Logo

3. Fatima (S.A.)


Lakabinta: Zahra
Alkunyarta: Ummul A'imatul Athar (Mahaifiyar Imamai Tsarkaka), Ummul Hasan, Ummul Husain, (Mahaifiyar Husain), Ummul Muminin, (Uwar Muminai), Ummul Fada'il, (Uwar Falala), Sayyidatu Nisa'il Alamin (Shugabar matan halittu), Khairun Nisa'i, (Mafificiyar mata), Albatul, Ummul Khiyaratu, (Uwar zababbu), Ummun Nijaba'u, Ummul Azhar. Mahaifinta: Muhammadu Manzon Allah (SAWA)
Mahaifiyarta: Khadijatu' Kubra Ummul Muminin
Ranar Haihuwarta: Ran Jumma'a 20 watan Jumada sani.


( 16 )

Gurin Haihuwarta: Garin Makka mai Alfarma.
Shekarar Haihuwarta: Shekara ta biyar bayan ba da Annabci shekara takwas kafin hijira.
Ranar Wafatinta: Ranar Talata 3 ga watan Jumada sani.
Shekarar wafatinta: Shekara ta 11 bayan Hijira.
Shekarunta: 18
Dalilin Wafatinta: Bala'o'i da wahalhalun da suka same ta bayan wafatin mahaifinta.
Gurin kabarinta: Baki'a a garin Madina.
Adadin `ya'yanta: `ya'ya maza biyu banda Muhsin wanda ta yi barinsa. Mazan su ne Hasan da Husaini sai kuma `ya'ya mata guda biyu wato:
1 ) Zainabul Kubra
2) da Zainabus Sugra wadda ake wa alkunya da ummu Kulsum.
Rubutun Hatiminta: Allahu Waliyu Ismati; wato Allah shi ne Majibincin kare ni.


( 17 )

4. Hasan (A.S.)


Lakabinsa.: Mujtaba, Taki, Zakiy; Sayyid, Sibt.
Alkunyarsa: Abu Muhammad.
Mahaifinsa: Amirul Muminina Ali (A.S.)
Mahaifiyarsa: Fatimatuz Zahra (A.S.)
Ranar Haihuwarsa: Ranar Talata 15 ga watan Azumi.
Gurin Haihuwarsa: Garin Madina Shekarar Haihuwarsa: Shekara ta Biyu Hijiriyya.
Ranar Wafatinsa: Ranar Alhamis 7 ga watan Safar.
Shekarar Wafatinsa: Shekara ta arba'in da tara bayan Hijira.
Shekarunsa: Arba'in da Bakwai
Dalilin Wafatinsa: Matarsa Fu'adatu `yar Ash'as ita ce ta shayar da shi guba da umarnin Mu'awiya.


( 18 )

Gurin Kabarinsa: Makabartar Baki'a Madina.
Adadin `Ya'yansa: 15 Takwas maza, bakwai mata, mazan su ne:
1) Zaidu,
2) Hasan,
3) Umar,
4) Kasimu,
5) Abdullah,
6)Abdurrahman,
7)Husain,
8)Talha.
Mata kuma su ne:
1) Ummul Hasan,
2) Ummul Husain,
3) Fatima
4) Ummu Abdullah
5) Fatima,
6) Umma Salama,
7) Rukayyatu.
Adadin matansa: 13
Rubutun Hatiminsa: "Al- Izzatu Lillah "Daukaka Ta Allah Ce".


( 19 )

5. Husain (A.S.)


Lakabinsa: Sayyidus- Shuhada, Arrashid, Attayib, Al-Wafiy, Azzakiy; Assayyid, Assa'id, Sibtis Sani, Tabi'u Li Mardhatillah, Asshahidu Bi Karbala, Dalil Ala Zatillah, Imamus Salis.
Alkunyarsa: Abu Abdillah.
Mahaifinsa: Amirul Muminina Ali (A.S.)
Mahaifiyarsa: Fatimatuz Zahra (A.S.)
Ranar Haihuwarsa: Ranar Alhamis uku ga watan Sha'aban.
Gurin Haihuwarsa: Garin Madina
Shekarar Haihuwarsa: Shekara ta uku bayan Hijira.
Ranar Wafatinsa: Ranar Juma'a Goma ga watan Muharram.
Shekarunsa: Hamsin da takwas


( 20 )


Dalilin Rasuwarsa: Yazid dan Mu'awiya ne ya sa mayaka suka taru a kansa suka kashe shi da iyalan gidansa.
Gurin kabarinsa: Garin Karbala mai tsarki.
Adadin `Ya'yansa: (6) Hudu maza, biyu mata, mazan su ne:
1) Ali Akbar (Zainul Abidin),
2) Ali Awsat,
3) Ja'afar, 4) Abdullah (Ali Asgar) ko (Ali Awsat)
Matan kuwa su ne:
1) Sukaina da,
2) Fatima.
Zuriyarsa kuwa daga Zainul Abidin ne. An kashe Ali Awsat tare da shi kuma an masa kabarinsa a gefensa. Ja'afar kuwa mahaifiyarsa ita ce Kasa'iyyatu kuma ya rasu tun mahaifinsa na da rai kuma an masa kabari a Madina.
Shi kuwa Abdullahi a kashe shi a hannun mahaifinsa a Karbala yana jariri kuma ana ce masa Ali Asgar. Ali Awsat akan ce da shi Akbar dangane da shi karamin ana kuma ce da shi Awsat dangane da Zainul Abidin.


( 21 )

6. ALI (A.S.)


Lakabinsa: Zainul- Abidin, Sajjad, Zainus-Salihin, Warisul Ilmin- Nabiyin, Mutahajjid, Azzakiy, Azzahid, Al-Abid, Al- Adil, "Al-Bakka'u zun safanat" wato ma'abucin hawaye mai yawa.
Alkunyarsa: Abu Muhammad.
Mahaifinsa: Husain Sibtin Nabi.
Mahaifiyarsa: Shah Zanan Bintu Yazdjard (Shahr Banu)
Ranar Haihuwarsa: Alhamis: Goma ga Jumada Ula.
Gurin Haihuwarsa: Garin Madina
Ranar wafatinsa: Ranar 25 ga Muharram.
Shekarar wafatinsa: Shekara ta 95 Hijiriyya.
Shekarunsa: 57.
Dalilin wafatinsa: Hisham Bin Abdilmalik ya ba shi guba zamanin mulkin dan'uwansa Walid.


( 22 )

Gurin Kabarinsa: Makabartar Baki' Madina kusa da Baffansa Hasan (A.S.).
Adadin `Ya'yansa: (15) Maza Goma sha daya, mata hudu. Mazan su ne:
1) Muhammad Bakir,
2)Abdullah,
3) Hasan,
4) Husain,
5) Zaid,
6) Amru,
7) Husain Asgar,
8) Abdurrahman,
9) Sulaiman,
10) Ali,
11) Muhammad Asgar.
Mata kuma su ne:
1) Khadija,
2) Fatima,
3 ) Aliyyatu,
4) Ummu Kulsum.
Matansa: Daya, banda kuyangi.


( 23 )


Matarsa daya ita ce mahaifiyar Abdullah wato Fatima `yar Hasan bin Ali (A.S.) kuma ita ce mahaifiyar Bakir (A.S.).
Rubutun Hatiminsa: Hasbiyallahu Likulli Hammi. Wato Allah ya wadatar mini a kan duk wata damuwa.


( 24 )


( 25 )

7. Muhammad (A.S.)


Lakabinsa: Bakir, Zakir, Shakir, Hadi, Sabir, Jamiu, Hadhiru, Shabihu, Nathiru.
Alkunyarsa: Abu Ja'afar
Mahaifinsa: Ali Zainul- Abidin (A.S.)
Mahaifiyarsa: Fatima `Yar Hasan Sibt (A.S.)
Ranar Haihuwarsa: 6 ga watan Rajab
Gurin Haihuwarsa: Garin Madina
Shekarar Haihuwarsa: Shekara ta Hamsin da biyar bayan hijira.
Ranar Wafatinsa: Litinin bakwai ga watan Zulhijja.
Shekarar Wafatinsa: Shekara ta dari da goma shahudu, 114. Hijiriyya.
Shekarunsa: Hamsin da Bakwai.
Dalilin wafatinsa: Hisham Bin Abdul Malik ne ya ba shi guba.


( 26 )

Gurin Kabarinsa: Makabartar Baki'a a Garin Madina.
Yawan `Ya'yansa: (8) Shida maza biyu mata.
Mazan su ne:
1) Abu Abdillah Sadik,
2) Abdullah,
3) Ibrahim,
4) Ubaidullah,
5) Raja
6) Ali.
Mata kuwa su ne:
1) Zainab,
2) Ummu Salama.
Yawan matansa: Biyu ne banda kuyangi.
Rubutun Hatiminsa: Al- Izzatu Lillahi Jami'a (Wato Daukaka ta Allah ce baki daya).


( 27 )

8. Ja'afar (A.S.)


Lakabinsa: Sadik, Tahir, Ka'im, Kafil, Munji, Sabir, Musaddak, Muhakkak, Kashiful Haka'ik.
Alkunyarsa: Abu Abdillah.
Mahaifinsa: Muhammad Bakir (A.S.)
Mahaifiyarsa: Fatima wadda ake yi wa Alkunya da Umma Farwa `Yar Kasim dan Muhammad bin Abi Bakar (Karaiba)
Ranar Haihuwarsa: Litinin sha Bakwai ga watan Rabi'ul Awwal.
Gurin Haihuwarsa: Garin Madina
Shekarar Haihuwarsa: Shekara ta 83 Hijiriyya.
Ranar Wafatinsa: Alhamis 20 ga watan Shawwal.
Shekarar Rasuwarsa: Shekara ta dari da Arba'in da takwas, 148, Hijiriyya.


( 28 )

Shekarunsa: Sittin da biyar.
Dalilin wafatinsa: Mansur Dawaniki ne ya ba shi guba.
Gurin Kabarinsa: Makabartar Baki' a Madina Yawan `Ya'yansa (10) Bakwai maza, uku mata. Mazan su ne:
1) Isma'il,
2) Abdullah Aftahi,
3) Musa Kazim,
4) Ishak,
5) Muhammad Dibaj,
6) Abbas,
7) Ali.
Mata kuwa su ne:
1) Fatima,
2) Asma'u,
3) Ummu Farwa.
Yawan matansa: Daya, banda kuyangi.
Rubutun Hatiminsa: Allahu Khaliku kulli Shai'in (Wato Allah shi ne mahaliccin kome da kome).


( 29 )

9. Musa (A.S.)


Lakabinsa: Kazim, Zahid, Wafi, Amin, Zainul Mujtahidin, Nafsuz Zakiya, Abdus Salih, Sikatun Tayyib, Sayyid Ma'amun.
Alkunyarsa: Abu Hasanus Sani.
Mahaifinsa: Ja'afarus Sadik (A. S ).
Mahaifiyarsa: Hamidatu Musaffatu Andalus (Aspaniya)
Ranar Haihuwarsa: Daren Lahadi Bakwai ga Safar.
Gurin Haihuwarsa: Abu'a (wani guri tsakanin garin Makka da Madina)
Shekarar Haihuwarsa: Shekara ta dari da ashirin da takwas (128) Hijiriyya
Ranar Wafatinsa: Juma'a Ashirin da takwas (28) ga watan Rajab.
Shekarar wafatinsa: Shekara ta dari da tamanin da uku (183) bayan Hijira
Shekarunsa: Shekara Hamsin da Biyar (55).


( 30 )

Dalilin Wafatinsa: Haruna Rashid ne ya ba shi guba ya mutu a kurkuku.
Gurin kabarinsa: Kazimiyya.
Adadin `Ya'yansa: Talatin da shida (36), 19, maza 17, mata. Mazan su ne:
1) Ali,
2) Ibrahim,
3) Abbas,
4) Kasim,
5) Ismail,
6) Ja'afar,
7) Harun,
8) Hasan,
9) Ahmad,
10) Muhammad,
11) Hamza,
12) Abdullah,
13) Ishak,
14) Ubaidullah,
15) Zaid,
16) Hasan,
17) Fadhl,
18) Husain,
19) Sulaiman.


( 31 )

Mata kuwa su ne:
1) Fatima Kubra,
2) Fatima Sugra,
3) Rukayya,
4) Hakima,
5) Ummu Abiha,
6) Rukayya Sugra,
7) Ummu Ja'afar,
8) Lubabatu,
9) Zainab,
10) Khadija,
11) Aliyyatu,
12) Aminatu,
13) Hasanatu,
14) Barihatu,
15) A'ishatu,
16) Ummu Salama,
17) Maimunatu.
Adadin matansa: Ba a tantance ba.
Rubutun Hatiminsa: "Kun Ma'allahi Hirzan" Wato ka zaman mai kiyayewa tare da Allah.

Comments

Loading...
no comments!

Related Posts