Logo

makoyar ilimi ba, su sun zamanto kamar dabbobi masu kiwo da duwatsu masu tsauri."

Nahjul Balagha Huduba ta 108.



( 82 )

21- Imaninmu Game da Alkur'ani Mai Girma.

Mun yi imani cewa Alkur'ani wahayin Ubangiji ne da ya sauko daga Allah a harshen AnnabinSa, akwai bayanin kome da kome a cikinsa; shi ne Mu'ujiza madawwamiya wadda ta gagari bil Adama wajen karawa da ita a fasaha da azanci, abinda ya kunsa na daga hakika da sannai madaukaka. Jirkita ko canji ko karkacewa ba sa shafar sa. Allah Ta' ala Yana cewa:
"Mu Mu ne Muka saukar da ambato kuma Mu gare shi lalle masu kariya ne". Surar Hijri: 9.
Alkur'anin da ke hannunmu wanda ake karanta shi a yau shi ne wanda aka saukar wa Annabi (S.A.W.A.), duk kuma wanda ya yi da'awar sabanin wannan to shi mai kage ne, ko mai rikitarwa ko mai kuskure ne dukaninsu kuma ba a kan shiriya suke ba; domin shi Alkur'ani zancen Allah ne wanda: "Karya ba ta zuwa masa ta gaba gare shi ko kuma ta bayansa." Surar Fusilat: 42.
Daga cikin dalilan da ke tabbatar da mu'ujizarsa akwai cewa duk yayin da zamani ya dada tsawo ilimi da fasaha kuma suka dada ci gaba shi yana nan daram a kan abubuwan da yake kaddamarwa da daukarkar manufa da abubuwan da ya kunsa na ra'ayoyi babu wani kuskure da ke bayyana daga cikinsa dangane da tabbatattun matsayi na ilimi kamar kuma yadda ba ya taba kunsar tawaya game da falsafa ta hakika da yakini, sabanin littafan da malamai da manyan masanan falsafa kome matsayin da suka kai kuwa a fagen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa da tunani. Domin duk yayin da bincike ya ci gaba to yakan bayyana a sarari cewa rarrauna ne ko sabo ne ko kuma kuskure, hatta a gurin manyan masana falsafar kasar Girka kamarsu Sakarot da

( 83 )

Aplato a Arostatle wadanda kowa da kowa daga cikin wadanda suka zo daga bayansu suka musu shaida da cewa su ne iyayen ilimi da kuma amfani da kwakwalwa.
Kazalika mun yi imani da mutunta Alkur'ani mai girma da daukaka shi a magana da kuma a aiki. Bai halatta a najasta koda kalma guda a cikinsa wadda aka dauka cewa yanki ne daga cikinsa da kuma nufin cewa daga cikinsa take.
Kamar kuma yadda bai halatta ba ga wanda ba shi da tsarki ya shafa kalmominsa ko harrufansa. "Babu mai shafa shi sai wadanda suke tsarkakakku". Surar Waki'a: 79.
Sawa'un sun kasance suna da babban kari ne kamar janaba ko haila ko jinin biki da makamantansu, ko kuma karamin kari koda ma barci ne kUwa sai dai bayan yin alwala ko kuma yin wanka a bisa asasin filla-fillan bayanan da ke cikin littafan fikihu.
Kazalika bai halatta a kona su ba, bai halatta a wulakanta shi ba, koda ta wace fuska ne kuwa da yake sananne a tsakanin mutane kamar jefarwa, ko sanya masa kazanta, ko shurin sa da kafa , ko sanya shi a guri wulakantacce. Idan da wani zai wulakanta shi da gangan ko tozarta shi da aikata daya daga cikin wadannan abubuwan da muka ambata da makamantansu to shi ya shiga cikin masu karyata addinin Musulunci da abubuwan tsarkakewarsa, kuma abin hukuntawa ne da ficewa daga addini da kafircewa ga Ubangijin talikai.


( 84 )

22- Hanyar Tabbatar Da Gaskiyar Addinin
Musulunci Da Sauran Shari'u Magabata.

Idan muka yi jayayya da wani a kan ingancin addinin Musulunci za mu iya ja da shi mu tabbatar masa da mu'ujizarsa madawwamiya wato Alkur'ani mai girma kamar yadda ya gabata game da kasancewarsa gagarabadau. Kazalika Alkur'ani shi ne hanyar sanya mana yakini mu da kanmu yayin da kokwanto ya fara shigar mu saboda irin tambayoyin da kan tasowa mutum a zuciya kamar yadda babu makawa kowane mutum mai yanci ya fada cikin irin wadannan tambayoyin yayin karfafa akidarsa da tabbatar da ita.
Dangane da shari'o'in da suka gabata kuwa kamarsu Yahudanci da Kiristanci ba mu da wata hujja kafin amincewarmu da Alkur'ani ko kuma idan muka raba kammu da addinin Musulunci, babu hanyar da za mu bi mu gamsar da kammu ko kuma mu gamsar da mai tambaya, domin su wadannan addinan ba su da sauran wata mu'ujiza tasu da ta saura kamar yadda Alkur'ani yake. Abinda mabiyan wadannan addinan ke dauke da shi kuma ana zarginsu a kan daukar da suke yi ko kuma sun sanya hannu a cikinsa. Babu wani abu da ke cikin littafan addinan da suka gabata da ke hannun mutane a wannan zamanin wanda ya dace ya zama mu'ujiza madawwamiya mai karfi da za ta iya yanke hanzari, ko dalili mai gamsarwa kafin a yi imani da Musulunci.
Sai dai kawai mu musulmi ya inganta ne a gare mu da mu gaskata Annabcin ma'abuta shari'unda suka gabata domin bayan gaskatawarmu da addinin musulunci to ya wajaba a kanmu mu gaskata dukkan abinda ya zo da shi, kuma a cikin abinda ya zo da shi akwai gaskata Annabcin Annabawan da suka gabata kamar yadda ya gabata a

( 85 )

sashen bayani game da abinda muka yi imani da shi game da Annabawa da littafansu.
Saboda haka musulmi ya wadatu ga barin bincike game da ingancin shari'un da suka gabata, kiristanci da kuma abinda ya gabace shi bayan ya yi imani da Musulunci domin yin imani da shi imani da su ne, imani da shi imani ne da sakonnin da suka gabata da kuma Annabawan da suka shude. Bai wajaba a kan musulmi ya yi bincike game da gaskiyar mu'ujizar Annabawansu, domin abin kaddarawa shi ne cewa shi musulmi ne kuma ya yi imani da su saboda imaninsa da Musulunci kuma ya wadatar.
Na'am, idan da mutum, zai yi bincike game da addinin Musulunci ya ji cewa bai gamsu ba to lalle ne a kan kamar yadda hankali da kuma wajabcin neman ilimi suka wajabta Ya yi bincike game da addimin kirista domin shi ne addinin karshe kafin musulunci. Kazalika idan ya bincika addinin kirista bai gamsu ba ta sai kuma ya dukufa a kan addinin da ya gabace shi wato Yahudanci... Haka nan dai zai yi ta bincike har sai ya kai ga yakini yana binciken addinan da suka gabata har ya tabbatar da ingancinsa ya yi imani da shi ko kuma rashin ingancinsa ya yi watsi da su baki daya.
Wato sabanin wanda ya tashi a addinin Yahudanci ko kuma Kiristanci, shi Bayahude imaninsa da addininsa ba zai wadatar da shi ba ya bar binciken addinin Nasaranci da kuma addinin Musulunci bilhasali ma aiki da hankali da neman sa wajibi ne a kansa - kamar yadda hankali ya hukunta, haka nan shi ma addinin Kiristanci ba isar masa ba ya zama ya yi imani da Almasihu (A.S.) wajibi ne ya yi kokari wajen sanin Musulunci da ingancinsa. Domin Yahudanci da addinin kirista ba su kore shari'ar da za to daga bisani ba; wadda za ta shafe ta, kazalika Annabi (A.S.) bai ce babu Annabi bayan shi ba sabanin haka ma Annabi Isa (A.S.) ya yi bushara da zuwan Annabin da zai zo bayansa. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma yayin da Isa dan Maryama ya ce Ya Bani Isra'la lalle ni Manzon Allah ne gare ku, mai gaskata abinda ke gaba gare ni na Attaura kuma mai bayar da bushara game da wani Manzo da ke zuwa bayana, sunansa

( 86 )

Ahmad. Sai dai a lokacin da Ya zo musu da hujjoji bayyanannu sai suka ce wannan sihiri ne bayyananne." Surar Saff: 6.
Ta yaya zai halatta ga Kiristoci da Yahudawa su gamsu da akidojinsu, su dogara da addininsu kafin su yi bincike game da shari'ar da ta biyo bayansa wato kamar shari'ar addinin Kirista, da kuma addinin Yahudanci dangane da Musulunci. Wajibi ne kamar yadda yake a bisa dabi'ar hankali su yi bincike game da shari'ar da ta zo daga baya. Idan ingancinta ya tabbata gare su to sai su canja zuwa gare ta a addininsu, idan kuwa ba haka ba to ya dace a bisa hukuncin hankali su ci gaba da bin addininsu na da tare da riko da shi.
Shi kuwa musulmi kamar yadda muka riga muka fada idan har ya yi imani da Musulunci to ba bukatar ya yi bincike game da addinan da suka gabaci addininsa da kuma wadanda ake da'awa bayansa. Wadanda suka gabata dai a kaddare an san cewa ya yi imani da su don me kuma zai bukaci dalili ko hujja game da ita? Abin kawai da ya hukunta masa game da su shi ne cewa Shari'ar Musulunci ta shafe su don haka bai wajaba a yi aiki da hukunce-hukmcensu ko littafansu ba.
Wadanda ake da'awarsu daga baya kuwa shi ne saboda cewa Annabin Musulunci Muhammadu (S.A.W.A.) Ya ce: "Babu wani Annabi bayana."58 Kuma shi mai gaskiya ne kuma Amini. "Kuma shi ba ya magana a kan son rai ba wani abu ba ne face wahayi da ake yiwo wahayinsa" Surar Najmi: 3-4.
Don haka saboda mene ne ba za'a bukaci hujjar da'awar Annabcin da aka yi daga baya ba idan har mai da'awar ya yi da'awa?
Na'am yana kan musulmi ya yi bincike bayan tsawon lokaci tsakaninsa da wanda ya kawo sakon, a kuma sami Mazhabobi da tafarkuna dabam-daban ya yi bincike ya bi hanyar da ta fi dacewa wajen isar da shi ga sanin ainihin hukunce-hukuncen da aka saukar wa
____________
58- Sahih Muslim Juzu'i na 3 shafi na 1471 hadisi na 1842 da Musnad Ahmad Juzu'i na 3 shafi na 32, da Mu'ujamul Kabir Juzu'i na 8 shafi na 161 hadisi na 7617 da sunanu Baihaki Juzu'i na 8 shafi na 144 da Amali Shaikh Mufid: 33.
( 87 )

wanda ya kawo sakon Annabi Muhammadu (S.A.W.A.) domin shi musulmi an kallafa masa aiki da dukkan hukunce hukuncen da shari'a ta zo da su kamar yadda aka saukar.
Sai dai kuma ta yaya zai san cewa ita ce shari'ar da aka saukar kamar yadda take alhali musulmi sun sassaba jama'a-jama'a, sun rarraba, babu salla guda, babu ayyukan ibada da aka yi ittifaki a kansu, ayyuka ba su zama daidai ba hatta a bangaren mu'amala... don haka yaya zai yi? Da wace irin hanya zai yi salla? Da wace irin fuska na daga ra'ayoyi zai yi aikin ibada da mu'amalarsa kamar aure, da saki, da gado da saye da sayarwa da zartar da haddi, da sauransu?
Kuma sam bai halatta gare shi ya bi ra'ayin iyaye ba ko ya koma ga abinda zuriyarsa da mutanensa ke kai ba, sai dai ma babu makawa ya zama yana da yakini shi da kansa tsakaninsa da Allah Ta'ala domin babu wata zazzagawa a nan ba rufa-rufa, babu raragefe babu zurfafawa.
Na'am babu makawa ya samu yakinin cewa ya bi hanyar da ya yi imani da cewa zai sauke nauyin da ke kansa tsakaninsa da Allah. Ya kuma tabbatar da cewa ba za a yi masa azaba a kai ba, Allah kuma ba zai aibata shi a kan bin ta da aiki da ita ba. Bai halatta ba zargin mai zargi ya dame shi a kan tafarkin Allah "Shin mutum yana tsammanin za a bar shi haka nan ne sakaka kawai." Surar Alkiyama: 36.
"Lalle shi mutum a game da kansa mai gani ne." Surar Kiya 14.
"Lalle wannan fadakarwa ce don haka wanda ya so ya kama hanya zuwa ga Ubangijinsa." Surar Muzammil: 19.
Tambaya ta farko da za ta fara taso masa ita ce, shin ya kama tafarkin zuriyar gidan Manzon Allah ne ko kuwa tafarkin wasu daban? Idan ya kama tafarkin Ahlul Bait, zuriyar gidan Manzo (S.A.W.A.) shin tafarkin Imamiyya "Isna Ashara', masu bin Imamai sha biyu, shi ne ingantaccen tafarki ko kuma tafarkin wadansu daga bangarori dabam-daban? Idan kuma tafarkin Ahlussunna ya kama to da wa zai yi koyi daga cikin Mazhabobi hudun nan ne ko kuwa daga wasu


( 88 )

mazhabobi daban daga cikin wannan bangaren? Haka nan dai tambayoyi za su yi ta tasowa ga duk wanda ba ya tunani 'yanci da zabi har ya kai ga gaskiya abar dogaro.
Saboda haka bayan wannan ya wajaba a kanmu mu yi bayani game da Imama, mu yi bayani a kan abinda ke biye da ita game da akidar Imamiyya Isna Ashariyya, Masu bin Imamai goma sha biyu.



( 89 )

FASALI NA UKU


Imaninmu Game Da Imamanci:

  • Ismar Imami
  • Siffofin Imami da Iliminsa
  • Biyayya ga Imamai
  • Son Ahlul Bait, Zuriyar Gidan Manzo
  • Imamai
  • Imamanci Da Nassinsa Yake
  • Adadin Imamai
  • Al- Mahdi
  • Raja'a
  • Takiyya


    ( 90 )


    ( 91 )

    23- Imaminmu Game Da Imamanci

    Mun yi Imani cewa asalin Imamanci na daga cikin jiga-jigan addini59 kuma imani ba ya cika sai da imani da shi kuma bai halatta a
    ____________
    59- Imamanci shi ne jigo na hudu a cikin jiga-jigan musulunci a gurin Mazhabar Ahlul Bait Masu bin Imamai goma sha biyu, wato Shi'a Imamiyya, Imamanci kuma yana bayan Annabci a muhimmanci kuma za'a iya cewa ita ce ka'idar da ke bambance Mazhabar Imamiyya daga sauran Mazhobabi na Musulunci; kuma Imamanci asasi ne na tunani da Mazhabar mabiya Ahlul Baiti suka gina Mazhabarsu a kai.
    Imamanci: a lugga yana nufin shigewar gaban wani mutum domin sauran mutane su bi shi su yi koyi da shi, don haka Imami shi ne wanda mutane suke koyi da shi, mutanen da ke bin sa kuma su ne mamu. Jam'insa kuma shi ne Imamai. Kalmar Imami ta zo a Alkur'ani har sau goma sha biyu gurare dabam-daban. Akwai guraren da ta zo da sigar mufradi ba jam'i ba har sau bakwai a: Surar Bakara aya ta 124 da Surar Hudu: 17 da Surar Hijri aya ta: 79 da Surar Isra'i aya ta: 71 da Surar Furkan aya ta 74 da Surar Yasin aya ta 12, da Surar Ahkaf aya ta 12.
    Sa'an nan kuma akwai guraren da ta zo da sigar jam'i sau biyar wadanda su ne kamar haka: "Surar Taubati:12, Surar Anbiyai aya ta 73, Surar Kasas aya ta 5 da kuma ta 41 da Surar Sajdati aya ta 24".
    Ma'anarsa ta Ka'ida kuwa Imamanci yana nufin: Mukami ne da Ubangiji Allah kan zabi bayinSa ya ba su kamar yadda yake zaben Annabawa, kuma yakan umarci Annabi ya sanar wa al'umma wannan Imamin ya kuma umarci mutane da su yi masa biyayya. Mutane ba su da wani ikon su zaba wa kansu Imami: Allah Ta'ala yana cewa:
    "Kuma Ubangijinka yakan yi halitta kuma Yana zabe su ba su da wani zabi." Surar Kasas: 68.
    Shi Imami ya bambanta da Annabi ne da cewa Annabi ana yi masa wahayi shi kuwa Imami ba a yi masa wahayi, shi Imami yana karbar hukunce-hukunce ne daga Annabi da shiryarwar Ubangiji. Don haka shi Annabi mai isar da sako ne daga Allah


    ( 92 )

    kwaikwayi iyaye a kan haka ba, ko kuma zuriya ko masu tarbiyya kome girmansu da darajarsu kuwa, sai dai ma ya wajaba ne a nemi sani a yi bincike a game da shi kamar yadda ya wajaba a yi a kan Tauhidi da Annabci.
    Alal akalla imani da sauke nauyin da ke kan mukallafi yana daga cikin wajiban shari'a wadanda aka wajabta masa kuma sun dogara ne a kan Imani da su tabbatarwa ko korewa koda kuwa ba jigo ne daga cikin jiga-jigai da a kwaikwayi wani a kansu ba saboda shi kansa ta wannan kwibin wajibi ne a yi imani da shi. Wato ma'ana ta bangaren wajabcin sauke nauyin da ya wajaba a kansa tabbatacce daga Allah Ta'ala da kuma a hankalce; kuma ba dukkansu ne aka san su ta fuskar matabbacin dalili ba don haka babu makawa a koma ga wanda muka san cewa tabbas bin sa zai kai mu ga sauke nauyin da ya wajaba a kanmu, wato mu koma ga Imam ga wanda ya yi Imani da Imam ko kuma wani da ba Imam ba ga wadanda suka yi imani da wanin Imam.
    Kazalika mun yi imani cewa Imamanci tausasawa ne daga Allah kamar Annabci. Don haka babu makawa a kowane zamani ya zamanto , akwai Imami mai wakiltar Annabi a aikinsa na shiryar da bil Adama60 , da dora su a kan abinda yake maslaha a Sa'adar duniya da Lahira kuma biyayyar da Annabi ya cancata daga mutane baki daya shi ma ya
    ____________
    shi kuma Imami mai isarwa ne daga Annabi. Wannan shi ne abinda Mazhabar Ahlul Bait ke nufi da Imamanci.
    Amma a gurin sauran Mazhabobi kuwa Imamanci na nufin shugabanci ne na gaba daya a kan al'amuran addini da al'amuran duniya don Halifantar Annabi (S.A.W.A.) da hukunce hukuncensa a rassan al'amuran ibada. Domin karin bayani a duba littafan luga, da Aslus Shi'a wa Usuliha da Al'aka'iduj Ja'afariyya da Milal Wan Nihal na Shahristani da Sharhil Makasid.
    60- Allah Ta'ala Yana cewa: "Mu Mune Muka aika Manzo mai albishir kuma mai gargadi kuma babu wata al'umma face mai gargadi ya je mata". Surar Fatir: 24.
    Hadisai da dama da ke nuna cewa kasa ba ta taba zama babu Hujja. A duba Usul Kafi Juzu' i na 1 shafi na 136 Babun Annal Aradha la Takhlu minal Hujja, da kuma na 137 Babun Annahu Law Lam yabka fil Ardhi Illa Isnani La kana Ahaduhuma Hujja.


    ( 93 )

    cancata domin tafi da al'amuransu da maslaharsu, da tabbatar da adalci a tsakaninsu, da gusar da zalunci da kiyayya daga tsakaninsu.
    A bisa wannan asasin Imamanci ya zamanto ci gaban aikin Annabci, dalilin kuma da ke wajabta aiko da Annabawa da Manzanni ne ainihin wanda ke wajaba ayyana Imami bayan Manzon Allah.
    Wannan kuma shi ne dalilin da ya sa muke cewa: Lalle Imamanci ba ya taba yiwuwa sai da nassi daga Allah Ta'ala a bisa harshen Annabi ko kuma a bisa harshen Imamin da ya gabata; kuma Imamanci ba nadin ko zabin kowa ba ne a tsakanin mutane61, ba wai al'amarinsu
    ____________
    61- Ya riga ya shahara a tsakanin malaman addinin Musulunci game da sanya Imami akwai maganganu biyu da ba su da na uku. Akwai masu cewa Imamanci ra'ayi ne kuma zabin mutane ne ke ayyana shi. Akwai kuma wadanda ke cewa ayyanawa ne daga Allah. Kuskuren ra'ayi na farko abu ne da shi'a Imamiyya suka yi ittifaki a kai domin wajibi ne Imami ya zama Allah ne Ya ayyana shi kuma shi kuma Annabi ya nuna shi ya kuma yi wasici da yi masa biyayya bayansa - wato kamar yadda Manzon Allah (S.A.W.A.) ya yi a Ghadir Khum - sa'annan shi kuma Imamin sai ya yi wasici da biyayya ga mai zuwa bayansa kuma ya sanar da shi, haka nan za a yi ta yi bi da bi. Ko kuma a ga wata Mu'ujiza ta bayyana a hannunsa domin "Isma" Sharadin Imamanci ce kuma tana daga boyayyun al'amura wadda babu wanda ya san ta sai Allah Ta'ala.
    Su kuwa sauran Mazhabobi da ba Imamiyya ba cewa suka yi:
    Imamanci ba a shardanta nadawar Annabi ko alkawartawarsa game da shi ba, yana iya zama ta hanyar yin Mubaya'a, wato shi ne malamai masana halal da haram su yi wa wani mutum guda mubaya'a su sanya shi Imami - wannan kuwa yana ginuwa ne a kan sharadin rashin "Isma" ga shi Imamin kuma ba sharadi ba ne ya zamanto duka kowa da kowa ya yi masa mubaya'a hatta mubaya'ar mutum guda ma tana iya wadatarwa. Idan kuwa har Mubaya'ar ba ta yiwu ba to akwai wata hanyar nada Imamin: Tilastawa da kankanewa, idan Imami ya mutu wani wanda ya cika sharuda ya maye gurbinsa ba tare da an sanya shi ko an yi masa mubaya'a ba ya kuma tilastawa mutane kansa to halifancinsa ya tabbata koda kuwa fasiki ne Jahili, Ja'iri, Azzalumi kuma suka ce bai halatta ba a tsige Imami koda kuwa fasiki ne amma idan da wani da ya fi shi karfi zai zo ya kifar da shugabancinsa ya kuma tilasta kansa a kan mutane to da shi ma ya zama Imami.
    Tambaya a nan ita ce shin hankali yana yarje wa mutum ya bi mazhabar da ke wajabta biyayya ga Imami fasiki, ja'iri, jahili ba don kome ba sai dan kawai shi ne ya fi karfi da kudurar tilasta kansa a kan wasu koda ta hanyar fasikanci da ja'irci?

    ( 94 )

    ba ne da idan suka so za su dasa wanda suke son dasawa ko kuma su ayyana wanda suka son ayyanawa ya zama Imami a gare su, ko kuma a duk lokacin da suka so barin ayyanawar sai su bari su zama haka nan sakaka ba su da Imami bil hasali ma "Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu ne mutuwa irin ta jahiliyya"62 kamar yadda haka ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W.A.) a hadisi.
    A bisa wannan asasin ba zamani daga zamuna da zai zamanto babu Imami wanda aka wajabta yi masa biyayya ba a cikinsa, wanda kuma Allah ne Ya nada shi, sawa'un mutane sun ki ko ba su ki ba, sawa'un sun taimake shi ko sun ki taimakon sa, sawa'un sun yi masa biyayya ko sun ki yi masa biyayya, sawa'un yana hallare ne ko kuwa yana suturce ne daga idandunan mutane - domin kamar yadda ya inganta Annabi (S.A.W.A.) ya suturtu daga ganin mutane, kamar yadda ya suturtu a cikin kogo wanda game da shi Allah Ta'ala ke cewa: "Idan ma ba ku taimake shi ba to ai Allah Ya riga Ya taimake shi yayin da wadanda suka kafirta suka fitar da shi yana na biyun su biyu yayin da suke cikin kogo yayin da yake cewa
    ____________
    Kuma bai halatta a cire shi ba sai dai da wanda ya fi shi karfi ya tilasta shi sa'an shi ya zamanto shi ne Imamin? Shin wannan shi ne Imamin da idan mutum ya mutu bai san shi ba ya mutu mutuwar jahiliyya? To wannan Mazhabar ina matsayinta game da maganar Allah Ta'ala cewa: "Shin wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya shi ne ya fi cancantar a bi shi ko kuwa wanda ba ya shiryarwa sai an shiryar da shi, me ya same ku kuke hukunta haka?" Surar Yunus: 35.
    A duba Littafin "Nahjul Hakk wa kashussidki shafi na 168. Da sharhul Makasid na Taftazani Juzu'i na 5 shafi na 233, da At- Tamhid na Bakilani: 168 da Aslus shi'a wa Usuliha 22'da Aka'idi Ja'afariyya: 29.
    62- Al- Kafi Juzu'i na 1 shafi na 377 hadisi na 3 da Al- Mahasin Juzu'i na 1 shafi na 176 hadisi na 273, da Uyuni Akhbarir Ridha (A.S.) Juzu'i na 2 shafi na 58 hadisi na 214 da Kamaluddin shafi na 413 Hadisi na 15, da Al-Gaybatu na Nu'umani shafi na 130 hadisi na 6, da Rijal Al- Kasshi Juzu'i na 2 shafi na 723 hadisi na 799, da Musnad Al- Tayalasi shafi na 259 hadisi na 1913, da Hilliyatul Awliya'u Juzu'i na 3 shafi na 224 da Al- Mu'ujamul Kabir na Tabarini Juzu'i na 10 shafi na 350 hadisi na 10687, da Mustadrakul Hakim Juzu'i na 1/77 da Sharhun Nahjul Balaga na Ibin Abil Hadid Juzu'i na 9 shafi na 155 da Yanabi'ul Muwadda Juzu'i na 3 shafi na 155 da Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 5 shafi na 224 da Musnad Ahmad Juzu'i na 4 shafi na 96.

    ( 95 )

    ma'abucinsa kada ka damu lalle Allah na tare da mu, sai Allah Ya saukar da natsuwarSa gare shi Ya kuma taimake shi da rundunoni da ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar wadanda suka kafirta makaskanciya kalmar Allah kuma ita ce Madaukakiya kuma lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima" Surar Tauba: 40.
    Ko kuma kamar yadda ya suturtu a wadi63, to haka nan ya inganta Imami ya suturtu kuma babu bambanci tsakanin fakewa mai tsawo da gajera a hankalce.
    Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma ga kowace a'luma akwai mai shiryarwa." Surar Ra'ad: 7.
    "Kuma babu wata al'umma face mai gargadi ya zamanto cikinta." Surar Fatir: 24.
    ____________
    63- Wadi shi ne fili tsakanin duwatsu biyu. Wadin da ake nufi a nan shi ne wadin da ake kira "Wadin Abi Talib (A.S.) wanda Bani Hashim da Banu Abdul Mutallibi bin Abdu Manaf, in banda Abu Lahab, suka shiga cikinsa har na tsawo shekaru biyu ko kuma uku yayin da Kuraishawa suka sanya masu fago don kada wani ma ya kai musu abinci. A duk tsawan wannan lokacin sun kasance suna amfani da dukiyan Nana Khadija ne da ta Abu Talib har suka kare. A lokacin ba su kasance suna fita daga wannan wadi ba sai dai lokacin Umura a watan Rajab da kuma lokacin aikin Hajji. A wannan lokacin Aliyu bin Abi Talib (A.S.) shi ne ya kasance yana fita a boye zuwa Makka yana samo musu abinci.
    A duba As- Sahih Fi Siratin Nabi Juzu'i na 2 shafi 108, da Lisanil Arab Juzu'i na 1 shafi na 499.

    ( 96 )

    24- Imaninmu Game da Ismar Imami.

    Mun yi Imani da cewa Imami ma tamkar Annabi wajibi ne ya zama katangagge daga dukka munanan ayyuka da alfasha, na zahiri da na badini, daga yarinta har zuwa mutuwa, da mantuwa ko da ganganci.
    Kazalika wajibi ne ya zama katangagge daga kuskure da mantuwa, da rafkanuwa domin Imamai masu kare shari'a, masu tsayiwa a kanta halinsu tamkar halin Annabi ne. Dalilin kuwa da ya hukunta mana imani da ismar Annabawa haka nan shi ne dalilin da ya hukunta mama imani da ismar Imami ba tare da wani bambanci64 ba.
    Kuma ba gagararre ba ne ga Allah Ya tare talikai duk cikin abu dai duk jimillah65
    ____________
    64- Idan da ba don sun kasance ma'asumai ba to da ba su cancanci su zamo Halifofin Annabi (S.A.W.A.) domin rashin Ismarsu zai kare a dori a kan dori ne marar iyaka. Domin dalilin bukatar Imami bayan Annabi (S.A.W.A.) shi ne rashin Ismar mutane don haka suke bukatar wanda zai sa su a tafarki madaidaici, idan kuwa mai shiryarwar bai zama Ma'asumi ba to lalle da akwai bukatar wani ba shi ba wanda wannan zai sa a yi ta bi ni in bi ka har abada. Awa'ilul Makalat Shaikh Mufid 37 Tajridul I'itikad: 222.
    65- Dala'ilul J'ijaz 196(2l8), 424 (499) da 428 (502) Diwani Abi Nuwas.

    ( 97 )

    25 - Imaninmu Game da Siffofin Imami

    Mun yi Imani cewa Imami tamkar Annabi shi ma ya wajaba ya zamanto mafificin mutane a siffofin kamala, kamar su jaruntaka, da karimci, da kame kai, da gaskiya, da adalci, da tafi da al'amura, da hkima da kuma kyawun hali.
    Dalilinmu kuma game da Annabi shi ne ainihin dalilanmu ma game da Imami a game da haka...
    Dangane da Iliminsa kuwa, shi yana samun saninsa da hukunce-hukuncen Ubangiji da dukkan masaniyarsa ne ta gurin Annabi ko kuma Imamin da ya gabace shi.
    Idan kuwa aka sami wani sabon abu to babu makawa ya san shi ta hanyar ilhami daga karfin kwanyar da Allah Ya cusa masa, idan ya mai da hankalinsa a kan wani al'amari yana so ya san hakikaninsa to ba ya kuskure kuma ba ya rikirkicewa kuma ba ya bukatar hujjoji na hankali a kan haka kuma ba ya bukatar fahintarwar Malamai66; koda yake ilimin nasa na iya karuwa ya kara inganta, wannan shi ne abinda ya sa Annabi (S.A.W.A.) a addu'arsa yake cewa: "Ubangiji ka kara mini ilimi." Yana kunsa fadar Allah "Ka ce Ya Ubangiji Ka kara mini ilimi." Surar Taha.: 114.
    Na ce: Ya tabbata a ilimin sanin halayya cewa kowa yana da wata sa'a ayyananniya ko ma awowi da yakan san wani abu shi da kansa ta
    ____________
    66- Domin a bisa dabi'a idan da yana bukatar malami to da malamin nasa ya fishi ilimi a kan abinda ya koya masa don haka sai ya zama tilas ya bi shi a umarnin da ya masa kuma shi kansa malamin yana bukatar malami sai al'amari ya zamanto bi ni in bi marar iyaka. Don haka ne ya zama wajibi Imami ya zaman mafi ilimin zamaninsa.
    ( 98 )

    hanyar kaifin fahimta wanda shi a kan kansa reshe ne na ilhami, saboda abinda Allah Ya sanya masa na karfin yin haka, wannan kudurar ta sha bamban wajen tsanani da raunana, da karuwa da kuma raguwa a bil Adama gwargwadon sabanin daidaikunsu, sai tunanin mutum ya kai ga sani a wancan lokacin ba tare da bukatar ya tsaya ya yi tunani ko kuma tsara mukaddama da hujjoji ba ko kuma koyawar malamai ba, kuma sau da yawa mutum kan sami irin haka sau da yawa a kan kansa a rayuwa.
    Idan kuwa al'amarin haka yake to ya halatta ga mutum ya kai ga madaukakan darajojin kamala a karfin tunaninsa na samun ilhami. Wannan kuwa abu ne da masana falsafa na da da na yanzu.
    Don haka muke cewa: shi a kan kansa: to lalle karfin ilhami a gurin Imami da ake kira "kuwwal kadsiyya" ya kai ga mafi kololuwar darajar kamala, don haka yana da tsarkakar ruhi da ke daidai da karbar sannai a kowane kokaci ta kowane hali, don haka duk lokacin da ya mai da hankali ga wani abu daga abubuwa yana bukatar ya san shi sai ya san shi da wannan kudurar ta "Kuwwa Kudsiya" ta Ilhami ba tare da jinkirtawa ba ko shirya wasu mukaddimomi ko kuma koyo daga bakin malami, haka abinda yake son sanin zai bayyana gare shi kamar yadda abubuwa ke bayyana a tsaftatacce madubi, babu wani dindimi ko rikitarwa game abinda ya so sanin.
    Wannan kuwa abu ne da yake bayyananne game da tarihim Imamai (A.S.) tamkar Annabi Muhammadu (S.A.W.A.) ba su yi tarbiyya a hannnu kowa ba, ba su koyi karatu a gurin wani malami ba tun daga farkon rayuwarsu har zuwansu shekarun balaga, koda rubutu ba su koya a gurin wani ba, bai tabbata ba cewa daya daga cikinsu ya shiga gurin koyon rubutu ko ya yi almajiranci a hannun wani malami a kan wani abu duk kuwa da cewa kuwa suna da matsayin ilimi da ba a iya kintatawa67. Kuma ba a taba tambayar wani abu ba face sun ba da
    ____________
    67- Amirul Muminina Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) ya ce: "Manzon Allah (S.A. W.A.) ya sanar da ni Babi dubu, kowane Babi daga cikinsu kuma yana bude Babi dubu wato Babi dubu-dubu kenan har sai da na san abinda ya kasance da wanda zai kasance har zuwa ranar tashin Kiyama, kuma na san ilimin bala'o'i da
    ( 99 )

    amsarsa a lokacin da aka tambaya, ba a tabajin kalmar (ban sani ba)68 daga bakinsu ko kuma jinkirta ba da amsa har sai sun yi nazari ko tunani ko makamancinsu.69
    Alhali kuwa ba za ka taba samun wani daga cikin manyan malaman fikihu ba face wadanda ya yi tarbiyya a hannunsu da kuma guraren da ya ciro ruwayoyinsa ko kuma inda ya sami iliminsa daga mashahurai, da kuma cewa ya dakata a kan wasu matsaloli, ko kuma ya yi shakka a kan al'amura da dama kamar dai yadda al'adar mutum take a kowane guri a kowane zamani.
    ____________
    Mutuwa da kuma fasahar magana" Al- Kafi Juzu'i na 1 shafi na 239, Yanabi'ul Muwadda Juzu'i na 1 shafi na 75.
    Kazalika ya kara cewa: "Wallahi idan da na so da na ba wa kowa daga cikinku labarin in da ya fto da inda zai je da dukkan al'amuransa da na yi haka, amma ina jin tsoro ne kada ku kafircewa Manzon Allah (S.A.W.A.) a kaina. Ku sani cewa ni zan sanar da shi ga wani daga cikin kebabbun da aka amince da shi game da haka. Na rantse da wanda ya aiko shi da gaskiya ya kuma zabe shi a kan ba na magana face gaskiya. Kuma tabbas ya sanar mini da wannan duka da kuma mutuwar duk wanda zai mutu da tsiran wanda zai tsira da kuma makomar wannan al'amarin. Bai bar wani abu da ke shiga kaina ba face ya saka mini shi a kunnena ya bayyana mini shi." Nahjul Balaga Huduba ta 175.
    68- Ya zo a hadisi daga Hisham Bin Hakam cewa Imam Sadik (A.S.) ya ce "Lalle Allah Ta'ala ba Ya sanya hujjarsa a bayan kasa a tambaye shi ya ce ban sani ba." Al-Kafi Juzu'i na 1 shafi na 177 karshen hadisi na 1 Tanbihi na 32.
    69- Abu ne da ya shahara daga Amirul Mumini Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) cewa: "Ya ku mutane ku tambaye ni kafn ku rasa ni, na fi sanin hanyoyin sammai fiye da na kasa" Nahjul Balaga Huduba ta 184.

    ( 100 )

    26- Imaninmu Game da Biyayya Ga Imamai.

    Mun yi imani da cewa Imamai su ne "Ulul-Amri" Shugabannin da Allah Ta'ala Ya yi umarni a yi musu biyayya70, kuma su masu ba da shaida ne a kan mutane,7l kuma su ne kofofin Allah kuma tafarkin isa gare Shi, kuma masu shiryarwa zuwa gare Shi.72 Kuma su ne taskar iliminSa, masu fassara wahayinSa, rukunan TauhidinSa, ma'ajiyar saninSa,73 don haka su ne aminai ga mazauna bayan kasa kamar kuma
    ____________
    70 - Ishara ga fadar Allah Ta'ala: "Ya ku wadanda suka yi Imani ku bi Allah ku bi Manzo da shugabanni daga cikinku kuma idan kuka yi jayayya a kan wani abu ku mayar da shi ga Allah da Manzo idan kun kasance masu imani da Allah da Ranar Lahira wannan shi ne aiheri kuma mafi kyau." Surar Nisa'i: 59.
    71- Ya zo daga Imam Bakir (A.S.) da kuma Imam Abi Abdullah Sadik (A.S.) cewa sun ce: "Mu mu ne al'umma tsakatsaki, mu mu ne shaidun Allah a kan halittunSa". Al-Kafi Juzu'i na 1 shafi na 146 Hadisi na 2 da na 4 inda ayar nan ta zo "Haka nan muka sanya ku al'umma matsakaiciya domin ku kasance shaidu a kan mutane Manzo kuma ya zama shaida a kanku". Surar Bakara: 143.
    72- Saboda su su ne Imamai na gaskiya, ya zo daga Manzon Allah (S.A.W.A.) ta fuska maruwaita da dama cewa: "Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu mutuwar jahiliyya" A duba Abinda Muka Yi imani da shi game da Imamai.
    Ya zo daga Amirul Muminina Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) cewa: "Lalle idan da Allah Ya so hakika da Ya sanar da bayinSa kansa amma Ya sanya mu kofofinSa, da tafarkinSa, da hanyarSa, da kuma mafuskantarSa da ta nan ne ake zo maSa, duk wadanda suka fandare da shugabancinmu ko kuma suka fifita wani a kanmu to lalle su sun tabe daga kan tafarki." Al Kafi: 192.
    73- Kazalika ya zo daga Imam (A.S.) cewa "Mu mu ne taskokin ilimin Allah, kumu mu ne masu fassarar wahayin Allah, kuma mu mu ne hujjar Allah cikakkiya a kan

    ( 101 )

    yadda suke su ne taurarin amincin mazauna sama. Kamar yadda Manzon Allah (S.A.W.A.) ya fassara.74
    Kazalika kamar yadda ya fada (S.A.W.A.) : "Lalle misalansu a wannan al'umma kamar jirgin Nuhu ne , wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya dakata ya bar shi to ya nutse ya halaka."75
    Kamar kuma yadda ya zo a Alkur'ani mai girma , "Sai dai su bayi ne ababan girmamawa. Ba sa zarce shi da magana kuma su da umarninSa masu aiki ne." Surar Anbiya'i :26 - 27.
    Kuma su su ne wadanda Allah Ya tafiyar mmsu da datti Ya tsarkake su Sosai76: Bil hasali ma mun yi Imani da cewa umarninsu umarnin
    ____________
    wadanda ke koma bayan sama, da wanda ke doron kasa." Al-Kafi: Juzu'i na 1 shafi na 192.
    Kazalika ya zo daga Imam Sadik (A.S.) cewa: "Mu mu ne Shugabanni a kan al'amuran Allah, kuma taskar ilimin Allah kuma ma'ajiyar wahayin Allah" Al- Kafi Juzu'i 1 shafi na 192.
    74- A duba Sahifatul Imam- Ridha (A.S.) shafi na 47 hadisi na 67, da kuma Uyuni Akhbarir Ridha (A.S.) Juzu'i na 2 shafi na 27 hadisi na 14, da Ilalis Sharai'i Shafi na 123 Hadisi na 1 da Kamaluddin Juzu'i na 1 shafi na 205 hadisi na 19 da Fadha'ilu Ahmad: Shafi na 189 Hadisi na 267 da Mu'ujamul Kabir na Tabarani Juzu'i na 7 shafi na 25 Hadisi na 6260 , Matalibul Aliya Juzu'i na 4 shafi na 74 Hadisi na 4002, da Ihya'ul Mayyit Bi Fadha'ili Ahlul Bait na Suyuti, Shafi na 42 hadisi na 21, da Zakha'irul Ukba shafi na 17, Fara'idus Sumtain Juzu' i na 2 shafi na 241 hadisi na 515, da Kanzul Ummal Juzu'i na 12 shafi na 101 Hadisi na 34188, da Mustadrak na Hakim Juzu'i na 3 shafi na 149, da Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 9 hadisi na 174, da Sawa'ikul Muhrika shafi na 234.
    75- Malaman tafsiri sun yi ittifaki kuma an ruwaito daga Imaman Ahlul Bait (A.S.) da kuma sahabbai da dama cewa fadar Allah Ta'ala: "Abin sani kawai shi ne cewa Allah Yana nufin kawai Ya tafiyar muku da datti ne Ya ku Mutanen gida kuma Ya tsarkake ku sosai " Surar Ahzab: 33.
    76- Cewa wannan ayar ta sauka ne game da Manzon Allah (S.A.W.A.) da Aliyu (A.S.) da Fatima (A.S.) da Hasan (A.S.) da Husain (A.S.) kuma wannan shi ne abinda marubucin littafin ya yi ishara da shi.
    Domin karin bayani a duba: Nahjul Hakk shafi na 173, da Shawahidut Tanzil na Haskani Juzu'i na 2 shafi na 10 Hadisi na 192, da Durrul Mansur Juzu'i na 5 shafi na 198, da Mushki Lil Asar Juzu'i na 1 shafi na 332, da Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 9

    ( 102 )

    Allah Ta'ala ne, biyayya gare su biyayya ce gare Shi, saba musu kuma saba Masa ne, kuma soyayya gare su soyayya ce gare Shi, kiyayya gare su kiyayya ce gare Shi.77
    Bai halatta ba a mayar musu domin mai mayarwa gare su tamkar mai mayarwa ga Allah ne.78
    Don haka Ya wajaba mika wuya gare su da biyayya ga umarninsu da riko da maganganunsu.
    Saboda haka: Mu mun yi imani cewa hukunce-hukuncen Shari'ar Ubangiji ba sa samun shayarwa sai dai daga ruwansu, kuma bai halatta a karbe ta sai dai daga gurinsu, kuma nauyin da aka dora wa baligi ba ya sauka daga kansa ta hanyar komawa ga waninsu. Kuma mukallafi ba ya samun kwanciyar hankalin cewa ya ba da wajibin da aka dora masa face ta hanyarsu.79
    ____________
    shafi na 121; da Musnad Ahmad Bin Hanbal Juzu'i na 1 shafi na 330 da Juzu'i na 4 shafi na 107 da Juzu'i na 6 shafi na 292, da Sawa'ikul Muhrika shafi 85, da Tafsirut Tabari Juzu'i na 22 shafi na 5 da Usudul Ghabati Juzu'i na 4 shafi na 29, da Khasa'isun Nisa' i Shafi na 4, da Al-Gadir Juzu'i na 1 shafi na 49 da Juzu'i na 3 shafi na 195 da Juzu'i na 5 shafi na 416 da Ihkakul Hakk Juzu'i na 2 Shafi na 501-553 da kuma Juzu'i na 5 shafi na 54, 55, 58 da kuma Juzu'i na 9/69-1 da Juzu'i na 18 shaf na 359-383, da Dala'ius Sidki Juzu'i na 2 sahfi na 103, da Sahih Muslim Juzu'i na 4 shafi na 1883, Sunan Tirmizi Juzu'i na 5 shafi na 351, da Tafsirin Ibin Kathir Juzu'i na 3 shafi na 493.
    77- Tunda yake Manzon Allah (S.A.W.A.) game da Aliyu bin Abi Talib (A.S.) a hadisin Gadir "Ya Allah so wanda ya ka so shi, Ka ki wanda ya yi kiyayya da shi Ka tozartu wanda ya tozarta shi Ka sanya gaskiya ta juya tare da shi duk inda ya juya." Bayani game da haka zai zo a sashen bayanin Abinda muka yi imani da shi cewa Imamanci da nassi ne.
    78- Saboda cewa Imami sanarwa ce daga Manzon Allah (S.A.W.A.) kuma da yake Manzon Allah (S.A.W.A.) ya fada da nassi cewa: "Duk wanda na kasance ni shugabansa ne to ga Aliyu shi ma shugabansa ne." Wannan yana nufin cewa da'a ga Imam da'a ce ga Manzo (S.A.W.A.) kuma yin watsi da hukuncinsa tamkar watsi da hukuncin Manzo ne, Allah Ta'ala Ya ce: "Duk wanda ya bi Manzon Allah to ya bi Allah ne." Surar Nisa'i: 80.
    79- Ya zo daga Abi Hamza cewa daga Imam Sajjad (A.S.) cewa: "Aliyu Binul Husain (A.S.) ya ce mana: Wane guri ne mafifici? Sai muka ce Allah da ManzonSa

    ( 103 )

    Su kamar jirgin ruwan Annabi Nuhu (A.S.) suke duk wanda ya hau to ya tsira wanda kuwa ya jinkirta ya bar su to ya dulmuye a cikin wannan ambaliyar da ke makare da igiyoyin ruwan rikitarwa da bata da da'awowi da rikice- rikice.
    A wannan zamanin bayanin tabbatar da Imamai (A.S.) a matsayin cewa su ne halifofin gaskiya a shar'ance kuma shugabanni zabin Ubanjiji domin wannan al'amari ne da ya riga ya shude a tarihi , kuma tabbatar da hakan ba zai sake dawo mana da zamanin da ya wuce na tarihi ba, ko kuma ya dawo musu da hakkinsu da aka kwace na tafi da hukuncin Allah na shari'a ba, da kuma samar da abinda Manzon Allah (S.A.W.A.) kamar yadda ya zo da shi din ba.
    Sai dai kuma karban hukunce-hukunce daga masu ruwaya da kuma Mujtahidan da ba sa sha daga daddadan ruwan mashayarsu to nesanta ne daga tafarkin sawaba a addini, kuma baligi ba ya taba samun kwanciyar hankalin cewa ya saukar da abinda aka kallafa masa daga
    ____________
    da dan ManzonSa su ne suka fi sani, sai ya ce mana guri mafifici shi ne tsakanin Makama Ibrahim (A.S.) da Rukun, kuma koda mutum zai yi tsawon rai irin na Annabi Nuhu (A.S.) wato shekaru dubu ba hamsin - yana azumtar yininsu yana kuma tsayuwar kiyamullailin dararensu a wannan gurin sa'an nan yaje ga Allah ba ya da biyayya ga shugabancinmu to wannan ba zai amfana masa kome ba."
    Man La Yahdhuruhu Fakih Juzu'i na 2 shafi na 159 hadisi na 17, da Ikabul A'amal shafi na 243 hadisi na 2, da Amali na Tusi shafi na 132 Hadisi na 209 Wasa'ilus Shi'a Juzu'i na 1 shafi na 122 hadisi 308 da baki dayan hadisan Babi na 29 da Babobin mukaddamar Al-Ibadat a Wasa'il Juzu'i na 1.
    Al- Hakimul Haskani ya kawo hadisin da ke biye a littafin Shawahidut Tanzil Juzu'i na 2 shafi na 141 daga Abi Amamal Bahili cewa: "Manzon Allah (S.A.W.A.) ya ce: Allah Ya halitta Annabawa daga bishiyoyi dabam-daban, ni da Aliyu kuma an halitta mu daga bishiya guda, ni ni ne tushenta Aliyu kuma reshenta Hasan da Husain kuwa 'ya'yanta, Shi'awanmu kuma ganyayenta duk wanda ya makale wa wani reshe daga rassanta ya tsira wanda kuwa ya kauce to ya halaka, kuma idan da Bawan Allah zai yi bauta a tsakanin Safa da Marwa shekaru dubu har ya zamanto kamar tsohon kirgi da fatarsa ta tattara amma bai samu soyayyarmu ba Allah zai kifa shi a kan fuskarsa ranar Alkiyama, Sa'an nan sai Manzo (S.A.W.A.) ya karanta wannan aya "ka ce ni ba na rokon ku wani lada kansa sai dai soyayyar dangi makusata". Surar Shura: 23.

    ( 104 )

    Allah Ta'ala, domin tare da kaddara cewa akwai sabanin ra'ayoyi a tsakanin jama'ar musulmi dangane da hukunce-hukuncen shari'a sabani irin wanda babu mai sa ran yin daidai a kansa to kuwa babu wani abu da ya saura ga mukallafi face ya juya ga mazhabar da ya so da kuma ra'ayin da ya zaba, kai babu makawa gare shi face ya yi bincike har ya kai ga hujja tabbatacciya tsakaninsa da Allah Ta'ala wajen ayyana mazhaba kebantacciya wadda ya hakikance cewa da ita ce zai isa ga hukunce-hukuncen Allah, kuma cewa da ita ce zai sauke wa kansa nauyi da aka farlanta, domin abinda ake da yakinin wajibcinsa babu makawa yana bukatar a samu yakinin saukar da shi.
    Dalili tabbatacce da ke nuna wajabcin komawa ga Ahlul Bait, da kuma cewa su ne ainihin wadanda za a koma gare su a kan hukunce-hukunce bayan Annabi (S.A.W.A.) akalla shi ne maganar Manzon Allah (S.A.W.A.) "Ni lalle na bar muku abinda idan har kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba har abada bayana, su abubuwa biyu masu nauyi, dayansu ya fi daya girma, wato littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa da kuma zuriyata mutanen gidana, kuji ku sani cewa su ba masu rabuwa da juna ba ne har su iske ni a tabki.80
    ____________
    80- Sunan Tirmizi Juzu'i na 5 shafi na 663 Hadisi na 3788 da Musnad Ahmad Juzu'i 3 shafi na 14 da 17 da 26, Juzu'i na 5 shafi na 182 da shafi na 189, da Sunanud Darimi Juzu'i na 2 shafi na 431 da Al- Musannif na Ibin Abi Shaiba Juzu'i na 11 shafi na 452 hadisi na 11725, da Sunan Ibin Abil Asim Juzu'i na 2 shafi na 336 hadisi na 754, da 628,m 630, 1548, 1549, 1553, 1555, da Tabakat na Ibin Sa'ad Juzu'i na 2 shafi na 194 da Mushkilul Asar Juzu'i na 4 shafi na 368, da Mustadrikul Hakim Juzu'i na 3 shafi na 109 da 148 da Hillayatul Awliya'i Juzu'i na 1 shafi na 355 da Mu'ujamul Kabir na Tabarani Juzu'i na 5 shafi na 153-154 hadisi na 4921-4923 da hadisi na 169-170, 4980-4982, Mu'ujamul Sagir Juzu'i na 1 shafi 131, da Al-Munakib na Ibin Magazili 234-235 hadisi 281-283, da Masabihus Sunna Juzu'i na 4 shafi na 190 hadisi na 4816 da Jami'ul Usul-Juzu'i na 1 shafi na 278 da Usudul Gaba Juzu'i na 2 shafi na 12 da Zakha'irul shafi na 16 da Ihya'il Mayyit bi Fadha'ili Ahlit Baiti (A.S.) na Suyuti shafi na 30-32 hadisi na 6-8 da Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 1 shafi na 170 da kuma Juzu'i na 9 shafi 162, da Kanzul Ummal Juzu'i na 1 shafi na 172-173 hadisi na 870-873 da 875, 876, da 185-186 hadisi na 952-9S3 da Sahih Muslim Juzu'i na 4 shafi na 1873 hadisi na 36 da 37, Tafsirur Razi Juzu'i na 8 shafi na l63 da Tafsirin Ibin Kasir Juzu'i na 4 shafi na 122.

    ( 105 )

    Wannan hadisin masu ruwaya a tafarkin Sunna da Shi'a sun yi ittafaki a kansa. Don haka ka kyautata nazarin wannan hadisin da kyau za ka iske abinda zai gamsar da kai ya kuma ba ka mamaki a ma'anarsa da abinda ya kunsa, manufar maganar Manzo "Matukar kun yi riko da shi ba kwa taba bacewa bayana har abada", tana da zurfi, kuma abinda ya bari a tsakaninmu masu nauyi guda biyu ne a hade tare, domin ya sanya su ne kamar abu guda daya bai wadatu da a yi riko da guda daya ba kawai daga cikinsu, saboda haka ta riko da su tare ne kawai ba za mu taba bacewa ba har abada.
    Kuma ma'anar fadinsa (S.A.W.A.) cewa "Ba za su taba rabuwa ba har su iso gare ni a tabki" a sarari take sosai, wato wanda ya raba tsakaninsu bai yi riko da su tare ba to ba ya taba samun shiriya har abada, wannan kuma shi ne abinda ya sa suka zamanto "Jirgin Ruwan Tsira" da "Amincin Allah a bayan kasa". Kuma duk wanda ya jinkirta ya dakata ya bar su to ya nutse a cikin guguwar bata ba kuma zai amintu daga halaka ba.
    Fassarar wannan kuwa da soyayya gare su ne kawai ba tare da riko da maganganunsu da bin hanyarsu ba guje wa gaskiya ne, babu abinda ke kaiwa ga hakki illa ra'ayin rikau da gafala daga ingantacciyar hanya a bisa fassarar bayyanannen zancen Larabci.


    ( 106 )

    27 - Imaninmu Game da Son Ahlul Bait (A.S.)

    Allah Ta'ala Yana cewa:

    "Ka ce ni bana rokon ku wani Lada a kansa sai dai soyayyar dangi na kusa kawai."81 Surar Shura: 23.
    Mun yi imani cewa baicin wajabcin riko ga Ahlul Bait wajibi ne a kan kowane musulmi ya yi addini da soyayya gare su da kaunarsu domin a wannan ayar Allah Ta'ala Ya kayyade abinda ake rokon mutane da su yi shi shi ne soyayya ga dangi makusata.
    Ya zo jejjere ta hanyoyi daban-daban da dama daga Ananbi (S.A.W.A.) cewa soyayya gare su alamar imani ne kuma kiyayya gare su alamar munafunci82 ne da kuma cewa wanda ya so su ya so Allah da ManzonSa wanda kuma ya ki so to ya ki Allah da Manzonsa.83
    ____________
    81- Ya zo daga Ibn Abbas cewa ya ce: Yayin da wannan aya ta "Ka ce ni ba na rokon ku kome na lada a kansa sai dai soyayya ga dangi na kusa kawai" ta sauka, sun ce: Ya Manzon Allah su wane ne danginka na kusa wadanda soyayyarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu da Fatima da Hasan da Husaini."
    Domin karin bayani a duba Durrul Mansur Juzu'i na 6 shafi na 7, da Tafsirin Tabari Juzu'i na 25 shafi na 14 da Mustadrakul Hakim Juzu'i na 2 shafi na 444 da Musnad Ahmad: 199 da Yanabi'ul Muwadda: 15, da Sawa'ikul Muhrika shafi na 11 da na 102, da Zakha'irul Akbar: 25 da sauransu.
    82- Fadha'ilu Ahmad shafi na 176 hadisi na 248, da Zakha'irul Akbar shafi na 18 da Kunuzul Haka'ik na Mannawi shafi na 135 da Ihya'ul Mayyit bi Fadhli Ahlil Bait (Alaihimus Salam), shafi na 35 hadisi na 13 da Musnad Ahmad Juzu'i na 1 shafi na 84, 95, 128 da Sahih Muslim Juzu'i na 1 shafi na 86 hadisi na 131, da Tajuj Jami'u Lil Usul Juzu'i na 3 shafi na 335, da Sunan Tirmizi Juzu'i na 2 shafi na 301, da


    ( 107 )

    Bilhasali ma soyayya gare su farilla ce da wajiban addinin Musulunci wadda ba zai yiwu a yi jayayya ko shakka a kai ba. Dukkan musulmai sun yi ittafaki a kai duk da sabanin da suke da shi kuwa a tsakaninsu a tafarkuna da ra'ayoyi in banda wata jama'a kalilan ba da aka dauke su a matsayin masu gaba da Zuriyar Manzon Allah ba wadanda aka yi watsi da su da suna "Nawasib" wato wadanda suka kulla gaba da zuriyar gidan Muhammadu(S.A.W.A.). Don haka ne ma ake kidaya su a cikin masu karyata wajiban addinin musulunci tabatattu, mai karyata wajiban addinin musulunci- kamar salla da zakka - to ana kidaya shi ne a cikin hukuncin wanda ya karyata ainihin addinin musulunci, kai tabbatacce ne ma cewa shi ya karyata Sakon koda kuwa a zahiri ya yi furuci da kalmar shahada.
    Wannan shi ne abinda ya sa kiyayya ga zuriyar Muhammadu (S.A.W.A.) ta zama daga cikin alamun munafunci, soyayya gare su kuma daga alamun imani, saboda haka ne kuma har wa yau kiyayya gare su ta zama kiyayya ga Allah da ManzonSa. Kuma babu shakka Allah Ta'ala bai farlanta soyayya gare su ba sai don sun cancanci soyayya da biyayya, ta bangaren kusancinsu gare shi Ta'ala, da matsayinsu a gurinSa, da tsarkakarsu daga shirka da sabo, da kuma daga dukkan abinda zai nesantar daga gidan karamarSa da farfadiyar yardarSa.
    Ba zai taba yiwuwa ba a suranta cewa Allah Ta'ala Ya wajabta son wanda ke aikata sabo, ko kuma wanda ba ya bin sa yadda ya kamata, domin shi ba shi da wata kusantaka ko abota tare da kowa, mutane a gurinsa ba kome ba ne illa bayi halittattu a matsayi guda, sai dai kawai maffici a cikinsu a gurin Allah shi ne mafi tsoron Allah daga
    ____________
    Sunan Nisa'i Juzu'i na 8 shafi na 117, da Sawaikul Muhrika shafi na 263 da Al-Mahasin Juzu'i na 1 shafi na 176 hadisi na 274, da Amali Saduk shafi na 384.
    83- Amali Saduk shafi na 384 hadisi na 16 da Kanzul Ummal Juzu'i na 12 shafi na 98 hadisi na 34168 da shafi na 12: 103 hadisi 34194, da 12 shafi 116 hadisi na 34286, da Maktalul Husain na Khuwarzami na 1/109 da Zakha'irul Akbar shafi na 18 da Sawa'ikul Muhrika shafi na 263.

    ( 108 )


    ( 109 )

    28- Imaninmu Game da Imamai (A.S.)

    Ba mu yi imani game da Imamai (A.S.) irin yadda 'Yan Gullatu85, masu wuce iyaka suka yi ba haka nan ba mu yi irin yadda 'Yan
    ____________
    85- 'Yan Gullatu, masu wuce iyaka, sune wadanda suke imani da abinda ba daidai ba kana ba gaskiya ba game da Imamai (A.S.) suna cewa su Imamai Iyayengiji ne kuma su ba halittattu ba ne da dai sauransu na daga batattun akidu. Su 'Yan Gullatu sun kasu kashi daban-daban kamar haka:
  • Garabiyawa: Su ne wadanda suke cewa Allah Ta'ala Ya aiko Jibrilu da sako zuwa ga Aliyu bin Abi Talib (A.S.) sai ya kuskure ya ba wa Annabi Muhammadu (S.A.W.A.) saboda tsananin kama da juna da suka yi.
  • Ulya'iyawa: Su ne mabiya Ulya'i bin Dira'id Dausi ko kuma Asadi, su ne wadanda suke da imanin cewa Aliyu bin Abi Talib (A.S.) Ubangiji ne da kuma cewa Annabi Muhammadu (S.A.W.A.) bawan Aliyu bin Abi Talib (A.S.) ne -wal iyaza billahi!
  • Khamsiyyawa: Su ne wadanda suke da imanin cewa Aliyu bin Abi Talib (A.S.) Ubangiji ne kuma Salmanu Farisa da Abu Zar da Mikdada bin Aswad da Ammar Yasir, da Amru Bin Umayyatad Dhamiri su Annabawa ne da ubangiji Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) ya wakilta su su gyara duniya baki daya.
  • Bazi'iyawa: Su ne mabiya Bazi'i Bin Musa Al- Ha'ik wadanda suke cewa shi Annabi Ma'aiki ne kuma Imam Sadik (A.S.) shi ne ya aiko shi. Imam Sadik (A.S.) yaji Labarin sa kuma ya la'ance shi a sarari.
  • Saba'iyawa: Su ne mabiya Abdullahi Bin Saba wanda malaman tarihi ke da sabani game da shi kan cewa shi hakika mutum ne da aka yi shi ya rayu da gaske a tarihi ko kuma dai wani tatsuniya ne kawai da makiyan Shi'a suka kago shi, mabiyansa su ma sun yi Imani ne da cewa Aliyu Bin Ali Talib (A.S.) Ubangiji ne abin bautawa.
    ( 110 )

    Halluyuna86 suka yi ba, "Kalmar da ke fita daga bakunansu ta girmama." (Surar Kahf: 5).
    Mu Imaninmu a kebe shi ne cewa su mutane ne kamar mu, suna da abinda muke da shi, kuma abinda yake kanmu yana kansu, sai dai kawai su bayin Allah ne ababan girmamawa Allah Ya kebance su da
    ____________
  • Mugiriyyawa: Su ne mabiya Mugira Bin Sa'idil Ajali wanda ya yi da'awar annabci, kuma ya halalta haram da yawa kuma ya cusa barnace-barnacensa a littafin Shi'a hatta ya zo a hadisi cewa Imam Sadik (A.S.) ya la'ance shi.
  • Mansuriyyawa: Su ne mabiya Abi Mansur Ajali wanda Imam Bakir (A.S.) ya yi masa ba ni ba kai kuma shi ne wanda ya yi wa kansa da'awar Imamanci kuma ya ce Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) shi ne ballin tarsashin da ke fadowa daga sama kuma sakon manzanci da ba ya karewa har abada.
  • Khaddabiyawa: Su ne mabiya Abil Khaddab Muhammadu bin Abi Zainab Al-Ajda'il Asadi wanda ya yi da'awar cewa shi Annabi ne Manzo, kuma shi yana daga cikin Mala'iku da dai ire-irensu na daga bace-bace.
    Duk wadannan kungiyoyin bata da makamantansu fandararru, Imamai (A.S.) sun nesanta kansu daga wata alaka da su kamar yadda ya zo a hadisai da dama, kana kuma sun gargadi Shi'awansu game da su. Alal Misali ya zo daga Imam Sadik (A.S.) yayin da Sadir ya tambaye cewa: "Lalle wasu jama'a suna da'awar cewa ku iyayengiji ne kuma suna karanta mana ayar Alkur'ani game da haka wadda take cewa "kuma Shi ne wannan da yake Ubangiji a sama kuma Ubangiji a kasa" Sai ya ce: "Ya Sadir Jina da ganina da fatata da namana da jinina da gashina duk ba su ba wadannan, Allah Ya barranta daga gare su, wadannan ba a kan addinina suke ba kuma ba sa kan addinin iyayena, Wallahi Allah ba zai hada ni da su ba ranar Alkiyama face Yana fushi da su." Al- Kafi Juzu'i na 1 shafi na 269. Milal Wan Nihal Juzu'i na 1 shafi na 154 Al- Farku Bainal Firak shafi na 238, Firakus Shi'a shafi na 42, Muruji'z Zahab Juzu'i na 3 shafi na 220.
    Mikbasul Hidaya Juzu'i na 2 shafi na 361 Aslus shi'a wa Usuliha shafi na 172, Wasu hadisai da dama kuma sun yi gargadi game da 'Yan gullatu, masu ketare iyaka, daga cikinsu akwai wadanda ke Biharul Anwar Juzu'i na 25 shafi na 265 da dai sauransu.
    86- 'Yan Halluyuna: Su ne wadanda suke cewa "Ruhin Ubangiji" Ya sauka a jikin Imami kuma su kansu dukansu asalinsu 'Yan Gullatu ne, bayani game da su kuma tamkar bayani ne game da'Yan gullatu.

    ( 111 )

    karamarSa kuma Ya so su da soyayyarsa, domin sun kasance a kan daraja mafi kamala mafi dacewa ga mutum na daga ilimi, da takawa, da jarumta da karimci, da kamewa, da dai dukkan kyawawan dabi'u mafifita na daga kyawawan siffofi, kuma babu wani dan Adam da zai yi kusa da su a kan abinda aka kebance su da shi.
    Da wannan ne kuma suka cancaci su zamo Imaman shiriya, da kuma duk abinda yake ya shafi bayanin shari'a da kuma abinda ya kebanci shari'a da kuma abinda ya kebanta da Akur'ani na daga tafsiri da bayani.
    Imam Sadik (A.S.) Ya ce:
    "Duk abinda ya zo muku daga gare mu wanda ya halatta ya zamanto daga halittu ba kuma ba ku san shi ba ba ku fahince shi ba to kada ku musa shi ku mayar da shi gare mu, kuma abinda ya zo muku daga abinda bai halatta ya kasance daga halittu ba ku musa shi kuma kada ku mayar da shi gare mu."87
    ____________
    87- Mukhtasarul Basar'irud Darajat: 92


    ( 112 )

    29- Imaninmu Game da Cewa Imamanci
    Sai da Nassi

    Mun yi imani cewa Imamanci tamkar Annabci ne ba ya kasancewa sai da nassi daga Allah Ta'ala a harshen ManzonSa, ko kuma a bisa harshen Imamin da ya kasance da nassi idan har ya so ya ba da nassi game da Imamin bayansa. Hukuncin Imamanci a kan haka tamkar hukuncin Annabci ne ba tare da wani banbanci ba, mutane ba su da ikon wani hukunci a kan wanda Allah Ya ayyana shi mai shiryarwa ga bil Adama baki daya, kamar kuma yadda ba su da hakkin ayyana shi, ko kuma kaddamar da shi, ko zabensa, domin wanda yake da tsarki da kwazon daukar alkyabbar Imamanci baki daya da kuma shiryawa da illahirin bil Adama gaba daya bai dace ya san wani abu ba face da sanarwar Allah kuma bai kamata a ayyana shi ba face da ayyanawar Allah.88
    Mun yi imani cewa Annabi (S.A.W.A.) ya ba da nassi game da halifansa kuma Imamin talikai Aliyu Bin Abi Talib Amirul muminina (A.S.), amini a kan wahayi Imamin halittu, ya ayyana shi a gurare da dama kuma ya nada shi ya kuma karba masa bai'a a kan shugabancin Muminai ranar Gadir Ya ce: "Aji a fadaka duk wanda na kasance ni shugabansa ne to ga Aliyu shi ma shugabansa ne, Ya Allah Ka so wanda ya so shi Ka ki wanda ya ki shi, Ka taimaki wanda ya taimake
    ____________
    88- ya riga ya gabata cewa Imami tamkar Annabi ne sai dai cewa Annabi ana yi masa wahayi Imami kuwa ba a yi masa wahayi.

    ( 113 )

    shi Ka tozorta wanda ya tozarta shi kuma Ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya."89
    Daga cikin guraren farko dangane da nassi a kan imamancinsa maganarsa (Manzo) yayin da ya kirayi danginsa makusata da 'yan'uwansa na kusa kuma ya ce. "Wannan shi ne dan'uwana kuma wasiyyina kuma halifana, ku bi shi"90, a yayin nan kuma shi yana yaro bai balaga ba.
    ____________
    89- Al- Musannaf na Ibin Abi Shaiba Juzu'i na 12 shafi na 67 hadisi na 1214 da 68 hadisi na 12141, da Sunan Ibin Majah Juzu'i na 1 shafi na 43 hadisi na 116, Sunan Tirmizi Juzu'i na 5 shafi na 633 hadisi 3713, da As- Sunna na Ibin Abi Asim shafi na 59l hadisi na 1361, Musnad Ahmad Juzu'i na 118- 119 da kuma Juzu'i na 4 shafi 281 da 368 da 370 da 372, da Khasa'is na Nisa'i shafi na 102 hadisi na 88, Ansabul Ashraf na Balaziri Juzu'i na 2 shafi na 156 hadisi na 169, da Kashful Astar na Bazari Juzu'i na 3 shafi na 190-191, da Al- Mu'ujamul Kabir na Tabarani Juzu'i na 3 shafi na 21 hadisi na 3052 da kuma Juzu'i na 4 shafi na 173 hadisi na 4053, da Mu'ujamus Sagir Juzu'i na 1 shafi na 1 da shafi na 65 da Mustadrakul Hakim Juzu'i 3 shafi na 109 da Akhbaru Isfahan Juzu'i na 1 shafi na 107 da Juzu'i na 2 shafi na 228 da Tarikhu Bagdad Juzu'i na 7 shafi na 377 da Juzu'i na 14 shafi 236, da Al-Manakib na lbin Magazili shafi na 16-27 hadisi na 23, 26, 27, 29, 33, 37, 38, da Shawahidut Tanzil na Haskani Juzu'i na 1 shafi na 157 hadisi na 211, da Tarikhu Dimashk na Ibin Asakir - Tarjamatul Imam Ali (A.S.) Juzu'i na 2 shafi na 38-84 Tazkiratul Khawas shafi na 36, da Usdul Ghaba Juzu'i na 1 : 367 da Juzu'i na 4 shafi na 28 da Zakha'irul Akba shafi na 67, da AI- Isaba Juzu'i na I shafi na 304, don karin bayani kuma ana iya duba Littafan- Al- Gadir na Shaikh Amini da littafin Ihkakul Hak, da Abkatul Anwar da Dala'ilus Sidki da sauransu da dama.
    90-Amali Saduk shafi na 523, A'alamul Wara shafi na 167, da Ihakak Hak Juzu'i na 4 shafi na 297, Musnad Ahmad Juzu'i na 111 da shafi na 159 , Khasais na Nisa'i shafi na 83 hadisi na 66, da Tarikhut Tabari Juzu'i 19 shafi na 74, da Shawahidut Tanzil Juzu'i na 1 shafi na 420 da Sharhin Nahjul Balaga na Ibin Abil Hadid Juzu'i na 3 shafi 267, da Yanabi'ul Muwadda Juzu'i na 1 shafi na 104, Al- Kamil Juzu'i na 2 shafi na 62 da Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 8 shafi 302 da sauransu, da ba za su kidayu ba.

    ( 114 )

    Kuma ya maimaita maganarsa sau da dama cewa: "Kai a gare ni matsayin Haruna ga Musa kake sai dai kawai babu Annabi ne bayana."91
    Da sauran ruwayoyi da ayoyi masu girma da suke nuni da tabbatar shugabanci na gaba daya gare shi kamar ayar da ke cewa: "Tabbatacce kawai shi ne cewa Allah ne Majibincinku da ManzonSa da Wadanda suka yi imani wadanda suke ba da zakka su suna masu ruku'i." Surar Ma'ida: 55.
    Wannan ta sauka ne game da shi yayin da ya ba da sadakar zobensa yana cikin ruku'u.92
    ____________
    91- Al- Musannif na Ibin Abi Shaiba Juzu'i na 12 shafi na 60 hadisi na 12125 da shafi na 61 hadisi na 12126, da Tarikhul Kabir na Bukhari Juzu'i na 1 shafi na 115 hadisi na 333 da Juzu'i na 7 shafi na 301 hadisi na 1284, da Sahih Muslim Juzu'i na 4 shafi na 1870 hadisi na 2404, da Sunanut Tirmizi Juzu'i na 5 shafi na 640 hadisi na 3730, Sunan na Ibin Abi Asim: Ya ambata shi da isnadai dabam-daban daga hadisi na 1333-1348, Musnad Ahmad Juzu'i na 1 shafi na 179 da Juzu'i na 3 shafi na 32, da Juzu'i na 6 shafi na 438, Khasa'is na Nisa'i shafi na 68-79 hadisi na 45, 48, 50, 51, 62, 63, 64 da Hilliyatul Awli'ya'u Juzu'i na 4 shafi na 345 da Juzu'i na 7 shafi na 195 da 196 da Tarikhu Isfahan Juzu'i na biyu shafi na 281, 328 da Mu'ujamul Kabir na Tabarani Juzu'i na 1 shafi na 146 hadisi na 328 da 148, 333, 334, da Juzu'i na 2 shafi na 247 hadisi na 2035, da Juzu'i na 4 shafi na 17 hadisi na 3515 da Juzu'i na 11 shafi na 74 hadisi na 11087 da Juzu'i na 24 shafi na 146 hadisi na 384-389, da Mu'ujamus Sagir Juzu'i na 2 shafi na 53,54, Tarikhu Bagdad Juzu'i na 1 shafi na 325 da Juzu'i na 3 shafi na 406, Juzu'i na 8 shafi na 53 da Juzu'i na 9 shafi na 365 da na 10 shafi 43, da'Juzu'i na 12 shafi na 323, da Isti'ab Juzu'i na 3 shafi na 34, da Al-Manakib na Ibin Magazili shafi na 27-36 hadisi na 40-56, Tarikhu Dimashk Tarjamatu Imam Ali (A.S.) Juzu'i na 1 shafi na 306-390, Majma'uz Zawa'id Juzu'i na 9 shafi na 109 da sauransu.
    92- Tafsiru Furatul Kufi shafi na 40-41, da Amalis Saduk shafi na 107 hadisi na 4, da Tafsirut Tibyan na Tusi Juzu'i na 3 shafi na 559, da Ihtijaj na Tabrisi Juzu'i na 2 sha 489, da Tafsiriut Tabari Juzu'i na 6 shafi na 186, da Asbabun Nuzul na Wahidi shafi na 113 da Al- Munakib na Ibin Magazili shafi na 3 12 hadisi na 356 da shafi na 313 hadisi na 357, Al-Manakib na Khawarzimi shafi 264, Tazkiratul Khawas shafi na 24, Tafsiri

    ( 115 )

    Bin diddigin duKkan abinda ya zo na daga ruwayoyi da ayoyin Alkur'ani ba ya goyon bayan cewa wannan sakon kagagge ne kazalika bayani manufofinsu da suke nuni da su.93
    Sa'an nan shi kuma kansa (A.S.) ya ba da nassi game da Imamancin Hasan da Husain (A.S.), shi kuma Husain94 ya ba da nassin Imamancin dansa Aliyu Zainul Abidin (A.S.) haka nan dai Imami ke ba da nassin Imami bayan Imami, wanda ya gabata ya ba da na mai zuwa har zuwa kan na karshensu kuma shi ne zababbensu kamar yadda zai zo.
    ____________
    93- Littafin As- Sakifa na marubucin wannan Littafin sashen Aliyu bin Abi Talib (A.S.)" shafi na 59-73 Akwai sharhin wasu ayoyin.
    94- Kari a kan abinda ya zo daga Manzo (S.A.W.A.) game da su biyu domin hadisi ya zo a jejjere da hanyoyi da dama kan cewa ya ce: "Wadannan 'Ya'yan nawa guda biyu Imamai, sun tashi ko sun zauna" Annaukat shafi na 48, Ilalus Shara'i-i Juzu'i na 1 shafi na 21 1, Al- Irshad shafi na 220, Kifayatul Asar: 117, da At Tuhaf na Majduddin shafi na 22, da Yanabi'un Nasiha shafi na 237, da ya ce "Babu wata rikitarwa game da kasancewar wannan hadisin daga wanda al'umma ta karbe shi domin Ya kai darajar hadisi mutawatiri, mai hanyoyin zuwa da yawa, don haka ya inganta a kafa dalili da shi." Game da shi ne ma Ibin Shahar Ashubi ya ce a manakib: "Ma'abuta Alkibla sun yi ittifaki a kansa".

    ( 116 )

    30-Imaninmu Game da Adadin Imamai.

    Mun yi imani da cewa Imamai wadanda suke da siffar imamanci na gaskiya, sune wadanda muke komawa gare su a hukumce - hukumcen shari'a wadanda aka bada nassi game da Imamancinsu su goma sha biyu ne ,Annnabi(S.A.W.A.) ya bada nassi a kansu dukkanninsu da sunayensu95 sa'an nan kuma duk wanda ya gabata daga cikinsu to ya ba da nassi akan wanda ke biye da shi kamar haka:-
    ____________
    95- Kamaluddin shafi na 250-256 hadisi na 1-4 da Uyunu Akhbarur Ridha (a.s.) Juzu'i na 1 shafi na 41-51 hadisi na 2-16, da Amalit Tusi juzu'i na 1 shafi na 291 hadisi na 556/13 da Fara'idus Simtain juzu'i na 2 shafi na 132 hadisi na 431 da na 136 da na 435 da 313 da 564.
    Ya zo a ruwayoyi da dama wadanda maruwaitan Ahlus Sunna da dama suka kawo wadanda a cikinsu Annabi (S.A.W.A) yake cewa: lalle halifofi bayansa goma sha biyu ne da kuma cewa lalle dukkaninsu daga Kuraishawa suke. Daga cikinsu akwai wanda Jabir bin Samrata ya kawo yayin da ya ce:" Na kasance tare da mahaifina a gurin Annabi (S.A.W.A) sai na ji yana cewa: Bayana akwai halifofi goma sha biyu sa'an nan sai ya yi kasa-kasa da muryarsa a kai, ya ce cewa yayi dukkanninsu daga Bani Hashim suke". Da dai wasun wannan ruwayar da dama.
    A duba Musnad Ahmad Juzu'i na 5 shafi na 89 da 90 da 92, da kuma Musradrakul Hakim Juzu'i na 4 shafi na 501 da Majma'ul Zawa'id Juzu'i na 5 shafi na 190 Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 201 da 206 da kuma Sahih Bukhari Juzu'i na 9 shafi na 101 da Sahih Muslim juzu'i na 2 shafi na 192 da Tarikhul Khulafa'i shafi na 10 da Sunan Tirmizi Juzu'i na 2 shafi na 35 da Yanabi'ul Muwadda shafi na 444 da sauransu da dama.

    ( 117 )

    Adadi
    Al-Kunya
    Suna
    Lakabi
    Haihuwa
    Rasuwa
    1
    Abul Hasan
    Aliyu bn Abi Talib
    Al-Murtad

    Comments

    Loading...
    no comments!

    Related Posts