10. ALI (A.S.)
Lakabinsa: Ridha, Sirajullah, Nurul- Huda, Kurratu Ainul Muminin Makidatul Mulhidin, Kufuwul Malik, Kafil Khalk, Fadhil, Sabir, Wafi, Siddik, Zakiy.
Alkunyarsa: Abul Hasan.
Mahaifinsa: Musa Kazim.
Mahaifiyarsa: Takattumu wadda ake yi wa alkunya da Ummul Banin, Khizarar, Shakra', Urwa, Sakina.
Ranar Haihuwarsa: Alhamis 11 ga watan Zilhijja.
Shekarar Haihuwa: Shekara ta dari da Arba'in da takwas bayan hijira (148).
Ranar wafatinsa: Ranar Talata 17 ga watan Safar.
Shekarar wafatinsa: Shekara ta dari biyu da uku (203) Hijiriyya.
( 34 )
Dalilin wafatinsa: Mamun Abbasi ne ya ba shi guba.
Shekarunsa: Shekara Hamsin da biyar (55).
Gurin Kabarinsa: Garin Mashhad Mai Tsarki- Iran.
Yawan `Ya'yansa: (6) Biyar maza daya mace.
Mazan su ne:
1) Muhammad Kani,
2) Hasan,
3) Ja'afar,
4) Ibrahim,
5) Husain.
Mace kuma ita ce: A'isha.
Yawan matansa: Daya banda kuyangi.
Rubutun Hatiminsa: "Ma Sha Allah La Kuwwata Illa Billah" Wato, "Allah, Ya yarda babu karfi sai daga Allah".
( 35 )
11. Muhammad (A.S.)
Lakabinsa: Jawad, Taki, Kani, Mukhtar, Zakiy, Murtadha, Alim, Nurus Satih.
Alkunyarsa: Abu Ja' afar.
Mahaifinsa: Ali Ridha (A. S. )
Mahaifiyarsa: Sabbikatu. Imam Ridha (A.S.) ya sa mata suna Khizaran, Rayhanatu, Durratu.
Ranar Haihuwarsa: 10 ga watan Rajab.
Gurin Haihuwarsa: Garin Madina
Ranar Wafatinsa: Ranar Talata ranar karshen watan Zul Kida.
Shekarar Wafatinsa: Shekara ta dari biyu da shirin (220) Hijiriyya.
Shekarunsa: Ashirin da biyar (25).
Dalilin Wafatinsa: Matarsa `Yar Ma'amun ce ta ba shi guba da umarnin Mu'utasim.
Gurin Kabarinsa: Kazimiyya.
( 36 )
Yawan `Ya'yansa: (4) Biyu maza, biyu mata.
Mazan su ne:
1) Ali,
2) Musa, Mubarka.
Matan kuma su ne:
1) Fatima da,
2) Imamatu.
Yawan matansa: Biyu.
Rubutun Hatiminsa: "Hasbiyallahu" Allah Ta Isar Mini.
( 37 )
12. ALI (A.S.)
Lakabinsa: Hadi, Naki, Mutawakkil, Askari, Najib, Murtadha, Alim, Fakih, Amir, Dalil, Amin, Mu'utamin, Tayyib, Nasih, Miftah.
Alkunyarsa: Abul Hasanus Salis.
Mahaifinsa: Muhammad Jawad (A.S.)
Mahaifiyarsa: Sammanatul Kani'a (da ga kasar Maroko ko Swiss)
Ranar Haihuwa: 15 ga watan Zulhijja ko kuma 5 ga watan Rajab.
Gurin Haihuwa: Garin Madina.
Shekarar Haihuwa: Shekara ta dari biyu da goma sha biyu (212) Hijiriyya.
Ranar Wafatinsa: Ranar Litinin uku ga watan Rajab.
Shekarar Wafatinsa: Shekara ta dari biyu da hamsin da hudu (254) Hijiriyya.
Shekarunsa: Arba'in da daya (41)
( 38 )
Dalilin Wafatinsa: Mu'utamid Abbasi ne ya ba shi guba.
Yawan `ya'yansa: (5) hudu maza daya mace.
Mazan su ne:
1) Abu Muham
2) Husain,
3) Muhammad,
4) Ja'afarul Kazzab, macen kuwa ita A'ishatu.
Yawan matansa: Daya.
Rubutun Hatiminsa: "Almulku Lillah" mulki na Allah ne.
( 39 )
13. Hasan (A.S.)
Lakabinsa: Askari, Zakiy, Khalis, Siraj, Mushaffi, Hadi, Sakhiy, Samit, Mawla, Rafik, Mudhiy, Mardhiy, Mustawdi.
Alkunyarsa: Abu Muhammad.
Mahaifiyarsa: Hadisatu tana daga cikin Arifai game da Allah. (daga Swiss. Harbiyya)
Ranar Haihuwa: Goma ga watan Rabi'us Sani.
Shekarar Haihuwarsa: Shekara ta dari biyu da talatin da biyu (232) Hijiriyya.
Ranar Wafatinsa: Juma'a takwas ga watan Rabi'ul Awwal.
Shekarar wafatinsa: Shekara ta 260, Hijiriyya.
Dalilin Wafatinsa: Mu'utamid Abbassi ne ya ba shi guba.
Gurin kabarinsa: Samarra.
( 40 )
Yawan `Ya'yansa: Dansa Daya ne kuma shine Al- Hujjatul Ka'im Muhammad Mahadi (A.S.)
Yawan matansa: Daya.
Rubutun Hatiminsa: "Innallaha shahidun "Lalle Allah Mai Shaida ne".
( 41 )
14. Muhammad (A.S.)
Lakabinsa: Mahadi, Hujja, Ka'im, Basit, Bakiyyatullah, Bakiyyatul Anbiya, Gausul Fukara, Khatamil Awsiya, Muntazar, Sa'ir, Hujjatullah, Khatamul A'imma, Khashiful Gumma, Khalafus Salih, Khalifatullah, Khalifatur Rahman, Imamul Insi Wal Jan, Sahibur Raja'a, Sahibuz Zaman, Da'iy, Assa'a, Sahibud Dar, Sahibun Nahiya, Sahibul Asr, Sahibul Amr, Samsamul Akbar, Al- Fakih, Al-Farajul A'azam, Al- Gayatul Kuswa, Katilul Kafara.
Al- Kunyarsa: Abul Kasim.
Maha.ifinsa: Hasanul Askari.
Mahaifiyarsa: Narjis Khatun.
Ranar Haihuwarsa: Daren jumma'a 15 ga watan Sha'aban.
Garin Haihuwa: Samarra.
( 42 )
Shekarar Haihuwa: Shekara ta dari biyu da hamsin da biyar (255) Hijiriyya.
Shekarunsa biyar ne yayin da mahaifinsa ya bar duniya. Allah ya zabe shi halifa kuma ya sanya shi Imami kamar yadda ya sanya Yahaya da Isa Imamai suna kanana yara.
A halin yanzu yana raye ana arzuta shi yana jiran umarnin Allah ne kawai ya bayyana don ya cika duniya da adalci da daidaito kamar yadda ta cika da zalunci da rashin daidai.
Shi Imam (A.S.) ya boyu sau biyu, boyuwa karama wadda ta dauki tsawon shekaru 74 wadda ta fara tun daga haihuwarsa zuwa shekara ta 329 Hijiriyya.
A lokacinta ya kasance yana da Jakadu guda hudu:
1) Usman Bin Sa'idul Umari (Abu Amru)
2) Muhammad Bin Usman wanda aka fi sani da Khalani (Abu Ja' afar)
3) Husain Bin Ruh (Abul Kasim)
4) Aliyu Bin Muhammad Samari (Abul Hasan)
( 43 )
Daga lokacin wafatinsa ne (shi na karshe) a shekarar 329 sai boyuwa babbar ta fara.
Dukansu wadannan an musu kabari ne a Gabas da Bagadaza (a Iraki) guraren Ziyartarsu mashahurai ne sanannu.
Amma: Wakilansa kuwa, shi maulana Hujja (A.S.) ya kasance yana da wakilai aminai a kowane bangare wadanda suke zuwa da sanya hannu daga bangarorin wadannan jakadun hudu wadanda muka ambata sunayensu. Wadanda suka kasance suna da matsayin wakilanci a kebe kuwa Jama'a ne masu yawa kamarsu Abil Husain bin Ja'afarus Asadi, da Ahmad bin Ishak Al- Kummi, da Kasim binul Ala Al- Azarbaijani, da Hajiz Bin Yazid Al-Washa da Abi Hashim Dawud- binul Kasimul Ja'afari, da Ibrahim, da Ahmad binul Yasa da sauransu.
A zamanin akwai Na'ibancin mutane da dama wadanda ake samun sanya hannu daga bangaren Jakadun da aka nada.