Logo

SANIN MA'ASUMAI
GOMA SHA HUDU
A TAKAICE



Muhammad Husain Adib

Wanda Ya Fassara: Y.A. Ningi


( 3 )

Sunan Littafi : SANIN MA'ASUMAI GOMA
SHA HUDU
Marubuci : Muhammad Husain Adib
Wanda Ya Fassara: Yakubu Abdu Ningi
Adadi: 3000
Shekarar da aka Buga: 1418, 1997
Mada ba'ar da ta Buga: Mihir
Hakkin Mallaka: Mu'assasar Imam Ali (A.S.)


( 4 )



Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai


( 5 )

IMAM ALI (A.S.) FOUNDATION
P.O. Box 37185/737
Qum - IRAN
Telfon: 730001- 4
Faks: 730020


( 6 )

Gabatarwa
Da Sunan Allah mai Rahama mai jin kai.

Godiya ta tabbata ga Allah wanda falalarsa da karimcinsa suka yadu, baiwarsa da ni'imominsa kuma suka kwarara, tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Muhammadu da zuriyarsa ma'abuta ilimin baiwa.
Bayan haka, wannan takaitaccen tarihi ne dangane da Ma'asumai goma sha hudu wadanda su ne: Manzon Allah Muhammadu (SAWA) da Fatima da Imamai tsarkaka, dangane da wasu daga cikin martabobinsu wadanda babu makawa mumini ya san su, musulmi kuma su fahince su, a takaice. Tare da fatan samun lada a kan haka da kuma samun kyakkyawan yabo, Allah Shi ne mafificin mai ba da dacewa kuma mai taimako.

Muhammad Husain Adib
Karbala, Alhamis
25 ga watan Shawwal 1393 Hijiriyya
21 ga watan Nuwamba 1973 Miladiyya


( 7 )

1. MAFIFICIN ANNABAWA
MUHAMMADU (SAWA)

Babban Lakabinsa: Mustafa.
Alkunyarsa: Abul Kasim wato Baban Kasimu, Khairul Bariyya: Mafificin Halittu, Nabiyur Rahma (Annabin Rahama), Sahibul Malhama, Muhallilul Tayyibat (Mai Halatta Kyawawa), Khatamun Nabiyin (Cikamakin Annabawa), Rasulul Haamidin (Ma'aikin masu godiya), Rahmatan Lil Alamin (Rahama ga halittu), Ka'idul Garril Muhajjalin: Abdullah (Bawan Allah), Khiyaratullah; (Zababben Allah), Sayyidul Mursalin, (Shugaban Manzanni), Imamul Muttakin; (Jagoran Masu Takawa), Habibullah: (Masoyin Allah), Safiyallah; (Zabin Allah), Ni'imatullah; (Ni'imar Allah), Sahibulliwa; (Ma'abucin Tuta), Ibinul Fawatim; (Dan Fatimomi), Abdul Mu'ayyad;


( 8 )

(Bawa Abin Taimako), Nabiyul Muhazzab; (Annabi Mai Tsari), Safiyul Mukarrab; (Zababbe Abin Kusatarwa), Habibul Muntakhab; (Abin so Zababbe), Aminul Muntakhab; (Amini Zababbe), Sahibul Haudha wal Kausar; (Ma'abucin Tabki da Alkausara), Khairul Bashar; (Mafificin Mutane), Almurtadha Lil ilmi; (Abin yarda ga Ilimi), Muharrimul Khaba'is; (Mai haramta kazanta), Miftahul Jannati; (Mabudin Aljanna), Da'awatu Ibrahim; (Addu'ar Annabi Ibrahim), Bushra Isa; (Busharar Annabi Isa).
Mahaifinsa: Abdullah
Mahaifiyarsa: Amina bintu Wahab
Ranar Haihuwarsa: Ranar Juma'a da Safe 17 ga watan Rabi'u Awwal.
Gurin Haihuwarsa: Garin Makka Mai Alfarma
Shekarar Haihuwarsa: Shekarar giwaye zamanin mulkin Adalin sarki Anusharawan shekara ta 622 miladiyya.
Ranar wafatinsa: Ranar Lahadi 28 ga watan Safar kafin magariba.
Shekararsa: Sittin da Uku.


( 9 )

Dalilin Rasuwarsa: Guba da aka sa masa a abincinsa.
Gurin Kabarinsa: Garin Madina
Adadin `ya'yansa: 7, uku maza hudu mata.
Mazan su ne:
1) Kasimu,
2) Abdullah wanda ake yi wa lakabi da Attahir, (mai tsarki), da kuma Attayyib (kyakkyawa). Mahaifiyarsu ita ce Khadija,
3) Ibrahim Mahaifiyarsa ita ce Mariya.
`Ya'ya mata kuma su ne:
1) Zainab,
2) Rukayya,
3) Ummu Kulsum,
4) Fatima.
Adadin Matansa: 15.
Hatiminsa: Kalmar Shahada.


( 10 )


( 11 )


2. ALI (A.S.)


Lakabinsa: Amirul Muminin
Alkunyarsa: Abul Hasan (Baban Hasan), Abul Hasanain (Baban Hasan da Husaini), Abul Sibtain (Baban Hasan da Husaini), Abu Raihanatain (Baban ma'abuta kamshi), Abu Turab (Baban Turbaya).
Mahaifinsa: Abu Talib (Baffan Annabi) Imran ko kuma Abdu manaf Ibin Abdul Mutallib.
Mahaifiyarsa: Fatima Bintu Asad
Ranar Haihuwarsa: Ranar Juma' a 13 ga Rajab
Gurin Haihuwarsa: Cikin Ka'aba Dakin Allah mai alfarma.
Shekarar Haihuwarsa: Shekara talatin bayan Shekarar Giwaye.


( 12 )

Ranar Rasuwarsa: Daren Juma'a 21 ga watan Azumi.
Shekarar wafatinsa: Shekara ta 40 bayan Hijira.
Shekarunsa: Shekara sittin da uku.
Dalilin Rasuwarsa: Ibn Muljam ne ya kashe shi sakamakon harin ba zata da ya kai masa yana salla a cikin masallacin Kufa.
Adadin `ya'yansa: 36, 18 da cikinsu maza ne 18 kuma mata.
Mazan su ne:
1) Al- Hasan Mujtaba,
2) Husain,
3) Muhammad Bin Hanafiyya,
4) Abbas Akbar wanda ake yi wa alkunya da Abul Fadli,
5) Abdullahil Akbar,
6) Ja'afarul Akbar
7) Usmanul Akbar,
8) Muhammad Asgar,
9) Abdullahil Asgar,
10) Abdullah wanda ake yi wa Alkunya da Abu Ali, (Baban Ali),


( 13 )

11) Aun,
12) Yahya,
13) Muhammadul Awsat
14) Usmanul Asgar,
15) Abbasul Asgar,
16) Ja'afarul Asgar,
17) Umarul Akbar,
18) Umarul Asgar.
Mata kuwa akwai:
1 ) Zainabul Kubra,
2) Zainabul Sugra wadda ake kira Ummu Kulsum,
3) Ramlatal Kubra,
4) Ummul Hasan,
5) Nafisatu,
6)Rukayyatus Sugra
7) Ramlatul Kubra,
8) Rukayyatul Kubra,
9) Maimunatu,
10) Zainabus Sugra,
11 ) Ummu Hani,
12) Fatimatus Sugra,
13) Imamatu,


( 14 )

14) Khadijatus Sugra,
15) Ummu Kulsum,
16) Ummu Salama,
17) Hamamata,
18) Ummu Kiram.
Adadin matansa: 12
Hatiminsa: Almulku Lillahi Wahidul Kahhar, (Mulki na Alla ne Shi kadai mai tilastawa).

Comments

Loading...
no comments!

Related Posts