuran da masana falsafa a Yammacin Turai na baya bayan nan suka gano alhali kuwa Imamai sun riga su tun kafin karni goma da suka wuce.
Imam Sadik (A.S.) yayin da yake bayanin hanyar nan matsakaiciya yana cewa: "Babu Jabru, (tilastawa), kuma babu sallamawa ayyuka baki daya sai dai al'amari ne tsakanin al'amuran guda biyu.38
Wannan ma'ana girmanta na da yawa manufarta kuma na da zurfi. Abin nufi a takaice shi ne cewa: Lalle ayyukanmu a bangare guda ayyuka namu alal hakika kuma mu ne musabbabansu na dabi'a kuma suna karkashin ikonmu da iyawarmu. A daya bangaren kuma su ayyukan kudurar Allah ne kuma suna cikin karkashin ikonSa. Domin Shi ne Mai ba da samuwa Mai samar da ita. Bai tilasta mu a kan ayyuka ba ballantana Ya zamanto Ya zalunce mu a kan yi mana ukuba idan har muka saba. Saboda muna da iko da kuma zabi a kan abinda muke aikatawa. Kuma bai sallama mana samar da ayyukanmu ba ballantana Ya zamanto Ya fitar da su daga karkashin ikonSa ba, Shi dai Shi ne Mai halittawa Shi ne kuma mai hukuntawa, Shi ne kuma mai umarni, Shi kuma Mai iko ne a kan kome, kuma a kewaye Yake da bayinSa.39
____________
ikon aikatawa, kuma bai sallama musu ayyuka ba saboda hana su aikata mafi yawa daga cikin su da kuma sanya musu iyaka a kansu, Ya umarce su da masu kyau Ya hana su munana, wannan shi ne bambanci tsakanin tilastawa da kuma sallamawa, Musanafat Shaikhul Mufid. Juzu'i 15.
38- Al-Kafi Juzu'i na 1 shafi na 160 hadisi na 13 da kuma Al-Ihtijaj Juzu'i na 2 shafi 490, da Littafin Al Tauhid Shafi na 362, da Al- Itikadat na Shaikh Saduk: 10 da Tashihul I'itikad Musanafat na Shaikh Mufid Juzu'i na 5 shafi na 46.
39- An tambayi Abul Hasan Musa bin Ja'afar (A.S.) dangane da ayyukan bayin Allah, daga wa suke? Sai ya ce: "Ayyukan bayin Allah ba sa wuce dayan uku: Ko dai su kasance daga Allah da kebe, ko kuma su kasance daga gare Shi ta fuskar Yana da hannu a ciki ko kuma su zamanto daga bawa zalla. Idan da sun kasance daga Allah ne zalla to da Shi ne Ya fi cancantar yabo a kan Kyawawansu, da zargi kuma a kan

( 51 )

Ko ta halin kaka dai abinda muka yi imani da shi game da hukuncin Allah da kuma kaddara shi ne cewa sirri ne daga asirran Allah Ta'ala duk wanda ya iya ya fahince Shi yadda ya dace ba tare kwauro ko zurfafawa ba to shi kenan, idan kuwa ba haka ba to ba wajibi ba ne ya kallafa wa kansa cewa sai ya fahimce Shi daidai wa daida, domin kada ya je ya bata akidarsa, kuma ta baci saboda wannan yana daga cikin al'amura masu wahala, har ma sun fi binciken al'amuran falsafa zurfi. Babu mai iya gane su sai `yan kalilan daga cikin mutane wannan shine abinda ya sa da yawa daga cikin ma'abuta ilimin akida suka tabe.40
Don haka kallafa shi ma ga bayi kallafa abu ne da ya fi karfin mutum wanda yake daidai da sauran mutane. Ya wadatar mutum ya zamanto ya yi Imani da shi a dunkule kawai yana mai biyayya ga maganar Imamai tsarkaka, amincin Allah ya tabbata gare su, cewa shi wani al'amari ne tsakanin al'amura guda biyn, babu tilastawa babu kuma sallamawa a cikinsa.
Kuma shi baya daga cikin jigo daga cikin jiga jigan addini ballantana ya zama kudurcewa da shi wajibi ko ta halin kaka filla-flla daram.
____________
munanansu, yabo da zargi ba zai taba zama ya ta'allaka ga kowa ba. Idan kuwa da daga Allah ne da kuma bawa to da yabo da suka ya zamanto nasa tare idan wadannan biyun sun tabbata ba daidai ba to ya tabbata ke nan ayyuka daga halittu ne, idan Allah ya yi musu ukuba a kan laifinsu da suka aikata to hakkkinsa ne ya yi haka. Idan kuwa ya yafe su shi ma'abucin takawa ne da gafara." Tashihul I'itikad Shaikh Mufid Juzu'i na 5 shafi na 44.
40- A cikin littafin laccocin Falsafa Shaikh Muzaffar na da wannan ra'ayin mai zurfi da ke cewa:
"Kowane daya daga cikin Mujabbira wato masu ra'ayin tilasta ayyuka ga bayin Allah, da kuma Mufawwidha, masu ra'ayin sallama ayyuka bai daya ga bayi, sun dubi kwuibi daya ne kawai sun mance da dayan sai dai kuma wajibi ne mutum ya zamanto mai ido biyu ba mai ido daya ba, duk wanda ya duba da kwuibi daya to ya zama mai ido daya yana duban bayar da samuwa ta bangare har ya suranta cewa ana tilasta mutane a kan ayyuka, sa'an kuma idan ya duba kwuibi dayan da mutane ke aikata ayyukansu da zabinsu sai ya suranto cewa an sallama musu ne. Amma kuma idan da kulawar Allah za ta katse mini koda na dan lokaci ne to da na gushe kuma da ayyuka na ma sun gushe ni ina linkaya ne a karkashin mulkinSa.

( 52 )

11- Imaninmu Game da Bada'.

"Bada" ga mutum: shi ne wani sabon ra'ayi ya bayyana gare shi wanda a da can bai kasance yana da wannan ra'ayin ba, wato ya canja himmarsa da ya yi a kan wani aiki da ya kasance yana nufin aikata shi, wannan kuma saboda jahilcine game da amfani da kuma nadama a kan abinda ya riga ya gabata daga gare shi.
"Bada" da wannan ma'anar ta koru ga Allah Ta'ala. Domin kuwa yana daga jahilci ne da nakasa wannan kuwa ya koru ga Allah Ta'ala Shi'a Imamiyya kuma ba su yarda da shi ba.
Imam Sadik (Alaihis Salam) Ya ce:
"Wanda Ya yi da'awar cewa Bada ta auku ga Allah Ta'ala game da wani abu. Bada irin na nadama ta a gurinmu wannan Kafirine a game da Allah mai girma.41 Har ila yau kuma Ya ce: "Wanda ya raya cewa wani abu ya yi Bada ga Allah wanda da Ya kasance bai san shi ba jiya to ni ba ni ba shi".42
Sai dai kuma akwai wasu hadisai da aka ruwaito daga Imamanmu wadanda suke kamar nuni da ma'anar "Bada" yadda ta gabata. Kamar yadda ya zo daga Imam Sadik (Alaihis Salam) cewa: "Bada bai taba yiwuwa ga Allah ba kamar yadda ya yiwu gare shi ba a kan Isma'ila dana."43 Don haka ne wadansu marubuta daga cikin bangarorin
____________
41- Kamaluddin shafi na 69.
42- Kamaliddin shafi na 70.
43- Al- Tauhid shafi na 336 Hadisi na 10, da Kamaluddin shafi na 69 da kuma Tashihul I'itikada na Shaikh Mufid Juzu'i na 5 shafi na 66. Shaikh Mufid ya kara bayanin hadisin da cewa: "Abinda yake nufi, (Alaihis Salam), shi ne abinda ya

( 53 )

musulmi suka dangata Bada' ga Shi'a Imamiyya don yin suka ga mazhaba da tafarkin Ahlul Bait suka sanya shi ya zama abin kyama ga Shi'a.
Sahihin al'amari a nan shi ne mu fadi kamar yadda ya fada a Alkur'ani "Allah Yana shafe abinda Ya so kana Yana tabbarwa asalin littafi kuma gare Shi Yake." Surar Ra'ad: aya ta 39.
Abin nufi shi ne cewa Allah Ta'ala na iya bayyana wai abu a bisa harshen Annabinsa ko waliyinSa ko kuma a zahiri wata maslaha ta sa bayyanawar sa'an nan daga baya kuma Ya shafe shi Ya zama ba abinda ya bayyana da farko ba, kamar yadda ya faru a kissar Annabi Isma'il (A.S.) yayin da mahaifinsa Annabi Ibrahim (A.S.) ya ga yana yanka shi.44
Wato kenan ma'anar maganar Imam (Alaihis Salam) sai ta zama kenan cewa: Lalle babu wani abu da ya bayyana ga Allah Ta'ala na daga al'amari a kan wani abu kamar yadda ya bayyana gare shi a kan Isma'ila dansa domin (Allah) Ya dauke shi (Isma'ila) kafin shi (Imam Sadik (A.S.) domin mutane su san, (cewa) shi (Isma'ila) ba Imami ba ne, a zahiri ya riga ya bayyana cewa shi ne Imami bayansa saboda shi ne babban dansa.45
____________
bayyana daga Allah Ta'ala na kore kisa gare shi, masa sai ya tausasa gare shi wajen kore shi daga gare shi.
Labarin haka ya zo ga Sadik (Alaihis Salam), an ruwaito daga gare shi cewa har sau biyu sai na roki Allah don ya kore masa kuma ya kore". Abu na iya zama rubutacce da sharadi sai halin al'amarin ya canja.
44- Allah Ta'ala Ya ce: "Kuma yayin da ya isa aiki tare da shi ya ce: Ya karamin dana ni na gani a mafarki lalle in yanka ka. To ka duba me ka gani. Sai ya ce: "Ya Babana ka aikata abinda aka umarce ka, in Allah Ya so za ka same ni daga masu hakuri. To yayin da suka amince kuma ya kayar da shi a gefen goshinsa. Kuma Muka kiraye shi cewa ya Ibrahim.,Hakika ka gaskata mafarki kuma tamkar haka ne Muke sakamtawa masu kyautatawa. Lalle wannan tabbatacce shi ne babban bala'i bayyananne. Kuma sai Muka musanya shi da abin yanka mai girma." Surar Saffat: 102-107.
45- Akwai wasu jama'a daga cikin Shi'a - duk da abinda Imamus Sadik (Alaihis Salam) da abubuwan da ya fada dangane da rasuwar dansa da kuma shirya jana'izarsa

( 54 )

Abu da yake da "Bada" a ma'ana kuma shi ne shafe hukunce-hukuncen shari'o'in da suka gabata da shari'ar Annabinmu Muhammadu sallallahu Alaihi wa ahlihi hatta ma shafe wasu daga cikin hukunce-hukuncen shi Annabin namu sallallahu Alaihi wa ahlihi.46
____________
da kai shi kabari-suna cewa Isma'il shi ne Imami bayan mahaifinsa Imam Sadik (Alaihis Salam). Wadannan su ne ake kira da `Yan Isma'iliyya, su dabam suke da Shi'a Imamiyya da fadinsu cewa "Imamanci bayan Imam Sadik (Alaihis Salam) ya koma ga babban dansa ne Isma'il kuma suna raya cewa Imam Sadik (Alaihis Salam) shi ne ya ba da nassin haka game da shi tun yana da rai. Kuma sun yi sabani game da Isma'ila. Wasu daga cikinsu suka ce ya rasu tun zamanin Mahaifinsa Imam Sadik - wannan shi ne ya tabbata a tarihi kamar yadda marubucin littatin ke ishara da shi a nan. Su wadannan su ne suke cewa Imamanci ya ci gaba a zuriyar shi Isma'ila na farkonsu kuwa shi ne Muhammad bin Isma'ilu, wasu daga cikinsu kuma suke cewa shi Isma'la bai mutu ba mahaifinsa ya bayyana rasuwarsa don takiyya, gudun kada Abbasiyawa su kashe shi har ma ya sa gwamnan Mansur a Madina Muhammad bin Sulaiman ya halacci mutuwarsa da shirya jana'izarsa da kuma kai shi kabari. Wadanda suka tsaya a kan shi Isma'ila daga cikinsu, ba su ketare shi ba, su ake kira "yan wakafiyya" a zahiri suna kidaya Imamansu bakwai ne daga kan Imam Aliyu bin Abi Talib (Alaihis Salam) zuwa kan shi Isma'ila da suke ce Imami ne. Sashensu kuwa da suke ce dan Isma'il Muhammad shi ma Imami ne suna da Imami goma sha hudu, bakwai na zahiri bakwai kuma na boye, na zahirin sun fara daga kan Imam Aliyu bin Abi Talib (Alaihis Salam) zuwa kan shi Isma'il bakwai boyayyu kuwa sun fara ne daga kan Muhammad bin Isma'il sai dansa Ja'afar As-Sadik, sai dansa Muhammadul Habib, sai kuma Abdullahil Mahdi wanda ya bayyana a Arewacin Afirka daga cikin 'ya'yan Fatima har ya kafa hukumar Fatimiyya.
A duba littafin: Firakus Shi'a shafi na 67, da kuma Al-Fusulul Mukhtara minal Uyuni wal mahasin shafi na 308, da kuma Asshi'atu Bainal A'sha'ira wal Mu'utazila shafi na 78, da Tarikhul Mazahibi Islamiyya shafi na 54, da al-Milal wan Nihal na Shahrastani Juzu'i na 1 shafi na 149, da kuma al-Farku Bainal Firak shafi na 62.
46- As- Shaikh Muhammadul Husain Kashiful Gita ya yi bayani game da haka yana cewa: "Shi Bada a duniyar halitta tamkar shafe hukunci da maye gurbinsa da wani ne a duniyar tsara shari'a. Kamar yadda shafe hukunci da maye gurbinsa akwai wasu fa'adoji da asirrai wadanda wusunsa sun fito sarari wadansu na boye kazalika a wajen boyewa da kuma bayyanawa a duniyar halitta. A bisa asasin cewa wani bangare na Bada (Bayyanawa) saboda sanar wa zukatan, ke da sadarwa da madaukakin matsayi ne, wasu abubuwa sa'an nan a kange musu sharudansu ko kuma


( 55 )

12- Imaninmu Game da Hukunce-Hukuncen Addini

Mun yi imani cewa Allah Ta'ala Ya sanya hukunce-hukunce -wajibai da haram-haram da sauransu daidai da maslaha da alheri ga bayinSa a cikin ainihin su ayyukan, abinda maslaharsa ta zama babu makawa sai da ita Ya sanya shi wajibi wanda kuma cutarwar da ke tare da shi ta kai matuka to Ya haramta shi wanda kuwa maslaharsa ta zama da kadan ta rinjayi cutarwarsa to Ya sanya mana shi mustahabi.
Kazalika ma sauran hukunce-hukuncen, wannan kuwa yana daga adalcinsa da kuma tausasawarSa ga bayinSa.
Kuma lalle babu makawa Ya zamanto Yana da hukunci a kan kowani al'amari47, babu wani abu daga cikin abubuwa da zai zamanto
____________
shamakinsu. Alal Misali an nuna wa Annabi Isa (A.S.) cewa wani ango zai mutu ranar da zai shiga dakin amarya amma ba a nuna masa cewa da sharadin rashin sadaka ba ne sai aka yi gamon katar mahaifiyarsa ta yi masa sadaka, shi kuma Annabi Isa (A.S.) ya riga ya sanar da cewa zai mutu a daren shiga dakin amarya sai ya zamanto bai mutu ba. Da aka tambaye shi game da haka sai ya ce: "Mai yiwuwa kun yi masa sadaka ne, sadaka kuwa na iya kare bala'i mummuna." Hakaza da makamantan wannan... Idan da ba don Bada' ba to da babu wata ma'ana ga sadaka da addu'a da ceto, da ma kukan Annabawa da Waliyai da tsananin tsoronsu da taka tsantsan dinsu ga Allah alhali ba su taba saba masa ba ko da gwargwadon kiftawar ido, tsoronsu kawai saboda saninsu ne game da shamakin nan taskantacce wanda babu wani da ya gan shi."
Littafin Aslus Shi'a wa Usuliha shafi na 314.
47- "Ba mu bar wani abu ba daga littafi" Surar An'am aya ta 38. Kuma ya zo a hadisi "Babu wani da mutane biyu ke da sabani a kansa face yana da asalinsa a cikin littafin Allah." Usulul Kafi Juzu'i na 1 shafi na 78 hadisi na 6. Har ila yau kuma ya

( 56 )

ba shi da hakikanin hukuncin Allah a kansa koda kuwa tafarkin saninsa a toshe yake gare mu.
Kuma har ila yau muna cewa lalle yana daga mummunan abu Ya zamanto Ya yi umarni da aikata abinda yake akwai cutarwa a cikinsa, ko kuma Ya hana abinda akwai maslaha a cikinsa.
Sai dai kuma wasu daga cikin bangarorin musulmi suna cewa: Mummunan abu shi ne kawai abinda Allah Ta'ala Ya hana, kyakkyawa kuwa shi ne abinda Ya kyautata kuma Ya yi umarnin a aikata, ba wai ainihin maslaha da cutarwar a ayyukan suke ba, kuma babu kyawu ko rashin kyawu a ainihin zatin.48 Wannan kuwa batu ne da ya saba wa abinda hankali ya wajabta.
Kazalika sun halatta cewa Allah na iya aikata mummuna Ya yi umarni da abu wanda akwai cutarwa a cikinsa, kuma Ya hana abinda yake akwai maslaha a cikinsa. Ya riga Ya gabata cewa wannan irin magana akwai rashin girmamawa a cikinta kwarai. Saboda wannan magana na hukunta danganta jahilci da gazawa ga Allah, Allah Ta'ala Ya daukaka, daukaka mai girma ga barin irin wadannan al'amura.
A takaice dai: Abinda yake sahihi a akida shi ne mu ce: Shi Allah Ta'ala ba Shi da wata maslaha ko fa'ida a kallafa wajibai da kuma haramta haramtattu sai maslahar da fa'idojin duka suna komawa ne gare mu a dukan ayyuka. Kuma babu wata ma'ana wajen a kore maslaha ko barna game da ayyukan da aka yi umarni ko aka hana aikatawa, Allah ba Ya umarni don wasa ba Ya hani haka banza shi kuma mawadaci ne ga barin bukatar bayinSa.
____________
zo cewa: "Babu wani abu da ke faruwa face Allah yana da hukunci a kansa." Biharul Anwar Juzu'i na 93 shafi na 91-93.
48- Asha'ira na cewa: Kyakkyawa da mummuna al'amura biyu ne da suke daga shari'a kuma hankali ba ya hukunta kyawun daya daga cikinsu ko kuma muninsa, sai dai mai hukunta haka ita ce shari'a kawai duk abinda ta ce mai kyau to shi ke nan shi ne mai kyau wanda kuwa ta munana to shi ne mummuna.
A duba littafin: Nahjul Hak shafi na 83 da Almilal wal Nihal juzu'i na 1 shafi na 89 da Sharhut Tajrid na Kaushaji: 375.


( 57 )

FASALI NA BIYU ANNABCI


  • Annabci
  • Annabci Tausasawa Ne.
  • Mu'ujizar Annabawa.
  • Ismar Annabawa.
  • Siffofin Annabawa
  • Annabawa da Littafansu.
  • Musulunci
  • Mai Shar'anta Musulunci
  • Alkur'ani Mai Girma
  • Tafarkin Tabbatar da Alkur'ani da Shari'un Magabata.


    ( 58 )


    ( 59 )

    13- Imaninmu Game da Annabci

    Mun yi imani cewa Annabci aiki ne na Allah Ta'ala, wakilci ne na Ubangiji, wanda shi Allah Ta'ala Yake daukar wadanda Ya zaba daga cikin bayinSa salihai da waliyanSa kamilai a `yan Adamtakarsu, Ya aika su zuwa ga sauran mutane domin shiryar da su ga abinda yake da amfani da maslaha gare su a duniya da kuma lahira. Tare kuma da nufin tsabtace su da tsarkake su daga daudar miyagun dabi'u da munanan al'adu kuma da koya musu hikima da ilimi da bayyana musu hanyoyin Sa'ada da alheri domin `yan Adamtaka ta kai ga kamalarta da ta dace da ita domin ta daukaka ga daraja madaukakiya a gidajen duniya da na lahira
    Kuma mun yi imani cewai Lalle ka'idar tausasawa -wanda da sannu za mu yi bayanin ma'anarta nan gaba- ta sanya ya zama babu makawa Allah Ya aiko ManzanninSa domin su shiryar da dan Adam, da kuma isar da sokan gyara domin su zamanto wakilan Allah kuma halifofinSa.
    Kamar kuma yadda muka yi imani da cewa Allah Ta'ala bai dora wa mutane hakkin ayyana Annabi ba ko kuma kaddamar da shi ko zaben sa. Ba su da wani zabe a kan haka, sai dai al'amarin haka ga Allah yake domin "Shi ne Ya fi sanin inda zai sa sakonSa." Surar An'am ayata 124. Kuma ba su da wani hukunci a kan wanda Allah zai aiko shi a matsayin mai shiryarwa, mai albishir ko mai gargadi, kamar kuma


    ( 60 )

    yadda ba su da wani hukunci a kan abinda ya zo da shi na daga hakunce-hukunce da sunnoni da shari'a.49
    ____________
    49- Imam Aliyu Bin Abi Talib (a.s.) yayin da yake bayani ya siffanta fara halitta sama da kasa da halitta Annabi Adam (A.S.) da kuma ambata Annabawa da aiko su ya fada a hudubarsa cewa: "Kuma Subhanu Ya zabi Annabawa daga cikin `ya'yansa (Adam) Ya karbi alkawarinsu a kan wahayi da kuma amanarsu a kan isar da sako. Yayin da yawancin halittunSa suka canja suka jahilci hakkinSa, suka riki ababan bauta tare da Shi shedanu suka fitsare su daga saninSa, suka yanke su daga bautarSa. Sai Ya aiko musu da ManzanninSa, kuma Ya bibiyar musu da AnnabawanSa domin su sake shiryar su ga alkawarin halittarsu, su tunatar da su mantattun ni'imominSa kuma su kafa musu hujja da isar da sako, su farfado da abubuwan da hankali ya mance, su nuna musu ayoyin kudura, na daga rufin da ke dage a samansu, da shinfidar da ke sanye a karkashinsu da abincin rayuwarsu, da ajalin da ke kare su, da gajiya da ke tsofar da su, da faruwar al'amura dake bibiye da su, kuma Allah bai taba barin bayinSa babu Annabi aikakke ko kuma littafi saukakke ba, ko kuma wata hanya bayyananniya ba. Manzanni da karancin mabiya ba ya sa su gaza ko kuma yawan masu karyatawa gare su, duk wanda ya gabata daga cikinsu kan sanar musu wanda zai zo daga bayansa ko kuma wanda ya zo daga baya ya sanar da wanda ya gabance shi. A kan haka karnoni suka yi ta shudewa, zamunna suka yi ta wucewa, iyaye suka yi ta gabata Annabawa suka yi ta biyowa, har Allah subhanahu ya aiko Muhammadu Rasulullahi, sallallahu Alaihi wa alihi, domin aiwatar da alkawarinSa da cika AnnabcinSa da Ya karbi alkawari a gurin AnnabawanSa wanda sunansa mashahuri ne, haihuwarsa kuma mai girma ce. A lokacin mutanen bayan kasa al'ummu ne a rarrabe, masu ra'ayoyin zukata dabam-dabam, da hanyoyi mabambanta, tsakanin masu kamanta Allah da halittunSa, ko kuma wuce iyaka a sunanSa, ko kuma mai nuni zuwa ga waninSa, sai Allah Ya shirye su da shi daga bata, ya tserar da su da kokarinsa daga jahilci." Nahjul Balagha Huduba ta. 1.
    ( 61 )

    14- Annabci Tausasawa

    Lalle shi mutum halitta ne mai haddodi masu ban al'ajabi, mai sarkafaffun gabobi a halittarsa da dabi'arsa da ruhinsa da kuma hankalinsa, kai hatta ma a kan kowane daya daga cikin jama'arsa nauo'in zaburar fasadi sun tattara a cikinsa kamar kuma yadda masu zaburarwa zuwa ga alheri da gyara suka tattara a cikinsa ta bangare gudan.
    Allah Ta'ala yana cewa: "Da rayi da abinda Ya daidaita da kuma Ya cusa mata fajircinta da kuma takawarta." (Surar Shamsi: 7-8) "Lalle shi mutum tabbatacce yana c ikin hasara." Surar Asri: 2, da kuma "Lalle ne shi mutum tabbas yana dagawa. Don kawai ganin ya wadata" Surar Alak: 6-7 "Lalle zuciya tabbas mai umarni da mummuna ce". Surar Yusuf: 53. Da sauran ayoyi makamantan wadannan da ke bayyanawa a sarari suna nuni ga irin yadda ran mutum ke kunshe da rauni da kuma sha'awa.
    A bangare na biyu kuma, Allah Ta'ala Ya halitta masa hankali mai shiryarwa tare da shi wanda zai kai shi zuwa ga gyara da kuma guraren alheri da kuma zuciya mai gargadi da ke masa fada kada Ya aikata mummuna da zalunci tare da aibata shi a kan aikata abinda yake mummuna abin zargi.
    Abokin husumar rai da ke cikin zuciya da imani yana tsakanin aron raunanawa ne da kuma hankali. Duk wanda hankalinsa ya yi galaba a kan rauninsa to yana daga cikin mafi kololuwar matsayi masu shiryarwa a `yan adamtakarsu, kammalallau a ruhinsu wanda kuwa rauninsa ya rinjaye shi to lalle yana daga cikin masu hasarar matsayi,


    ( 62 )

    masu taraddudi a yan Adamtaka, masu faduwa zuwa matsayin dabbobi.
    Mafi tsanani daga cikin wadannan masu husuma biyu itace tausasawar zuciya da rundunarta. Don haka ne kake ganin yawancin mutane sun dulmuye a cikin bata, suna nesa da shiriya ta hanyar bin sha'awace-sha'awace da amsa kiran raunin zuciya, "kuma mafi yawan mutane ba za su zama muminai ba koda kuwa ka yi kwadayin haka." Surar Yusuf 103.
    Shi mutum saboda gazawarsa da rashin saninsa game da abubuwan da ke kewaye da shi, da kuma rashin sanin asirran abubuwan da ke kewaye da shi da ma wadanda ke bullowa daga cikinsa shi kansa, ba zai iya sanin dukan abinda zai cutar da shi ko ya amfane shi ba shi da kansa, ba kuma zai iya sanin abinda zai kai shi ga samun sa'ada ko ya kai shi ga tsiyacewa ba, sawa'un a kan abinda ya kebatu da shi ne shi kadai ko kuwa wanda ya shafi dan Adam baki daya da kuma al'ummar da ke kewaye da shi. Shi bai gushe yana jahili kuma yana kara jahilci ne ko kuma kara fahintar jahilcinsa ne duk yayin da iliminsa game da dabi'a ko kuma ababan halitta ya kara karuwa. Saboda haka mutum a tsananin bukatarsa ta son kaiwa ga darajar sa'ada yana bukatar wanda zai dora shi a kan hanya mikakkiya shararriya zuwa ga shiriya domin rundunar hankali ta kara karfafa da haka har ya zamanto mutum zai iya yin galaba a kan abokin gabarsa yayin da ya shiga fagen faman gwabzawa tsakanin rundunar hankali da raunin tausasawar zuciya.
    Yawanci bukatar wanda zai kama hannunsa zuwa ga alheri da gyara na kara tsananta ne yayin da tausasawar zuciya ke yaudarar sa ta hanyar nuna masa abinda yake mummuna cewa mai kyau ne ko kuma kyakkyawa cewa mummuna ne ta nuna masa kyawun fandarewarsa, ta rikitar masa hanyar gyara da sa'ada da ni'ima a lokacin da shi ba shi da masaniyar da zai bambance dukan abinda yake mai kyau mai amfani da kuma wanda yake mummuna marar amfani ga mai gaggawar kutsawa cikin wannan arangamar ne ta yadda ya sani ko kuma ta inda bai sani ba sai dai wadanda Allah Ya kubutar.


    ( 63 )

    Saboda haka abu ne mawuyaci ga mutum masanin ilimin zamani ya kai kansa ga dukan tafarkunan alheri da amfani da kuma sanin dukan abinda zai amfane shi ko ya cutar da shi a duniya da lahira ballantana kuma jahili; sawa'un al'amari ne da ya kebe shi shi kansa ko kuma ya hada da al'umma da yake zaune a cikinta ne. Ba ya taba kaiwa ga wannan masaniyar koda kuwa ya hada kai ya yi taimakekeniya da sauran mutane da ke tare da shi ko da kuwa sun hadu sun yi bincike, koda kuwa sunyi tarurruka da zama dabam-dabam da kuma shawarwari.
    Don haka ne ya zama wajibi Allah Ta'ala Ya aiko da Annabawa da manzanni a cikin mutane domin rahama da tausasawa gare su. "Manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyinSa yana tsarkake su kuma yana koya musu littafi da hikima" (Surar Juma'a: 2). Yana musu gargadi game da abinda ke da cutarwa gare su kuma yana musu albishir game da abinda yake da alheri da gyaruwa da sa'ada a gare su. Tausasawar daga Allah wajibi ne domin tausasawa ga bayinSa na daga cikin tsantsan kamalarSa. Shi mai tausasawa ne ga bayinSa, Mai yawan baiwa, Mai karimci, idan kuwa har ya zamanto a wani guri da ya dace akwai bukatar Ya kwarara kyautarSa da tausasawa to babu makawa Ya zuba tausasawarSa domin babu rowa a farfajiyar rahamarSa, babu nakasa da tawaya a kyautarSa da karimcinSa.
    Ma'anar wajibi a nan ba wai tana nufin cewa wani zai umarce shi da aikata haka ba ne har Ya zama tilas a kansa Ya yi wa wanda Ya yi umarni biyayya! Allah Ya daukaka ga haka, ma'anar wajibi a nan tamkar ma'anar fadin da ake yi ne cewa shi Allah wajibin samamme ne wato ba zai taba koruwa ba ba zai taba yiwuwa a raba shi da samuwa ba.


    ( 64 )

    15- Imaninmu Game da Mu'ujizar Annabawa

    Mun yi imani da ccwa lalle Allah Ta'ala tunda Yake sanya wa bayinsa mai shiryarwa da kuma Manzo to babu makawa Ya sanar da shi gare su, Ya kuma nuna musu ko wane ne shi a ayyane. Wannan kuwa ya takaita ne a kan sanya musu wani dalili da kuma kafa musu hujja a sakon domin cika tausasasarSa da kuma kammala rahamarSa.
    Allah Ta'ala Yana cewa: "Manzanni masu bushara da kuma gargadi domin kada mutane su zama suna da wata hujja a gurin Allah bayan Manzanni kuma Allah Mabuwayi ne Mai hikima." Surar Nisa'i: 165.
    Wannan, kafa hujjar kuwa babu makawa ya ramanto irin wanda ba ya samuwa sai daga mahaliccin halittu, mai sarrafa samammu- wato ya zamanto abin ya dara kudurar dan Adam. Ya sanya shi a hannun shi manzon mai shiryarwa, domin ya zamanto an san shi da shi kuma ya zamanto mai shiryarwa zuwa gare shi wannan dalili da hujja shi ake kira mu'ujiza; wato gagara badau saboda kasancewarsa ya gagari dan Adam, ya yi gasa da shi ko kuma ya kawa makamancinsa.
    Kamar yadda babu makawa ga Annabi ya zo da mu'ujiza ya bayyana ta ga mutane domin ya kafa musu hujja haka nan babu makawa wannan mu'ujizar ya nuna ta kuma yadda za ta gagari malamai da kuma kwararrun zamaninsa; ballantana kuma sauran mutane, tare kuma da danganta wannan mu'ujizar da ikrarin Annabci daga mai mu'ujizar, saboda kasancewarsa yana da sadarwa ruhi da wanda yake jujjuya halittu.
    Idan wannan ya tabbata ga mutum, bayyanar mu'ujiza wadda ta saba wa al'ada, ya kuma yi da'awar Annabci da sako, to a lokacin sai


    ( 65 )

    ya zamanto abin gaskatawar mutane a kiran da yake yi, tare da yin imani da sakon nasa, da bin maganarsa da umarninsa, sai wanda zai gaskata shi Ya yi imani da shi wanda zai ki kuma ya kafirce masa.
    Wannan shi ne abinda ya sa muka ga cewa mu'ujizar kowane Annabi ta dace da ilimi da kuma fasahar zamaninsa. Mu'ujizar Annabi Musa ita ce sanda wanda ke hadiye sihiri da abinda suke yin ba duhunsa saboda kasancewar sihiri a zamaninsa shi ne fannin fasaha da yake mashahuri yayin da sandan ya zo sai dukan abinda suke aikatawa ya baci suka san cewa lalle wannan abu ne da ya fi karfinsu kuma ya dara irin fannin fasaharsu, lalle wannan yana daga cikin abubuwan da, dan Adam ya gaza ya kawo shi kuma kwarewa da ilimi sun dushe a gabansa. Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma sai muka yi wahayi ga Musa kan cewa jefa sandanka sai ga shi yana hadiddiye abubuwan da suke kirkirawa. Kuma gaskiya ta tabbata abinda suke aikatawa kuma ya baci. Sai aka rinjaye a nan ,sa'annan suka koma suna kaskantattu. Kuma aka kifarda masu sihirin suna sujada." Surar A'araf: 117-120.
    Hakanan mu'ujizar Annabi Isa (A.S.) ita ce warkar da makafi da masu albaras da kuma raya matattu saboda shi ya zo ne a lokacin da likitanci shi ne fannin fasahar kwarewar da ke tsakanin mutane kuma akwai malamai akwai likitoci da suke su ne manyan bokaye gare su sai iliminsu ya gaza jeruwa da abinda Annabi Isa (A.S.) Ya zo da shi. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma Manzo zuwa ga Bani Isra'ila cewa lalle ni na zo muku da aya daga Ubangijinku ni ina halitta muku daga laka abinda yake kamar surar tsuntsu kuma in hura a cikinsa ya zamanto tsuntsu da izinin Allah kuma ina warkar da makaho da mai albaras kuma ina raya mamata da izinin Allah kuma ina ba ku labarin abinda kuke ci da wanda kuke taskancewa a gidajenku lalle a cikin wannan akwai aya gare ku idan kun kasance muminai." Surar Al- Imran: 49.
    Mu'ujizar Annabinmu madawwamiya ita ce Alkur'ani saboda shi ya zo ne a lokacin ma'abuta ilimin balaga su ne kan gaba a tsakanin mutane inda ya kure su da balagarsa da bayaninsa. Duk da fasaharsu da balagarsu sai da Alkur'ani ya kaskantar da su ya rikitar da su ya


    ( 66 )

    fahintar da su cewa su ba za su iya fito na fito da shi ba don haka suka sallama masa rinjayayyu bayan sun gaza kasawa da shi, suka ma gaza isa ga kurar da ya tile su da ita ya wuce ya barsu.
    Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma idan da mutane da Aljannu za su taru a kan su zoda kwatankwacin wannan Alkur'anin to da ba za su zo da makamancinsa ba koda kuwa sashensu na taimakon sashe." Surar Isra'i: 88.
    Kalubalantar su da ya yi kan cewa su kawo sura goma suka kasa na tabbbatar da cewa lalle ya gagare su. Allah Ta'ala Yana cewa: "Ko suna cewa shi ne ya kage shi ne ka ce to ku zo da surori goma makamantansa kagaggu kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah in kun kasance masu gaskiya" Surar Hud: 13
    Sa'an nan kuma ya sake kalubalantar su kan su kawo sura guda kamar sa suka gaza. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma idan har kun kasance a cikin kokwanto daga abinda muka saukar to ku zo da sura guda kamar sa kuma ku kira shaidunku da ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya". Surar Bakara: 23
    Allah Ta'ala Yana cewa: "Ko suna cewa ya kage shi ne ka ce ku zo da sura guda kamarsa kuma ku kira duk wanda za ku iya ba Allah in kun kasance masu gaskiya". Surar Yunus: 38.
    Ya sanar da mu yadda suka koma fito na fito da hakora ba da harshe ba Ya sanar da mu cewa shi Alkur' ani wani nau'i ne na mu'ujiza kuma Annabi Muhammad bin Abdullah ya zo da shi ne da kira da kuma da'awar sako. Don haka muka san cewa Manzon Allah (S.A.W.A.) ya zo da gaskiya da hakika kuma shi ma ya gaskata da shi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.


    ( 67 )

    16- Imaninmu Game da Ismar Annabawa

    Kuma mun yi imani da cewa Annabawa ma'asumai ne, ba sa aikata sabo dukkaninsu kazalika Imamai kyakkyawar gaisuwa ta tabbata a gare su. Mun saba da wasu daga cikin musulmi a kan haka don su ba su wajabta isma (rashin aikata sabo) ga Annabawa50ballantana ma Imamai.
    Isma: Ita ce tsarkaka daga aikata zunubi da sabo kananansu da manyansu; da kuma tsarkaka daga mantu
    ____________
    50- A duba sharhin al-Makasid Juzu'i na 5 shafi na 50, da kuma al-Ganiyyatu fi Usuluddin shafi na 161.
    Sayyid Murtadha ya ambata a cikin littatin Tanzihil Anbiya da nassi kamar haka: "Asahabul Hadis da Hashwaiyawa sun halatta wa Annabawa aikata manyan zunubai kafin a ba su Annabci. Daga cikinsu ma har akwai wadanda suka halatta wa Annabawa aikata sabo hatta bayan karbar Annabcin in banda karya a kan al'amuran shari'a, akwai ma wadanda suka halatta karyar amma da sharadin a boyewa ba bayyanawa ba, akwai ma wadanda suka halatta a kowane hali, su Mu'utazilawa kuwa sun haramta cewa Annabawa na aikata sabo babba ko karami kafin annabci da kuma bayan ba su annabcin amma sun halatta aukuwar abinda bai kai karamin zunubi ba gare su kafin annabci da kuma bayan annabcin amma sun yi sabani a kan Shugaban Manzanni Muhammadu (S.A.W.A.) wasu sabi daga cikinsu akwai wadanda suka ce zai iya aikata kananan ayyukan sabo haka nan da gangan, daga cikinsu kuma akwai wadanda suka ce ata tau sam annabawa ba sa taba aikata wani abu da suka san cewa sabo ne sai dai kawai fuskar ba shi wata ma'ana ta dabam. An hakaito daga Nizam da Ja'afar Bin Mubasshir da kuma wasu jama'a da suka bi su a kan cewa aikata sabo daga gare su ba ya yiwuwa sai dai a kan mantuwa da rafkanuwa kuma za a kama su da haka koda kuwa an yafewa al'ummunsu saboda karfin saninsu da kuma martabarsu.

    Tanzihul Anbiya: Gabatarwa.



    ( 68 )

    wa51 , koda kuwa hankali bai kore aukuwar haka daga Annabi ba. Sai dai kawai wajibi ne ya zamanto ya tsarkaka hatta daga dukkan abinda ke zubar da mutunci kamar cin abu a kwararo a tsakanin mutane ko kuma kyalkyala dariya da dai dukkan abinda bai dace a aikata shi ba a tsakanin mutane ba.
    Dalilin da ya sa Isma ta zama wajibi kuwa shi ne idan da har ya halatta Annabi ya aikata sabo ko kuma ya yi kuskure, ko kuma wani abu makamancin wannan ya auku daga gare su to kuwa lalle da biyayya gare su a aikin da suka aikata da sabo ko kuskure bai wajaba ba, ko kuma da idan har ya wajaba to da mun halatta aikata sabo da dogaro da rangwame daga Allah, bilhasali ma dai mun wajabta haka52 ne wannan kuwa abu ne tabbatacce a wajiban addini da kuma a gurin hankali.
    ____________
    51- Ma'anar Isma a luga ita ce: Abu da ke kange mutum daga wani abu wato kamar ya kange shi daga aukuwar wani abu da ba ya so. Akan ce wane ya yi isma da dutse idan ya yi kariya da shi, da haka ne ake kiranta Isma wato fakewa a dutse don kariya da shi, ya zo a Lisanil Arab cewa: "Isma ita ce kariya, a kan ce na kare wani sai ya karu, na yi kariya da Allah idan har ya tsaru daga sabo da tausasawarSa.
    Isma daga Allah Ta'ala kuwa ita ce: Muwafaka da ke kubutar da mutum daga abinda da ya so idan har ya zamanto ya aikata aikin biyayya, kamar yadda muke mika igiya ga mutumin da kogi yake kokarin dulmuyarwa ya kama ya tsira da ita, Allah Ta'ala ya bayyana wannan ma'ana a littafinSa da cewa: "Ku yi riko da igiyar Allah baki daya" Surar Ali Imran: 103. A nan abin nufi da igiyar Allah shi ne addininsa.
    Ya zo daga Imam Zainul Abidin (A.S.) cewa yayin da aka tambaye shi ma'anar ya ce: Shi ne mai riko da igiyar Allah, igiyar Allah kuma shi ne Alkur'ani da Imam, ba sa taba rabuwa har zuwa ranar tashin kiyama, Imam yana shiryarwa ne zuwa ga Alkur'ani shi ma Alkur'ani yana shiryarwa zuwa ga Imam. Wannan shi ne fadin Allah Ta'ala: "Lalle ne shi wannan Alkur'ani yana shiryarwa zuwa ga wadanda suke su ne mafiya daidai " Surar Isra'i: 9.
    Biharul Anwar Juzu'i na 25 shafi na 194 da kuma farko al-Makalat na Shaikh Mufid Juzu'i na 4 shafi na 34. Da kuma Lisanul Arab Juzu'i na 12 shafi na 403 bayani game "Asama".
    52- Domin a cikin yin haka akwai kore ayar Alkur'ani wadda take kwadaitarwa da a yi biyayya ga Manzon Allah (S.A.W.A.) cewa: "Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa zai shigar da shi gidajen Aljanna wadanda koramu ke gudana a karkashinsu." Surar Nisa'i: 13. da kuma fadin Allah Ta'ala cewa: "Kuma wanda

    ( 69 )

    Idan kuwa biyayya gare shi bata wajaba ba a kan haka to kuwa wannan ya saba wa annabci wanda babu makawa tana tare da wajabcin da'a dimin da'iman. Idan kuwa ya zamanto duk abinda ya auku daga gare shi muna jin cewa imma daidai ne imma kuskure to bai wajaba a yi masa da'a a kan kome ba, sai fa'idar aiko Annabawa ta zamanto ta tafi haka nan kawai Annabin kuma sai ya zama kamar sauran mutane, maganarsa ba ta da wata kimar da za a dogara a kanta da'iman kamar yadda biyayya gare shi ba za ta zama tilas ba. Ba ma za a sami kwanciyar hankali ba baki daya game da maganganunsa da ayyukansa.53
    Wannan kuma dalili ne da ke tabbatar da cewa Isma na tare da Imami domin kaddara cewa shi zababbe ne daga Allah Ta'ala don shiryar da mutane a matsayin halifan Annabi. Za mu yi karin bayani a fasali game da Imamah.
    ____________
    ya bi Allah da Manzon to wadannan suna tare da wadanda Allah ya yi ni'ima gare su," Nisa'i: 69 da kuma fadinsa cewa: "Kuma wanda ya bi Manzon Allah to Lalle ya bi Allah ne" surar Nisa'i: 80 da kuma: "Lalle hakika gare ku daga Manzon Allah akwai kyawawan abin koyi ga duk wanda ke kaunar Allah da ranar Lahira kuma ya ambaci da yawa" Surar Ahzab: 22 da kuma fadin Allah Ta'ala: "Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa to lalle ya rabbonta da rabo mai girma". Surar Abzab: 71.
    53- Domin a cikin yin haka akwai kore ayar Alkur'ani da ke kwadaitar da biyayya ga Manzon Allah (S.A.W.A.) cewa: "Kuma wanda ya bi Allah da ManzonSa zai shigar da shi gidajen Aljanna da koramu ke gudana a karkashinsu." Nisa'i: 13
    "Kuma wadanda suka yi da'a ga Allah da ManzonSa to wadan suna tare da wadanda Allah ya yi ni'ima gare su". Surar Nisa'i: 69.

    ( 70 )

    17- Imaninmu Game da Siffofin Annabi

    Mun yi imani da cewa, Annabi kamar yadda ya wajaba ya zamanto ma'asumi haka nan ya wajaba ya zamanto yana da mafi kamalar siffofin dabi'u da hankali wadanda mafifita sune jarumtaka, da iya tafida jama'a, da shugabanci da hakuri, da karfin kwakwalwa da hazikanci, har ya zamanto babu wani daga cikin mutane da zai yi kusa da shi a kan haka, domin ba don haka ba da babu yadda Annabcin ya zamanto shugabaci a kan dukan halittu kamar kuma yadda ba zai yiwu ya zamanto ya tafi da al'amuran duniya baki daya ba.
    Kazalika wajibi ne ya zamanto mai tsarkin haihuwa dan halas, amintacce, mai gaskiya wanda yake tsarkakakke daga dukkan miyagun dabi'u hatta kafin aiko shi saboda zukata su amintu da shi rayuka kuma su juya zuwa gare shi hatta ma don ya cancanci wannan matsayi mai girma daga Ubangiji.


    ( 71 )

    18- Imaninmu Game da Annabawa da Littafansu

    Mun yi imani a dunkule da cewa dukkan Annabawa da Manzanni a kan gaskiya suke, kamar yadda muka yi imani da kasancewarsu ma'asumai tsarkakakku. Musanta Annabcinsu kuwa, da zaginsu, da yin izgili da su yana daga kafirci da zindikanci, domin yin haka yana nufin karyata Annabinmu wanda Ya ba da labari game da su da kuma game da gaskiyarsu.54
    Wadanda aka sani daga cikinsu kuwa kuma aka san shari'o'insu kamar Annabi Adam (A.S.) da Annabi Nuhu (A.S.) da Annabi Ibrahim (A.S.) da Annabi Dawud (A.S.) da Annabi Sulaiman (A.S.) da Annabi Musa (A.S.) da Annabi Isa (A.S.) da sauran Annabawan da Alkur'ani ya ambace su a sarari ya wajaba a yi imani da su a ayyane55
    ____________
    54- "Ku ce mun yi imani da Allah da abinda aka saukar gare mu da abinda aka saukar zuwa ga Ibrahima da Isma'ila da Ishaka da Yakuba da Jikoki da abinda aka ba wa Musa da Isa da abinda aka ba wa Annabawa daga Ubangijinsu, ba ma rarrabewa a tsakanin kowa daga cikinsu kuma mu masu sallamawa ne a gare shi." Surar Bakara: 136
    "Amma tabbatattu a cikin ilimi daga cikinsu da muminai, suna imani da abin da aka saukar zuwa gare ka da abinda aka saukar kafin kai kuma suna masu tsai da salla suna ba da zakka suna masu imani da Allah da ranar lahira wadannan za mu ba su lada mai girma" Surar Nisa'i: 162.
    55- Ya zo a ruwayoyi da hadisai cewa adadin Annabawa ya kai dubu dari da ashirin da hudu da dari uku da ashirin da uku daga cikinsu ne, ko kuma dari uku da ashirin da biyar a bisa sabanin ruwaya, su kuma wadannan Annabawan sunan mafi yawansu bai zo a Alkur'ani ba. Allah Ta'ala na cewa: "Kuma lalle hakika mun aika wasu Manzannin kafin kai, daga cikinsu akwai wadanda muka ba ka

    ( 72 )

    labarinsu daga cikinsu akwai wadanda ba mu ba ka labarinsu ba" Surar Ghafir: 78.
    Adadin wadanda sunansu yazo a Alkur'ani kuwa ashirin da shida ne kamar haka:-
    1- Annabi Adam (A.S.): sunansa ya zo sau 18 a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala yana cewa: "Lalle Allah ya zabi Adama da Nuhu da zuriyar Ibrahim da zuriyar Imran a kan dukkan talikai." Surar Al- Imran 33, Kamar Kuma yadda ya zo da Kiran Bani Adam sau Bakwai,
    2- Annabi Nuhu (A.S.): sunansa ya zo a Alkur'ani sau 43, game da shi Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma lalle Mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa ya zauna a cikinsu har shekaru dubu babu hamsin" Surar Ankabutu: 14.
    3- Annabi Idris (A.S.): sunansa ya zo sau biyu a Alkur'ani, Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma ka ambata Idris a cikin littafi Lalle shi ya kasance mai yawan gaskiya Annabi" Surar Maryam: 56.
    4- Annabi Hudu (A.S.): Sunansa ya zo sau goma a cikin Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala na cewa: "Kuma zuwa ga Adawa dan'uwansu Hudu, ya ce ya mutanena ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bautawa baicin Shi." Surar A'araf: 69 da Surar Hudu: 50.
    5- Annabi Salihu(A.S.): Sunansa ya zo sau tara a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle Mun aika wa Samudawa dan'uwansu Salihu ku bauta wa Allah sai suka zamanto bangarori biyu suna husuma." Surar Namli: 45.
    6- Annabi Ibrahim(A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau 69 a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle Mun aika Ibrahima kuma Muka sanya Annabci da littafi a zuriyarsu..." Surar Hadid: 26.
    7- Annabi Ludu(A.S.): sunansa ya zo a gurare 26 a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma lalle Ludu tabbas yana daga Manzanni". Surar Saffat: 133.
    8- Annabi Isma'il(A.S.): Ambaton sunansa ya zo a gurare goma sha daya a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Ibrahima da Isma'ila da Ishaka da Yakuba..." Surar Nisa'i: 163.
    9- Alyasa'u(A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau biyu a Alkur'ani, game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Da Isma'ila da Alyasa'u da Yunusa da Ludu kuma kowanne Mun fifita shi a kan talikai."
    10- Zulkifli(A.S.): An ambace shi sau biyu a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma ka ambaci Isma'ila da Alyasa'u da Zulkifli kuma duka suna daga zababbu." Surar Sad: 48.

    ( 73 )

    11- Annabi Ilyasu (A.S.): An ambace shi sau biyu a Alkur'ani, Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle Ilyasu tabbas na daga cikin manzanni." Surar Saffat: 123.
    12- Annabi Yunus (A.S.): Ambatonsa ya zo sau hudu a Alkur'ani. Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma lalle Yunusa Tabbas yana daga cikin Manzanni." Surar Saffat: 139.
    12- Ishak (A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau goma sha bakwai a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma mun yi Masa albishir da Ishaka Annabi daga cikin Salihai." Surar Saffat: 112.
    14- Annabi Yakub (A.S.): An ambaci sunansa sau goma sha shida a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "...Kuma Muka yi wahayi ga Ibrahima da Isma'ila da Ishaka da Yakuba da Asbata da Isa..." Surar Nisa'i: 163
    15- Annabi Yusuf (A.S.): Ambatonsa ya zo sau ashirin da bakwai a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma daga cikin zuriyarsa akwai Dawuda da Sulaimanu da Ayyuba da Yusufa da Musa da Haruna kuma haka nan Muke sakamtawa masu kyautatawa." Surar An'am: 84.
    16- Annabi Shu'aib (A.S.): Sunansa ya zo sau goma sha daya a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa:"Kuma ga Madyana dan'uwansu Shuaibu." Surar A'araf: 85, Hud: 84, Ankabut: 36.
    17- Annabi Musa (A.S.): Ambatonsa ya zo sau dari da talatin da shida a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle tabbatacce Mun aiki Musa da ayoyinMu kan cewa ka fitar da al'ummarka daga duffai zuwa ga haske kuma ka tunatar da su game da ranakun Allah lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga dukkan mai hakuri mai yawan godiya." Surar Ibrahim: 5.
    18- Annabi Haruna (A.S.): Ambaton sunansa ya zo sau ashirin a Alkur'ani. Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma Muka ba shi Dan'uwansa Haruna Annabi daga rahamarMu." Surar Maryam: 53.
    19- Annabi Dawud (A.S.) Ambatonsa ya zo sau goma sha shida a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Da Ayyuba da Yunusa da Haruna da Sulaimana kuma Mun ba wa Dawuda Zabura." Surar Nisai: 163.
    20- Annabi Sulaiman(A.S.): Ambatonsa ya zo sau goma sha bakwai a Alkur'ani. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma lalle hakika Mun ba wa Dawuda da Sulaimanu ilimi" Surar Namli: 15.
    21 - Annabi Ayyuba (A.S.): An ambace shi sau hudu a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Ibrahima da Isam'ila da Ishaka da Ya'akuba da Asbata da Isa da Ayyuba." Surar Nisa'i: 163.

    ( 74 )

    22- Annabi Zakariyya (A.S.): Ambatonsa ya zo sau bakwai a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'ala Yana cewa: "Da Zakariyya da Yahya da Isa da Ilyasu kowane yana daga Salihai" Surar An'am: 85.
    23- Annabi Yahya (A.S.): Sunansa ya zo sau biyar a Alkur'ani. Game da shi Allah Ta'
  • Comments

    Loading...
    no comments!

    Related Posts